episode 5

42 5 0
                                    

KAWANCEN MU.
2017

Gudun kar ayi biu babu yasa sumayya shigowa tare da sallama, jiki a sanyaye ta naimi waje ta xauna.
Surayya kuwa tafia take cikin fushi, saida tayi nisa da ajinsu kafin ta naimi waje ta tsaya byan jikin bangon en aji biu.
"nifa rainin wayau ne bana so, sai wani kallan uku saura kwata yake mana Hakanan ba dalili, ita Kuma blad shine harda wani bashi hkr, xata ci ubanta ne bari ta fito" haka surayya ta cigba da kanan maganganu ran ta na mata suya sosai.
" waye a tsaye anan ? Surayya! Me kike yi anan baa cikin aji ba? Mallam hassan ya tambaya.
Mallam ba komai. Wani malami ne yace wai baxn shiga mai aji ba wai nayi latti. Inji surayya.
A'a muje ai baayi hakaba muje a bashi hkr, to ke mema ya kaiki yin latti ne?
Badan taso ba hakanan ta bishi har ajin nasu. A Nan ne mallam hassan ya roki malamin da yayi hkr ya barta ta shiga.
Malamin yace ba komai tana iya shigowa tare da sallama.
Haka surayya ta shigo fuska ba annuri , ta wuce xata xauna ya dakatar da ita , sannan yace ta koma can seat din karshe ne ta xauna.
Ya lura yaran sunada rawan kai, ba tun yau ba tun Randa yaga sun shigo office din headmaster, kunya Sam be ishe su ba amma ze gyara musu xama tsaf.

Bayan malamin ya gama darasin shi ya fita ne, surayya tayi wup, ta tashi ta koma inda ta saba xama, duk da taga wata xaune a wajanta, amma seda ta koreta da mugun kallo ba arxiki ta tashi mata to Dan halin surayya ba boyayye bane na rashin bari ta kwana!
Bayan ta xauna ne azeeza Usman da Zainab dalhat wa enda kawayen su ne a ajin suka matso kusa da su tare da fadin..
" sabon malami fa aka kawo mana, ranar asabar da baku xoba ya fara shigowa, mallam auwal yazo ya gabatar da shi a matsayin mallam MUHAMMAD, shi Zai dinga daukan mu darasin Qurani wanda kullun ake yi, sai Kuma tajweeda wanda akeyi kowani talata.
Wlh malamin bashi da matsala gashi da Qira'a mai dadin saurare gashi duk sanda aka shiga sabuwar surah Zai kawo mana _asbabu wan nuzoor _ dinta.
Kunga gobe talata Xai shigo ya mana tajweed knam. 
Abu daya ya fada mana da yafara shigowa shine baya san raini Sam sai Kuma latti, Allah yana da dadin sha'ani, lack of undrestanding kawai kuka samu.
Aziza ta dire tana mai kallan surayya. 
Surayya Kam tunda suka fara maganan take Taba baki, suna direwa kuwa ta ja tsaki abinta.
" ni dai wlh gwara tun wuri ya fita harkana to Dan bazamu kwashe ta dadi ba da shi"
Blad! Sumayya tace tare da ma er uwanta kallon 'pls shut up'.
Wannan taurin kai na er uwarta daban ne, malamin su ne, ya wuce wasa, bayanda xata bari tayi disrespecting dinshi. Bari su koma gida xata mata bayani a tsanake ba tare da tashin hankali ba.

Bayan an tashesu ne sun kama hanyan tafia gida surayya tayi charap ta rike sumayya tare da fadin 
"blad kixo mu canxa hanya, kin manta black yace xe jira ki? Ni wlh tsoron mutuminnan nakeyi ba kadan ba blad, ko kema ya kamata ki rage mai tsiwa, kin san irin su basa rabo da wuka ko wani makami, kiris suke jira sai dai kiji sun Burma maka".

