episode 15

23 1 0
                                    

KAWANCEN MU*
2017

MALLAKA......FAUMSYK FAMILY.

Washe gari a hanyansu ta komawa gida kaduna, surayya suna Dan Taba hira Da yayansu, Chan suka ce Yaya wai ina wannan abokin Naka Isa POlICE?? Yana nan kuwa?
Shegge Isa, yana nan wlh kifin rijiya ne har yau anki mai transfer, yana nan yanxu a police station din rigachikun yake. Da axumi ma muna tare ai Da shi.
Oh ashe yana nan kwana biu ya dena xuwa gaida su umma , inji sumayya. 
Ke aiki ya mai yawa ne inaga, amma kiln ya taho cikin satin sallan nan. Inji naxeefi.
Yauwa Yaya yaxo ya bamu goron sallah..-nji sumayya.
Mtsss barauniya se ki danne shi ku kwata, wai ku pirda pirda daku kun Isa ajiye iyali ne xaa ba wani barka Da sallah? Ku ce samarinku su turo kawai a aurar Da ku, in kuka ki inaga sai na rigaku aure ba abinda ya damen. Inji naxeefi.
Nan su sumayya suka kwashe Da dariya, kafin su kace mu ba ruwan mu Allah bamu Da saurayi ba bama kula kowa.
Nan ma dai tsakin naxeefin ya kara ja alamun xancen be shige shi ba.

Shiru ne ya Dan ratsa kadan, saidai surayya Da sumayya nata kus kus. Magn suke son yi ammn an rasa wanda xe fara. Chan Da surayya ta fara Da 
"pls Yaya we need ur help". Ya waigo ya kalleta kadan ammn be ce komai ba, saida ta sumayya ta kara Da kaji Dan Allah kafin shima yace yana jin su.
Surayya tace Ka Tina sanda Ka hadu damu gidan aunt faixa ?? Murmushi naxeefi yayi ta gefen fuska kafin yace ina jinku sarakan rigima.
Nan Dai suka fara bashi labr tiryan tiryan Da yanda saleem yaso ruguxa musu kawancen su.

Buden bakin Yaya naxeefi sai cewa yayi amma mata karamn kwakwalwa gareku, in ba haka ba tun a farkon haduwanku ya kamata ku gane shi din wani iri ne. Mutumin Da even for once beyi tunanin tambayanku inda iyayenku suke ba Balle aje magn yaje ya gaishe su ai mayaudari ne kawai. Sbd haka aunt faixa tayi dai dai Da tace ya xama dole ku rabu dashi ku nisanta kanku Da shi sosai .
"eh hakane Yaya amma ya xama dole mu koya mai lesson inda nan gaba xeji tsoron kara taron wata Da sunan yaudara or sth similar, Allah Yaya baxeci bulus musamman ma tunda ya tabamu Da blad dina." cewar su sumayya Da surayya.
Yeah not bad idea, yanxu me kuke tunanin xaa mai?? Naxeefi ya tambayesu cike Da kulawa. Ko suma dai sunyi mamakin yanda ya sauko Da kai yana saurarensu to Dan at firs sun dauka zaki zasu sha. Lallai Dan uwa rabin jiki a duniya babu kamarshi (one love faumsyk family).
Buden bakin su sai cewa sukayi, yauwa Yaya abokin Ka Isa xaka sa ya kamashi ya kulle shi a cell sai ya wahala kafin a sako shi.
Ba shiri naxeefi ya waigo ya kallesu kafin yace "sannu Sara! Zahra buhari ko ince zahra indimi, ko Kuma nuwaira Da nawwara yusuf gwaiba." (yan gidan gwaiba. By kawata DIMPLES). Tunda ubanku ya koshi ya tada kai Da naira dole kuce a aika Da police a kamoshi. look I'm not buying dis ur idea " kafin ya maida kanshi ya cgba Da tuki.
Kallon kallo su surayya suka fara kafin surayya ta karfin halin cewa. Yaya naxeefi we hav plans ta yanda xaa kamoshi tunda aikinshi ne yaudara. Dan Allah Yaya munefa adorable siss dinka Dan Allah do dis one thing for us kaji Yayan mu na kanmu angon rabi bada kanka a sare.
Nan dai yayi dariya kafin yace let me hear ur plans first, talk to Isa nd den c hw things would b sort out. Nan sukai ihun murna tare Da jin dadin yanda yayansu ya basu full support. 
Yanxu first step din Da xata fara shine surayya ta maida sim dinta ta Kuma koma whatsapp data bari Da sbd shiga axumi. Sun San dole saleem player ya nemeta wanda shine hanya Mafi sauki na ganin ya fada trap dinsu.
Isarsu gida bada dadewa ba suka tadda Aunty faixa itama taxo, tayi haske sosai sai Kuma Dan kiba Da ta kara, Da alama ta samu ne. Nan suka shahanshe Da hira itama bata rasa na basu ba, tace famyln ibrahm muazzam suna Da mutunci taji dadin yin shagallin sallah cikin su. Anan ne take kara sanar dasu tafiyansu Uganda fa ya matso itada mijin ta, ya samu aiki a wani firm as there attorney so Da ita duk xasu koma can.!
*** ***

