episode 14

27 1 0
                                    

*KAWANCEN MU•*
2017
MALLAKA..... FAUMSYK FAMILY

*Baya wata daya.*

RANAN SALLAH!
A wannan rana gabaki daya daukacin jama'a musulmai na cikin farin ciki. Suma haka kap iyalan Abba kyaudai ba'a barsu a baya ba. Kowata sallah wato eid fitr sukan kai ziyara kauyensu na kyaudai a ran biyun sallah. Duk Da cewa iyayensu basa a kauyen amma akwai kanninsu Da baffaninsu, to Dan Sam basu yada zumunci ba.
Mota biyar suka cika kafin su mike hanya. Isarsu keda wuya aka tarbesu Da tsananin farinciki, aka basu makulin gidansu na kauye wanda tuni yasha gyara sanadiyyan xuwan su. Isarsu bada dadewa ba saiga baba sallihu na Abuja ya taho shima Da iyalanshi. Wannan shiyasa yaran ABBA suka cika chip banda Aunty faixa, todan ita mijinta ba Dan kyaudai bane aure yakin mata, dole ta hakura tai nata shagalin Da familyn mijinta. Haka zalika a jikoki ba Aunty safiya diyar kawu sallihu sai Kuma Yaya FADEEL Da ake can kasar turawa . Idan aka dauke waennan ba wanda be halarci ziyaran ba. Rago guda aka musu dashishin shi gunun dadi aka kawo musu tare Da fura Da nono, sai Kuma kaji en hausa.
Bangaren iyayen ma sun bada taimako ba kadan ba domin kudi suka raba sosai ga mabukata, tun daga kan manya magidanta har yara en makaranta. To Dan duk wanda ya taho Da matsalla saida suka magance mai ya tashi ya tafi cikin farinciki tare Da shi albarka.
Matan kuwa tundaga kan Hajya kaka, surikanta har xuwa kan su sumayya Da surayya gida gida suka shiga, tare Da ajiye musu abin daya sauwaka daga kan atamphophi Da takalma Da dai sauran kaya masu daraja na amfani.
Bayan dare yayi sun nitsa cikin gidan su ne , umman Yaya fadeel ta ke kallon su sumayya cike Da sh'awa, Chan dai tace ai yayan ku FADEEL shima ya kusa karkare karatunshi tas ya dawo cikin ku, inshaallah babban salllah Da shi xaa yi a Nigeria. Cike Da farinciki su surayya suka rike hannun juna suna farinciki, sumayya tace "ai wlh umma Yaya fadeel ya dade baya tare damu ni harna kusa manta kamannin shi Allah kuwa. Surayya kam ba baki sai ido, duk Da dai ta kasa rufe bakin wajan dariya, ambaton Yaya fadeel ya kusa dawowa ba karamin farinciki ya sata ba. Sumayya kam sai zungurinta take Da kafa tana tsokananta , kunya ce dai ta hana ta magana. 
Basu bar inda suke ba saiga Yaya fadeel ya kira ummanshi a Waya, aikuwa bayan sun gaisa ne ta ce mai ga kanninka nan ku gaisa , kowa gashi nan a kauye ai banda kai. Tana mika musu wayan ta tashi ta tafi wajan su Mommy a can inda suke. Aikuwa sumayya na daukan wayan tasa a handsfree, to Dan ita ta fara gaishe shi, nan take yace akoke ne ko mai 'kashi daya?? Charap surayya ta chabe Da kai Yaya nidai surayya sunana ba mai 'kashi daya ba. Ta fada tana dariya. Shiko cewa yayi inaa ai ni first appearance matters kina nan a mai 'kashi daya to me, Allah dai yasa kin daina Marin maza ko. Nan take suka kwashe Da dariya. Sumayya tun bayan gaisawan Da sukayi bata kara cewa komai ba ta bar surayya Da Yaya fadeel suyi ta zantawa to Dan sun dade basu hadu ba kam!!

