3

44 10 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal

03
Fauzan Abubakar Umar, haifaffen garin Kano ne inda a nan yayi makarantar firamare da sakandare, bayan yayi Ijmb ne ya samu admission a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria . Yana shirin tafiya ne Allah yayi wa Mahaifiyarsa Hajiya Maimuna rasuwa wadda ta rasu ta bar  yaya hudu(4) Fatima, Fauzan, Faruk da Fadila.

Mahaifinsa Alhaji Abubakar Umar babban ma'aikacin gwamnati ne a jihar Kano. Mutum ne mai tsantseni da kokarin kare mutuncinsa. Wannan ya sa koda Fauzan ya gama karatun degree na farko, maimakon ya karbi takardunsa ya rabawa abokan aikinsa ko ya Kai ma'aikatar sa don a dauki dansa aiki, baiyi haka ba saboda a cewarsa, yanzu duk wanda yayi maka alfarma to fa shima zai dawo yace ka rama masa koda kuwa bai cancanci samun wannan alfarmar ba. Saboda haka ya biya masa kudi yaje yayi degree na biyu, duk a wannan lokacin kuwa Fauzan na tare da Anisa.

Har ya kammala bai samu aiki ba, a irin wannan yanayin ne aka yi bikinsu, a lokacin ita kuma ta gama 200 level. A cikin abokan baban Fauzan da suka zo daurin aure wani ya karba takardunsa yayi masa hanya aka dauke shi aiki a access bank. Fauzan yana ta farin ciki, yan uwa ana ta murna ai Fauzan zai yi kudi. Sai dai abinda basu sani ba, aikin banki nada matukar wahala ballantana Kuma a irin wannan lokacin da gwamnatin kasa take yaki da cin hanci da rashawa. Mutum ya fita tun safe bazai dawo ba sai yamma, wataran a zaune haka zai yini, ga matsalar mu'amala da mutane iri iri, shi yasa Fauzan yafi son fita neman kostomomi.

Haka wataran zai kwaso bacin ranshi yazo gida yana juyewa Anisa, kuskure kalilan zatayi Sai ya hauta da fada ko hantara. Tun tana yin shiru har ita ma ta koya fadan, duk abinda ya fada mata sai ta bashi amsa, daga baya kuma da ta fuskanci hakan ba tarbiyya bace mai kyau, zasu lalata rayuwar gidan aurensu ne sai ta dena biye masa, in ta san tayi masa laifi sai ta bashi hakuri, amman in ta san neman rigima kawai yake sai ta shige daki ta kyale shi.Har ga Allah Fauzan ba a son ransa yake yiwa Anisa masifa ba, to amman shi kansa ya rasa dalili. Ladabi da biyayya babu irin wanda batayi masa, matsala guda daya da ya sani ita ce baya samun nutsuwa a yayin da ya kusance ta. A budurwa ya same ta koda sukai aure, Kuma shima bai taba muamala da wata ya mace ba bayan Anisa. Shi dai yadda yake ji abokansa suna dokin abun, shi fa ba haka bane a gurinsa.

Fauzan Kai yayi zafi a office, bai ma bi ta kan wayarsa ba sai da ya fito zai tafi gida, koda yaga text din Anisa murmushi kawai yayi, a zuciyarsa yace ai na san baki da kudin mota ba inda zaki iya tafiya. Sai da ya isa gida ne sannan ya tabbatar, aiko ranshi ya dugunzuma ya baci, ya dauki waya yayi wa Anisa kira har sau biyar bata dauka ba, har zai rubuta text yace ina ai baza ta ji zafin abinda zan fada mata ba. Zai kara kira wayar ta nuna alamun babu caji, yayi jifa da ita a kan kujera. Ranar dai haka Fauzan ya kwana Suzuki, ga bakin cikin abinda Anisa tayi masa, gashi kuma babu ita a kusa dashi ballantana ya danji duminta.
😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now