episode 24

23 4 0
                                    

*KAWANCEN MU*

MALLAKA.......FAUMSYK FAMILY.

*_I really do hate it when two best frnds fought, whereas its just a misunderstanding. Allah ka tsare mu daga sharrin shaidan ameen_*

Kar ki damu surayya, kedin har nawa kike da kowa xe nemi ya juya miki baya?  Gobe dake xan tafi insha Allah, bar kuka ki kwanta kiyi barci kinji. Damn dayake tana fashin sallah saita koma ta kwanta. Har yanxu bata bar hawaye ba. Tunani dayawa ke damunta ta rasa wanne xatayi, amma bata jin na blad sosai to dan basu taba haka ba, bata ma san meye ta mata ba. Amma tasan dole nema su dinke. Chan saiga yaya fadeel ya fado mata. Batason tana tunaninshi da sauri ta kara kudindinewa tare da sakin kuka. Saida dare yayi nisa sosai kafin bacci ya dauke surayya a wannan ranan. Kanta kamn ta cire ta ajiye a gefe.

Washegari da sassafe umma naja ta samu su abba tace da surayya xata koma Gombe yau. Ta hade gida sosai dole yasa abba yarda kafin sanda hutunsu xai kare.

Wajan karfe 8am , Muhammad ya taho kofar gidan su surayya. Kallo daya xaka mishi ka gane bayida natsuwa. Jiya a islamia bayn surayya ta suma ne yakejin wai ashe har marinta akayi. Ranshi ya baci ba kadan ba. Sam be samu sukuni ba jiya. A yau ne kuma da asussuba aka mai waya da cewa mahaifinshi ya fadi unconscious har yanxu be farfado ba. Hankalin Muhammad ya masifan tashi. Da sauri ya dau jakanshi da niyyar komawa katsina. Har ya fito kuma ya tuna da surayya. Bejin xe samu natsuwa inba yaje yaji yanda take ba.

A kofar gidansu yaci karo da Abba. Dayake abba ya shaida shi suka gaisa . Abba ya dora da" kuyi hkr dan Allah da rashin kunyan da surayya ta muku jiya. Har yau tana kan amsan hukunci."

Da sauri Muhammad ya chapke da a'a Abba, dan Allah kar kuyi mata komai, ku duba yanayinta sosai kmn bata Da lafya ne. Nasan kila bata taba yin haka ba, wlh bansan sanda aka daketa ba da baxn bari ba.

Abba ya tsaya yayi shiru. Tabbas surayya bata taba haka ba. Kiln dai bata da lafyan ne dagske amma xe bincika ya gani. Muhammad ya kara da, abba nazo nai muku sallama ne xan wuce katsina mahaifina bayi da lafya. Nan take rashin jindadi ya sauka fuskan abba ya kuma mai adduan samun sauki.

Muhammad ya daura da dan Allah inba damuwa ina so inga surayya in kara duba jikinta in mata sallama. Abba yace ba damuwa ya shigo dashi parlour, to dan ya yaba da hankalin yaron.

Abba ya tura kiran surayya da cewa taje parlour tayi bako. Surayya ta fito dg wanka tanasa kaya tji kiran. Jikinta sam ba karfi ta sa hijjab ta wuce. Gabanta na faduwa. Tana shiga da sallama kawai ta tadda mallam Muhammad. Tsayawa tayi tana kallonshi. Shiko da sauri ya mike. Yanayin da yaganta yasa shi rufe idanuwanshi da karfi ya furxar da iska dg bakinshi. ya budesu Kafin yace. " surayya! Kiyi hkr. Kiyi hkr da duk abinda ya faru. Ki yi hkr nasan laifina ne, tunda sbd ni haka ya faru.

Surayya kam kamn jira take, nan take hawayenta ya balle. Sam a yau dai malam Muhammad be bata haushi ba. Damn neman me bata hakuri takeyi ko ta danji sauki a ranta. Fuskanta cike da hawaye ba zato ba tsammani Muhammad yaji surayya tace . Nima kayi hkr malam, duk abubuwan da nake maka kayi hkr kaji.

Yace a'a nine dai na hanaki sakat a rayuwa dan Allah kiyi hkr. Ita dai bata daina Sharban kuka ba. Muhammad ya kara da surayya naxo na miki sallama ne, bana jin xan kara dowo wa kaduna nan kusa. Babana bayi da lfya xan tafi nemo mai magani.Amma kafin na tafi ya zama dole na fada miki abinda ke raina. Suryya ina sonki, nafara sanki tun dg randa Allah yasa na fara ganinki. Ni kaina bansan adadin san da nike miki ba, burina in aureki surayya.

