episode 10

33 2 0
                                    

KAWANCEN MU*
2017
*MALLAKA*....FAUMSYK FAMILY!

Dayake saleem kwararren Dan duniya ne, ba arxiki ya maxa yayi composing kanshi ya kirkiro murmushin shi mai kara mai kyau yace.
"yau dai gani ga blad dinmu, amma nayi farinciki da ganinki sosai nima..." . Nan fa suka fara Dan Taba hira da surayya sumayya na Dan sa baki itama, kafin daga karshe tace " too ga amanar blad dina Nan na baka, pls take care of her heart nd plsss dnt evn dare hurting her." surayya ta fada tana mai hada hannayenta biu alaman roko.
" Kar ki damu, ur frnd is my heart itself, so how can I risk hurting dat?? Saleem ya fada yana mai kallon sumayya ita Kuma daidai da ta dago kai ta kalle shi, Nan suka wa juna murmushi gaba dayansu. 
A Nan surayya ta mike domin basu waje tare da jaddada mai yaci abinci gashi Nan.Nan dai saleem ya dinga Jan sumayya da hira ban dariya aikuwa kafin kuce me harta Dan saki jikinta da shi. Koda ya dauko peppered chicken yana ci haka ya dinga Santi wai ya mai dadi, itako tace kar ya damu in xe tafi xatai mai take away. " Kuma idan mukai aure xaki dinga yimn akai akai"inji saleem. Nan dai sukaita hira har suka kusan kwashe awa daya basu fargaba. A zahirin gaskya saleem daure wa kawai yakeyi, sbd bini bini ya kalli kofa yaga ko surayya xata leko amma shiru.
Sai wajajan 5;15 kafin saleem ya tashi Xai tafi tace bari taima Aunty faixa magana su gaisa tukun.

Sumayya ce ta rakashi har bakin motanshi dauke ta takeaway din Kazan shi, surayya na bayanta suna mai godiya hade da sallama(duk da dai zikau ya taho ba ko turare.lol). Hakanne ya bashi daman karewa surayya kallo yana ta hadiyan yawu. 
Ko cikin mota saleem tunani kawai yakeyi ta yanda Zai jefi taura biyu da dutse biu, sumayya yaxo gani amma sai ya tadda wanda tafita SoSai(a ganinshi,) sbd haka dole ne yayi amfani da basiranshi Dan ganin ya samu surayya, tare da sumayya a lokaci daya. "yes! I must have dem all!" ya fada tare da buga stear din mota da hannunshi.

