episode 8

33 3 0
                                    

KAWANCEN MU
2017

*mallaka*...*faumsyk family*

Bayan su sumayya sun Isa gida , suka huta gajya, sumayya nata yaba wa da garin nasu na jos.
Da dare yayi sumayya ta maida hankali wajan hada kayanta guri daya sbd ita a tsarinta tafiso su tafi da sassafe.
"kedai wlh sumayya kin cika taurin kai, duba fa yanda kowa yaketa rokanki ki kara kwanaki amma kika ki". Inji sha'awa.
Sumayya da tagama hada komai ta dakko laptop din sha'awa tana danne danne tace 
"ke Kam kin fiya naci wlh, nafa fada miki xamu dawo da surayya , ko yanxu da tana Nan ba abinda xe hana muyi wata dayan tare."
Can kofar gida kuwa wannan saurayin ne dasu sumayya suka hadu da a onigbinde supermarket tsaye tare da securities din gidan. 
"Meye sunayen wa enda kake nema?" securityn ya tambaya.
Nan ne fa yafara raba ido damn yasan xa'a rina, dayasani ya tambayi sunayensu amma yayi ragon azanci. Chan dai yace " eh to dayake suna sauri ne basu fada min sunayensu ba amma sun ban complementary card dinsu cewar na samesu a gida." gashi Nan.. Sai ya nuna musu.
Saida securityn ya Kare mai kallo tsaf kafin ya shiga kiran mai su. Hajjo mai aikin gidan ya fadiwa sakon ta isar wajan madam sha'awa,wai mutumin yace a supermarket suka hadu dazu da yamma.
Koda hajjo ta isar musu da sakon sha'awa tace. 
" kaman fa guy din daxu ne da ko sumayya? Wlh na xaci irin jobless guys dinnan ne shiyasa kikaga na mika mai card dinnan daxu, nasan d moment yaga address din ciki baxe ma yi tunanin ko xuwa ba. Amma I think he's serious enough tunda har ya iya biyoki a yau dinnan."
Sumayya Kam kallo ta bita dashi, tana direwa itama ta maida kanta Kan laptop kamn ba da ita akeyi ba.
"ki tashi kije mana sumayya wajn ki fa yaxo".
"ke ni ba inda xani, exams naxo yi garinnan ba saurayi ba." inji sumayya bayan ko pretending kawai takeyi tun daga sanda suka rabu daxu har xua yanxu tunanin shi kawai takeyi.
"tab see dis one wo, sau nawa Kuma akayi haka?" 
Har saida sha'awa ta ishi sumayya da mita kafin ta mikee ta dauki hijab dinta xata fita.
"like seriously! Hijjab xaki sa? c'mon bae Dan Allah ki cire kixo muje nai miki kwaskwarima a fuskan ki." inji sha'awa.
" Allah kuwa ba inda xani. Wlh kika nemi ki takura min sai nace baxn je ba."