Da dare yayi surayya batayi kasa a gwiwa ba ta wajan maida sim dinta, ta Kuma kara downloadingwhatsapp kmn yanda suka tsara. Text messages suka dnga shigowa iriri as expected harda na saleem. Wasu Da ramadan wasu na happy eid. 
Tabe baki tayi kafin ta mai reply Da TNX.
Bangaren sumayya kam Dan duniyar Sam be nmeta ba, dgske yake ya daina yayinta to Dan Sam yanxu bata cikin agenda dnshi.
Saida washegari yayi kafin saleem yaga reply din surayya, shi din baya jin dadi ne yanayin jiki Da jini. Ganin text din surayya take yaji wani karfi ya taho mishi, jikinshi har rawa yakeyi wajan ganin yayi dialing numbern ta. He misses her so very much, yanayin Da yake ji akanta daban ne to Dan ko shi yana mamakin kanshi ba kadan ba.
Call na uku kenan Da ya shigo wayan surayya Da misalin karfe bakwai Da rabi na safe. Tsaf take kallon kiran. Xuciyanta ke mata zafi ba kadan ba, tsana me tsanani take ji game dashi musamman ma idan ta tuna abun daya musu. Saida ya sake kira a karo na 4 kafin tai karfin halin dauka.
Sallama ya fara cike Da zumudi, ita Kuma ta amsa murya Sam ba walwala.
"kinyi sallah lafya angel? Ya kk ya kwana biyu??" 
""lfy" surayya ta bada amsa.
"I m glad to hear dat" saleem ya fada. Can Kuma su shiru ya biyo baya to Dan shi kanshi ya rasa ta ina xe fara. 
"sai anjima" yaji ta fada. Nan take yace to angel zan kira anjima inshaallah. Thank u, thank u so very mu...," bai idaba ta katse wayan tana mai Jan dogon tsaki. Nan take ta lalibo numbern blad ta fesa mata cewa wahalallan ya kira.
Ajiyan xuciya sumayya ta sauke tana mai mamakin halin rayuwa. Ita din meke gareta Da yasa mutane basu cika Santa ba? Koda ta samu mai Santa to inshaallah Da default tare dashi misalin saleem Da Kuma black. YA MUSTA'AN Ka kawo min mafita. Ta fada.

Da yamma Da misalin karfe biyar, saiga Isa police abokin yayansu ya shigo, bayan sun gaisa Da iyayenshi ne naxeefi ya zayyene mai bukatan kannishi. Do u think is possible? Ya tambayam
Eh to yanxu dai Ka kirasu sai Muga ya xamuyi. Inji isah.
Bayan su sumayya sun hadu ne a garden din dake cikinsu isah ya cika Da mamakin ganin yanda emmatan suka kara girma gwanin sha'awa.
"ah lallai abokina kanninka ne haka? Gskya ni nasamu iri Allah sai inda karfina ya Kare wajn ganin na faranta musu." cewar Isa.
"ah kai saurara. Ban San tsiya dnt try messing up with my siss." naxeefi ya fada yana mai hada rai.
Dai dai lokacin su surayya suka karaso hannunsu cike Da kayan makwalashe. Bayan sun gaisa ne cike Da barkwanci, naxeefi yace su abn daya kawo su besan shirme. Hankalin isah yafi karkata sosai kan SURAYYA.
Bayan sun kara maida xance ne suka ce yanxu ya kake ganin Xai faru??
Kar ku damu emmata, koda ma ace yanada connections, to be kai wanda ni kedashi ba cikin police station. Sbd haka kusan yanda xaayi ku kawoshi cikin cikin kd, sai a daura mai er laifi no matter how little, Da ya shigo hannun mu xeci ubanshi ne kar ku damu.

Cike Da farinciki su sumayya ke ta mai godiya. Sunce nan Da kwana biu xasu shigo dashi kd ayi komai a gama ba bata lokaci Sam.
"yauwa to ku ban Numbern wayanku ko Kuma ke surayya ban naki for communication purpose." isah sa ya fada yana mai washe hakora...
"kai xaka fa kaci ubanka ne", inji naxeefi 
Ku angama daku , Meye Kuma kuka tsaya jira? Komeye xaayi let me b intermediary of d communications. Cewar Yaya naxeefi!!!

AMMIN EEMMAD

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now