Sumayya ma tayi na'am da mgn er uwanta, ita dai Allah ya hadata da bala'I, in ba haka ba ina ita ina musa black da har xece duk dunia beda wanda yakeso sai ita?!? 
Bayan sun chanxa hanya ne sumayya ke cewa 
"anya blad baxn fadiwa su Yaya abba yanda black ke takura min?" 
Ki rufa mana asiri blad, Dan daba ne fa! Kin san irinsu basa ragawa kowa, ga Yaya abba da xuciya haduwarsu da black Sam baxe kyau ba. Mu samu dai mu lallaba shi mu rabu lafya, abinda islamian ma mun kusa gamata gaba daya kwanan Nan da munyi jamb muka shiga university fa shikenan. 
Fadin universityn da surayya tayi ne yasa sukaji wani dadi ya mamaye musu zuciya.
Daga nesa kadan da su ne suka hango wani kamn mallam Muhammad, yana tsaye kusa da wani masallaci yana amsa Waya. Yana yi yanacin mgani kamn Ana mai dole a magana a wayan. 
Karap idanuwan surayya da mallam Muhammad suka sarke, tako auna mai harara san ranta suka kara gaba.

" ikon Allah, amma ya akayi yarinyar Nan ta raina ni haka. Gani na da ita befi sau uku ba amma shine ta maidani kamn sa'anta. Tabbas ba tantama er uwanta ta fita hankali sosai amma itama xeyi maganinta. Inji ya muallim Muhammad.
Bayan su sumayya sun Isa layin su ne kowa yayi sallama da er uwarshi suka kama hanyan gida. 
Haka suke kullum a tare bacci ne kadai ke rabasu.
*** *** * * * *

Yau umman su surayya sinasir tayi, kasancewar Hajya kaka na matukar san sinasir yasa bayan ta gama ta cewa ismail da adeel su dauka su kaiwa mommyn su da Kuma kakarsu.
Sun maida abun kaman alada, duk sanda dayansu yayi abincin marmari Zai aikawa dayan gidan tare da sirikarsu. Bayanda baayi da Hajya kaka ba akan tabari a dinga sa sanwan abinci da ita amma tai fur taki, acewarta tafison ta girka da kanta.
Dayake Hajya kaka ba cima xaune bane, Kuma wayayyiyar tsohuwa ce baka rabata da en sana'ointa. Sbd haka kusan ko da yaushe kudi na shigo mata.
Jin cewa aiken harda na Hajya kaka yasa surayya tayi charap tace abata ita xata kai tare da sumayya daman jiya basu leka ba Sam.
Haka tacewa su adeel su tayata dauka xuwa gidan umma. 
Isarsu keda wuya suka tadda umma zaune a parlor tana kallon HUDA T.V, 
"umma ina wuni?"
Lafya klau surayya emmata ya mommyn Ku?
"tana lafya kalau, gashi tace a kawo muuku". Ta ajye ma mommy coolern sinasir din. 
"madallah yau anyi mutumn kakan Ku kenan, to na gd sosai." inji mummy. Tsakanin umma da mommy akwai shakuwa da fahimtan juna sosai, kaman dai yaransu.
Wai ina blad ne umma ban ganta bane?? Surayya ta tambaya.
Inaga tana daki tana bacci, Naga kamn bata jin dadi ne. Umma ta bada amsa.
"oh nooo", cikin hanzari surayya ta wuce cikin dakin, inda ta tadda sumayya kwance tana bacci. 
Da sassarfa ta Isa inda take ta xauna a gefenta, ta daura hannu a goshinta (forehead). Ta ji ba xafi sosai, da alama ba zazzabi knan.
A hankali sumayya ta bude idonta ta saukesu tas Kan surayya.
"blad kin tashi ne?" surayya ta tambaya fuska cike da kulawa.
Blad yaushe kikaxao? Sumayya ta tambaya fuska cike da jindadin ganin er uwanta.
"yanxu naxo umma tacemin bakya jin dadi.
"ina ji na kamn xanyi ciwo ne dazunnan amma yanxu naji nama warware. " sumayya ta fada bayan ta tashi ta zauna garau abinta.
"amma har naji dadi, na dauka ko xaki fara xaxxabin Nan naki na fama ne." dafa gidan Hajya kaka na biyo miki muje mu kai mata sinasir. Inji surayya. 
Charap sumayya ta mike tace bari in dauko hijjab sai muje, nayi missing Hajya kaka jiya bamu lekata ba Sam.