Bayan sumayya ta fito ne ta hangeshi xaune a wajan da aka ware domin shakatawa, wajan ya yawaltu da Haske . Ahaka ta karasa wajan gaban ta yana mai faduwa sosai.
"Assalamu Alaikum" ta fada bayan ta karasa wajan.
Da sauri ya juyo idanuwan shi suka sauka akanta. Ta mai kyau sosai cikin pink hijjab din dake jikinta.
Amsa sallaman yayi da murmushi yana jin wani fariinciki ya cika shi.
"kiyi hkr na taso ki cikin Daren Nan, wlh xuciya tace Sam ta kasa samun natsuwa , tinda ko sunanki ba bansani ba. Banjin xan iya bacci in ban kara ganin ki ba , shiyasa kika ganni cikin darennan." haka saurayin ya fada yana mai kallan sumayya data sunkuyar da kanta kasa tana murmushi.
"kinyi kyau sosai" saurayin ya fada. Hakan Kuma shi yasa sumayya ta dago kai ta kalleshi take kuwa idanuwan su suka sarke. Ba arxiki ta maida kanta kasa ta cigaba da murmushi.
"sunana SALEEM TAHIR ADAM, ni asalina Dan Zaria ne a jahar kaduna amma aiki ya kawo ni jos. Ina aiki ne da kamfanin nasco dake angolo jos." ya fada yana mai kallan sumayya da har yanxu kanta a kasa tana murmushi.
Can i knw smth abt my princess too? At least ur name...
Saida ta Dan Dade kamn baxata iya magana ba, daganan ne ta fadi mai sunanta SUMAYYA itama a kaduna take, exams ya kawota jos, Kuma gobe xata koma gida.
"wow dat's amaxing, sunan ya dacee da ke ba kadan ba princess, ashe I'm not dat fast da naxo yau , danayi delaying da kilan gobe baxn ganki ba. Amma naji dadi sosai".
Haka dai suka cigaba da hira ko da dai ita Sam bata cewa komai sai ya xama dole. Harda rashin sabo ke damunta. 
Ya amshi no wayanta sukayi sallama tare da mata alkawarin kawo mata visit a kaduna!
Farinciki da sabon al'amari taji yana ratsa ta sosai, duk ta rasa ina xata sa kanta taji dadi. Saida ta dauki Waya ta sanar da blad dinta suna Nan fa DAwo wa gobe. Sannan tace "blad! I met a guy here in jos"
Wani ihu ne ya cika speakern wayan surayya keta ihun dadi, can tace 
" r u serious blad,"(in a happy tone)."
" kar ki damu inna dawo xan baki lbr in details, amma yanxu dai bari in fada miki sunan shi, yace sunan shi saleem taheer Adam" sumayya ta fadi tana me kara lumewa a Kan gado cike da shauki. 
" wlh blad I can't wait! Dan Allah Ku taso da wuri kunji..." surayya ta fada. Ahaka sukai sallama kowa farinciki da dokin xuwan gobe ya cika musu xuciya.

Washegari bayan sun Karya sumayya ta matsa su koma gidansu kaka domin daga can zasu koma gida. Umma safiyya ta mata kyautan naira dubu ashirin da wasu lace masu masifan kyau, ta Kuma ce mata ta gaida kowa da kowa a kaduna.
Koda suka Isa gidansu kaka ta tadda naxeefi ko shirya wa beyi ba, yace ta rabu da shi sai azahar zasu tafi, sai yaje wani waje ya dawo.
"ah lallai mutuminna kace wannan yarinyan ta gama sacee maka xuciya kawai kenan. Yanxu sai kaje Ka kara ganinta salan Ka barmin kanwa da jira?" hamxa ne ke fadiwa naxeefi haka.
Charap SUMAYYA ta chapke da 
"laaa daman Yaya naxeefi budurwanka kaxoo gani? Haba! No wonder kayi ta insisting xuwa jos dinnan ashe.."
Ashe me? Munafuka ba, Kuma wlh inji lbrn Nan wajan su umma sai na ballaki.
sumayya ta kwashe da daria kafin tace 
Eh naji Yaya ba wanda xan fadamawa amma sai dai in Ka tashi Ka shirya yanxu, sai muje tare inganta daganan mu kama hanya. Amma idan kaki kasa mukai dare su abba suka tambayemu dalilin da makayi dare wlh sai ince kaine...
Naxeefi ya tashi yana mata mugun kallo kafin ya nufi hanyan bayi domin wanka, yasan halin sumayya sarai akwai xuba wani xubin kamn an bude pampo.
Wata budurwan shi ne da suka hadu a FACEBOOK, sundade sosai sun Kuma shaku na ban mamaki duk da dai basu Taba haduwa ba. Dalilinta nema yasa ya Sama sumayya jos sbd yaxo ya ganta tunda a jos itama take.
******
Lokacin da sumayya suka fito xasu wuce kakarsu hassatu harda er kwallanta. Tana matukar kaunar jikokin nata.
"kai! Amma dai wannan tsohuwar kin cika kulafuci, wai ko xaki bini ne? Wannan soyayya haka lallai kin cika Juliet." naxeefi Keta tsokanar ta.
Ita ko sumayya xuwa tayi ta rungume kakan nata tace "kar ki damu kawata ina Nan dawo wa kinji."
Haka dai sukai sallama cike da kewan juna.
Kafin su kama hanyan kadunan kuwa saida naxeefi yaje gidan budurwan nashi domin suyi sallama. Sunanta rabi , tana da kyau ba laifi amma saidai katuwa ce tubarkallah.
Sumayya Kam sai mamaki takeyi ko ina yayanta ze kai wannnan, lallai blad dinta nada shan hira kala kala to Dan kuwa sai ta bata lbr tsaf. Koda suke gaisawa da sumayya cije dariya kawai takeyi har sukai sallama suka kama hanya. Naxeefi Kam sai far'a yakeyi abinshi yana tuki cike da nishadi. (uhm...ina ruwan so!)
*** *** **