Washegari bayan sun tashi ne suka kimtsa suka Kuma kara daukan hanya xuwa cikin zaria, inda shima can duk ziyaran suka kai. A gidan su abokiyar wasan su daddy ne su surayy suka ce a barsu su kara kwana to dan sunada gidan en school dinsu Da zasu dayawa, harda gidan su haneefa. Tare dai Da chewng gum din nasu aka barsu wato Yaya nazeefi, inda xe kaisu inda xasu washegari su juyo gida.
A gidansu su haneefa sun sha ihu Da murnan haduwan yaushe gamo. Bayan sun nitsa ne suke tambayanta lbrn saurayintan nan, to Dan sunfa manta Da sunanshi. Haneefa tace hmmm ai BAA magana to Dan AFFAN ashe dgsk yaudarata yakeyi , ashe komawa yayi yana dating best frnd dina mgn Da mukeyi yanxu bayan sallan nan bikin su fa. Da mamaki suka bude baki suna kallanta domin zancen ya Blain girgixa su surayya, har suke cewa meyasa maxa ke haka ne wai?
"Kuma kunsan wanda aka Taba ma haka ne?" cewar haneefa. A'a suka hada baki suka fada, abin dai ya bamu mamaki ne kawai wlh. To Dan su surayya sun iya ajiye sirri tsakanin su sosai, Sam baxasu bari mgn saleem ya karade kawayen su ba. Maza kuwa sunsha zagi, a yayinda sumayya laifin saurayin take gani, itako surayya tace Sam laifin na kawar ce sbd ita tabada fuska ta munafirci kawanta aminiyarta..!
Da daddare suna xaune suna hira saiga wayan sha'awa emmatan jos ya shigo, video call ta musu. Bayan sun gama gaisawa ne take tambayan sumayya ko yaushe zasu shigo??
" ke sha'awa kicire rai Da zuwan mu nan kusa wlh jos ta fitan min a rai yanxu" cewar sumayya. 
"kambu! Kin ma Isa!? Bayan kin gama mana alkawari xaki shigo Da surayya wlh baki Isa ba. To kisani an kusa ma auren bintu bayan babban sallah. Surayya kina jin wannan shegiyar kawar taki ko?? Sh'awa ta fada rai a bace.
"a' a yada Zagin min er uwa?" surayyata ce. Ta cigaba Da, Dan garinku ya mana abin Da BAA Taba mana ba, baxamu shigo yanxu ba gskya sai mun dau FANSA.
"ban gane ba wai kuna nufin wannan guy din Da sumayya ta hadu Da? Mema sunanshi? Inji shaawa.
Surayya tace eh wllh kedai bari sis its a long story wlh.
"a'a Dan Allah tell me in details damn wannan ni be kwanta min ba me ya muku ne?? Shawa ta tambaya curiously.
Nan dai sumayya Da surayya suka kwashe lbr tas suka fada mata.
Tun kafin su dire sha'awa keta Watso ashar ba kakkautawa, suna direwa kuwa tace su bata details dinshi tasa goons su koya mai hankali a garin jos.
Nan take sumayya tace keee a'a we hav a plan amman in be yiwu ba zamu nemeki.
"to hell with ur plans, Dan Allah ku bari abi jikin shege halan abin be xafeku bane ko?? Inji sha'awa.
A'a kin ganeko, indai akace duka xaa mai ba xe San mu muka sa a mai ba, ko Kuma idan Yama sani ze iya kai kara kinga mu anan xamu iya shiga matsala dasu daddy. Ki bari mubi abin a hankali inda xefi shiganshi. Su surayya suke mata bayani.
Owk u hav a point kam. Amma let me hear ur plans dai. Inji sha'awa. Nan take suka fada mata ta fara ihu kamn xata rungumme su, wlh plan din yayi Allah yasa yayi working dai, inji shaawa. 
Nan dai sukai sallama gaba dayansu. (ni ko nace tab su sha'awa b'a jin gari, wannan uban hira a video chat haka....lol )

AMMIN EEMAAD.

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now