Suna shiga gidan suka tadda Hajya kaka tayi baki, to Dan har sun taso da alama xasu tafi ne.
Bayan Hajya kaka ta dawo dg raka bakinta ne surayya ke fadin 
" Hajya kaka business tycoon, Hajya kaka mai jama'a." 
Shiyasa da bikin Aunty na dinga ganin jama'a da fuskoki wasu ma ban sansu ba Sam.
"to ai ke banda abinki ai jama'a rahma ne, ko baka da arziki na kudi, Allah ya baka arzikin jama'a ai angama maka komai." cewar Hajya kaka. 
Kaka ga sinasir Nan dai, Nan sumayya ta fara mata bude buden kwanuka tana Hajya kaka me zamu samu ne? Danko kakartasu bata rabo da kayan makulashe kamn su dambun nama da suransu.
"ba abinda xaku samu, anzo a yasheni inda aka saba ko? Cewar kaka.
"laa! Wato fadama jama'a kike cewa in munxo yasheki mukeyi ko kaka? Aiko bazaki kara ganin mu a gidannan ba." inji sumayya.
"yar kusan uwa, yanxu ma xaku iya tashi Ku fita, yanda kuka kawo girman Nan dama ai auran Ku ya matso, ba bokon da xa kuyi tunda Ku jikin girma gareku kamn Kazan agaric(agric )."
"tab! Lallai ma wanann hajyan, to wlh kima daina mganan Nan kwata kwata, mu din har guda nawa muke." surayya ta fada tana mai kwanciya bisa cinyan kakartasu. Sumayya Kam ta tadda muricci adakin sai barewa takeyi tana kaiwa baki.
Haka sukaita hira da raha da kakartasu mai matukar sansu.
Can suka tambayeta ko Aunty fa'ixa taxo ranan Monday din?
Hajya kaka ta rike haba ta ce "wai!, ni ban sa ran zuwan auta Nan kusa, ai ba haka akeyi ba. Karkari ace sai tayi wata uku ko hudu."
Tabdi! aiko Aunty faixa bazata iyaba na sani, kubata Nan da sati daya zaku ga tazo, kilan ma baxai kai ba. Inji sumayya. 
To kaka ai ke ya kamata ki fara zuwaa, yaushe xaki mu rakaki?? 
A'a ba yanxu ba, inji Hajya kakus.

4:00 pm a gidan Hajya kaka*
Yaran Nan halan yau baxaku islamia bane, ko kunfiso sai kunyi latti? Inji kaka.
"a'a ba inda xamu yau, cewar. Surayya, ni wlh nama tsani islamian Nan , kinaji kaka, wani Dan rainin wayan malami ne aka kawo mana kumafa wai kullun sai ya shigo ajin mu ya koyar damu" not fair at all.

Kul surayya malamin naku ne marainin wayan naki?kar in kara ji wannan ai rashin kunya ne. Cewar kaka. 
"yauwa Hajya kaka Dan Allah ki fada ma blad ta rage tsiwa, mutuminnan ba abinda ya mata amma ta riga ta gama tsananshi ba dalili." inji sumayya. 
Aw wato tsanarshi kikayi ko surayya to ki cigaba ina Nan ina jira Randa xakizo kifara ban lbrn soyayyarku ai. Hajya kaka ta fada.
Tabdi jam amma wlh kin gama Dani kaka , nidai kumin shiru kar kusa raina ya baci. Surayya ta fada ta waiga tana auna ma sumayya harara.
Sumayya na kallanta ta lumshe ido dama tana kwance Kan doguwan kujera ne tanaji kamn xaxxabinta xe dawo, bata shirya jin masifan blad dinta ba da alama sun tsokano ta ita da kakus dinsu.

Mallaka
Faumsyk family
Ammin Eemad

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now