Sun Isa garin kaduna garin gwamna wajajen karfe uku, tafya yankin axaba, gaskya na xaunu."cewar sumayya. Tana shiga gida ta ruga da gudu ta rungume ummanta ,tana wlh umma nayi missing dinki sosai. Umma na dariya itama tace "ah lallai kuwa gashi emmatan nawa ta kara kumatu abinta"
Umma! Sumayya ta fada tana mai turo baki. 
can saiga kanninta Nan sun shigo aguje kowa yana rige rigen rungumeta. Kowa sai farincikin dawo wanta yakeyi.
Can tace umma wai ina blad dina ne? Tun a hanya nake kiranta wayanta baya shiga"
Surayya ta tafi jarabawa tun dazu amma inaga ta kusa dawowa.inji umma.
Eyya...!bata karasa gama rufe baki ba taji Ana kwala mata kira. Murya taji kaman na blad dinta, ai ba arziki ta mike da gudu taje ta tarota suka rungume juna suna ihun murna.
Wayyo blad u r looking good jos yasa kinyi fresh fa" surayya ta fada. 
Sumayya daketa washe hakora tace blad ya exams din? " Alhamdulillah wlh d questions r all bearable". 
Daga haka suka shiga ciki surayya ta gaisa da umma, sumayya Kam ta shiga wanka domin taji dadin jikinta. A takaice dai ranan a gidansu sumayya surayya ta kwana, aikuwa ba labrn da sumayya bata ba er uwarta ba. Suna cikin hiran ne saleem ya kira sumayya, bayan yaji sun Isa lafya ne tace mai ga eruwata my other me Ku gaisa. Haka surayya suka gaisa da saleem a mutunce kafin sukai sallama , anan ne Kuma yake cewa sumayya yana Nan xua wajanta ranar Saturday, da har xatace ya dakata surayya ta maxxa tai mata sign akan yaxo ba damuwa. 
Haka sukai sallama kowa ya kwanta xuciyoyin su cike da nishadi.

Da asubahi misalin karfe 4:30am, daidai lokacin MUHAMMAD FAISAL KANTI ya tashi daga bacci ya sa hannun shi ya dafe kirjin ji yana mai sauke numfashi da sauri da sauri, addu'a fal bakinshi. Tun ranan da magana ta fara hadasu, wato ranan da suka shigo ajinshi er uwanta ta bada hkr ita Kuma taki, har xuwa yau bai Taba fashin ganinta cikin mafarkinshi ba. Sosai ya haddace sunanta Kuma ba abinda be bincika akanta ya sani ba. Amma abinda ke bashi mamaki shine kullun a cikin mafarki far'a take mai, magana mai dadi take mishi, tana kula da shi sosai. Unlike a gaske ko ince a zahiri wanda idan sun hadu in banda rashin kunya da harare harare ba abinda ke shiga tsakaninsu?!? Ko mafarkin da yagama yi yanxu taxo mai ne cikin shiga mai ban sha'awa taci Gayu sosai, yana xaune bakin rafi yana kallan tafiyan ruwa yaji muryanta ma'aboci zaki, ta rangada mishi sallama fuska dauke da murmushi, ta xauna kusa dashi tare da miko mai bowl cike da inibi(grapes). Da ya miko hannu Xai dauka sai ta hanashi tace" allow me to feed u pls" haka yana budebaki tana saka mai Chan saita kira sunan da tasaba kiranshi dashi kullun cikin mafarki wato "HAMMAD" da ya dago kai ya kalleta idanuwan su suka sarke na tsawon wasu mintoci kafin can tace "pls marry me"!!!
Wannan kalma da ta fada shi yayi daidai da farkawan shi daga bacci. Haka ya sauke nannauyen ajiyan zuciya tare sauke kafafuwanshi a kasa daga Kan gado, can dai ya dafe kanshi tare da fadin SURAYYA A ABBA, what r u up to???
**** ***

AMMIN EEMAAD

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now