A bangaren emmatan kuwa surayya sai koda saleem takeyi tana "wlh blad kinyi dacee guy din wayayye ne, ba karamn dacewa kukayi ba." Aunty faixxa ma ta kara da aiko dai Naga alama zeyi hankali. 
Nan ko sumayya sai farinciki takeyi Ana yaban saurayinta dadi da sonshi na kara ratsa ta sosai.
A hanyansu ta komawa gida ne cikin keke napep sumayya ke cewa "blad kema fa ya kamata Yaya FADEEL ya san da xamn soyayyan ki , ahaka ko ya dawo kinga ba wani matsala sai maganan aure.
" uhm Yaya fadeel din da ba wanda yasan ranar dawowanshi, gashi kullun da sanshi nake kwana nake tashi wlh, banaso na xubar da class dina ne , rannan na gwada kiranshi saida na mai missed call biyu kafin yayi calling back, koda na gaisheshi nace mai cousin dinshi ce, he didn't evn care to ask who, he just thank me for calling nd cut d call" surayya ta fada tana mai sauke ajiyan xuciya.
Sumayya Sam bataji dadin wannan zance ba to Dan kuwa ko ita shaidace akan yanda surayya ke dakon san yayan su fadeel tun suna jss3, wani xuwa ne dayayi daga UK, inda yake karatu, su Kuma sunxo hutun jssce. 
A gidan kaka suka fara haduwa , kakan tasu ta rasa ina zata sahi domin murna, tana matukar kaunar jikannan nata, ya Kan Dade sosai kafin ya dawo gida, domin kuwa medicine yake karantawa a Birmingham UK. yana gama secondary ya tafi can sbd haka sai ya samu a very long break kafin yaxo gida. 
Yana xaune a falon Hajya kaka gabanshi fura ne me sanyi hade da dambun nama, sumayya ce ta fara shigowa a guje tana aunt faixa, kaka wayyo Allah na na shiga uku... Da gudu ta shigo palon sukuma suka mike atare, kaka ta taho aguje tana na shiga uku sumayya me xan gani me ya faru?? Sam bata kula da cewa akwai wani a palon ba fuska dauke da hawaye tace 
" kaka surayya ce, gata can ta Mari wasu samari shine suka shakureta wai sai sun Rama." ai kafin ta Ida maganan da kakan da Yaya fadeel din sunyi hanyan waje a guje, anan suka tadda surayya kai ba dankwali, ta yagama wani yaro da baxe wuci sa'anta ba riga sai kokawa sukeyi dagani gaba dayansu ba wanda be jin jiki. Da sauri sauri Yaya fadeel ya Isa wajan ya fincike yaron tare da sharara mai Mari ya Kuma ture shi kasa. Itako Hajya kaka sai fadi take " kunga tsinannan yaro , Ka rasa dawa xakayi kokuwa sai mace? Ragon banxa ragon hofi Mara mutunci, ina ne iyayenka suke? Inaso in gansu yau a garinnan. Dai dai lokacin aunt faixa ta karaso dga mkrnta to Dan har mutane sun fara taruwa taja mahaifiyarta cikin gida tare da sumayya dake ta hawaye surayya Kam nata huci.
Koda suka koma cikin gida hankali ya Dan nitsa, Aunty faixa take tambayan surayya abinda ya hadasu take fada da maxa kamn wanda ba'a ma tarbiyya?
" haba Aunty yaronnan ba karamin raina min wayau yayi ba, tunda fa muka dawo banda ikon fita sai yaxo ya tasa ni agaba waishi yana sona, wlh damn na fada mai duk sanda ya kara min magana zaisha mamaki wlh. Shine fa yau harda riko min gyale abokinshi Kuma ya sha gaban blad ya tare mata hanya sbd sunga munyi nisa da gida, shine ni Kuma na mareshi!l surayya ta karasa tana mai turo baki.
Haaaa! Aunty faixa da kaka suka bude baki. Yaya fadeel ko kara bude idonshi yana karema surayya kallo. Wannan er siririyan yarinyan haka take da taurin xuciya?
" lailahaillalahu surayya kina da hankali, Marin namiji a inda kike dinnan? Dama wani Dolo ne ze tsaya yana kallanki yace baxe Rama ba?" inji Aunty fa'xa.
Aunty befa Rama ba inji sumayya, kokawa ya hauta dashi fa Dan mugunta. Allah shiyasa nima duk na rude na shigo naiman taimako karsu Karya min blad. Ta karasa tana mai fashewa da kuka ta tusa kanta Kan cinyan Hajya kaka.
Fadeel Kam kallansu yakeyi mamaki ya kusan kashe shi. Can dai yace Hajya kaka wannan wasu irin yara ne sangartattu? Ita wannan kuka kawai ta iya ya nuna sumayya, ita Kuma wannan fada da maxa? Ya dire yana mai bushewa da dariya yana girgiza kanshi.
Hajya kaka waye Kuma wannan? Surayya ta tambaya tana me yatsuna fuska. Har ga Allah su sai yanxu suka lura dashi. 
"yayanku na turai mana karkice dai baki ganeshi ba."inji kaka.
Ba arxiki surayya ta xabura tace Yaya fadeel? Kaine? ta fada tana mai daga murya cike da murna. 
Heyy! Easy! Nima kar ki kaimin duka Naga alama kina da 'kashi daya tsaya daga can. Fadeel ya fada.
Nan kowa ya kwashe da dariya surayya tace " haba dai Yaya ai kai baxn bige kaba shima dayan Dan yace yana sona ne sbd ya rainani. Surayya ta fada tana mai washe hakora.
Yanxu nima idan nace ina sanki xaki iya marina kenan. Fadeel ya fada. 
Surayya taga alama an maida abin en tsokana ne kawai sai aka kara kwashewa da dariya.
"gwada Ka gani kilan kanada rabon shan Mari ne kaima"Aunty faixa ta fada.
A'a ni rufamin asiri Aunty baxance ba ina tsoron Mari gaskiya.inji fadeel.
Nan dai kowa ya kara kwashewa da dariya harda sumayya me kuka tuni ta ware.
"ke Kuma idan nace ina sonki kila saidai ki fara kuka Naga kamn anan kikafi auwki. Fadeel ya fadiwa sumayya haka cike da tsokana. Nan dai suka dinga hira inda kasan sun Dade da sabawa abin gwanin ban sha'awa.
Ko da daddare yayi tuni har fadeel ya gama rada musu suna, sumayya" akoke" ita Kuma surayya "mai 'kashi daya". 
Yaya Dan Allah Ka Dena cemin mai 'kashi daya" surayya ta fada tana mai turo baki.
Inbahakaba mene? Xaki mareni ne? Fadeel ya fada yana mai jin dadin tsokanarsu.
" Ai kai yayana ne, Kuma ko kace kana sona baxan ma komai ba sbd kai Yaya na ne" surayya ta fada.
"haha tooo hmm nidai baxan ma fara ba." fadeel ya fada yana mai maida hankalinshi Kan ayanshi soyuwar Hajya kaka.
Washegari da xe koma abj haka ya tasa su gaba yana "ke surayya ki daina fada da maxa kinji? In sunmiki laifi ki xo ki fadane agida kinji." to inshaallah Yaya fadeel ta fada tana washe hakora,
"ke Kuma, ya nuna sumayya ki daina saurin kuka,ki xama brave kamar kawarki in ba hakaba rainaki xasuyi." Nan dai ta turo baki . Nan dai yayi musu sallama ya shiga motanshi ya koma gida, ya barsu da kewa sosai todan tsakanin jiya xua yau suna jinshi har cikin ransu.
Tu daga ranar har xuwa rana mai kaman ta yau basu kara haduwa da Yaya fadeel ba. Sun dai ji lbrn yazo har sau biu lokacin suna mkrnta so basu haduba. Ya tafi ya bar surayya da dakon sanshi daya gama mamaye mata xuciya shikam besan tana yi ba!
***

Ammin Eemaad

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now