Chak surayya ta tsaya da kuka ta dago kai tana kallanshi cike da mamaki. Sosai taji mamaki . Muhammad nagama fada mata yace na barki lafya surayya, ya fita ya bar parlour da gidan gaba daya. Koba komai ya dan ragema xuciyanshi kaya.

Surayya kam zama tayi dabas kan kujera. Yanxu an kara mata damuwa kan damuwa. Sam ta rasa tunanin da xatayi kuma. Mallam Muhammad na santa!  Ikon Allah abin be taba xuwa mata rai ba sam.

Jiki a sanyaye ta koma ciki. Umma naja tace mata ta karya taxo su tafi.kadan taci abincin ta dauko akwatinta na tafiya. Wajan abbanta taje tamai sallama ta kara da umma da abba dan Allah kuyi hkr. Abban ta sai yanxu ya kara lura kmn bata da lafiyan. Nan ya tambayeta tayi shiru. Yace in wani abu na damunki ki fada akaiki hospital kinji. Tace to. Anan ne suka sa mata albarka.

Surayya da umma naja suka dga gombe tare da driven ta taxo dashi. Kiri kiri surayya taki shiga ko ina tai musu sallama. Ko gidan kakan su taki shiga fushi take da ita sbd ita ta ta fada mata mumunar lbr kan fadeel. Sannan haushin blad dinta takeji itama kwata kwata bata san ganinta. Ko wayanta ma bata dauka ba bama tasan inda yake ba!

Bangaren SUMAYYA kuwa bayan ta koma gida sharban kuka kawai takeyi. Ta riga ta gama sakankancewa surayya taci amnarta. Itako meta tsarewa surayya a rayuwa. In samarin ne tafita, kyau ma tafita, kai kusan komai ta fita amma take mata bakin cikin da abun da ta samu. Bata jin xata iya yafe mata wannan karan dole ta dau mataki kwatankwacin yanda ta bakanta mata.!

Koda safiya tayi taji lbrn surayya ta wuce gombe, kuma taji wai har duka tasha jiya a gida. Sam xuciyarta ko dar beyi ba in banda tsanarta daya kara samun matsuguni.(niko maman eemad nace wayyo, gashi yanxu ba me baku shawara. Sam banji dadin fadan nan ba).

Rayuwan gidansu sam saiya dawo baya mata dadi. Kullun cikin kunci take, haka yasa ta koma gidan hajya kaka da zama. A chan dinma bata chanxa xani ba, kullun sai tayi kuka, kallo daya xaka mata ka gane tana cikin kunci. Hajya kaka tayi tambayan duniyan nan taki cewa komai. Tayi fadan har ta gaji.
Sumayya tana nan tana tunanin irin ramuwar gayyan da xatawa surayya. Tun bayan da surayya ta tafi gombe ko sau daya bata nemeta ba. Gashi shima taufeeq kamn anyi ruwa an dauke sam be nemeta ba shima.

Zuciyanta tuni ta gama kitsa mata cewa suna chan suna cin amanarta da surayya sun maidata gaula.

Hajya kaka da ta gama gajya da yanda take ganin sumayya saita dawo lallashi. Tace ' sumayya nifa kakar kice kuma kawarki, ki fada mn meke damunki dan Allah. Ko kinyi fada da surayya ne?? Tace a'a.
To ko wani kikeso shi yace baya yi kika daga hankalinki sumayya?

Da sauri sumayya ta Waigo ta kalli kaka. Hajya kaka n.a. ganin haka tace kar ki damu ki fada mn ko waye. Indai me yiwu wane to inshaallah sai inda karfi na ya kare xaki sameshi kinji.

Cikin sanyin murya sumayya tace. Kaka YAYA FADEEL NAKESO, NA DADE INA DAUKE DA SANSHI. DAN ALLAH KI TAIMAKENI IN AURESHI! !! (Niko maman eemad da sauri naja baya ina dafe kirji nace what!!!! Sumayya hankalinki daya kuwa???)

A take hajya kaka ta rangada guda iya karfinta tare da rungume sumayya cikin doki. Kafin dg bisani tace. Ki kwantar da hankalinki. Kisawa ranki kin samu fadeel kin gama a rayuwa. A take kuma ta latso waya ta kira babban danta da cewa tana neman su cikin gaggawa su fadiwa har salihu su taho gobe cikin shiri.!!

AMMIN EEMAAD ♥♥♥♥♥

'KAWANCEN MUWhere stories live. Discover now