15

36 8 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal

15
Assalamu Alaikum" inji Saude matar Tijjani. Anisa da take kitchen ta amsa mata da WA alaikumussalam. Ta fito parlour suka gaisa, ita dai Anisa a ranta cewa takeyi wannan wace irin mata ce, kullum tana hanyar gidan mutane, ni sau daya na taba shiga gidanta, ga tsegumi da iyayi da shishshigi.

Ji tai an taba ta, Saude tace "tunanin mi kikai ina ta dumi ni dai" (cikin hausarta ta sakkwatawa)

Anisa tayi mata yake tace "yi hakuri me kike cewa"
Saude tace "hakin maye na ni kawo miki, don naga alama kina wasa da harka, baki karbar kudi gun oga"
Anisa tace "meye kuma hakin maye, kuma ban gane bana karbar kudi gun oga ba"
Saude tace "kayan gyara mace nake nuhi" ta cigaba da cewa "yo gani niyi kinyi wata guda garin ga amman ya bar miki daki kamar kango, ya za ayi ya kasa siya miki furnitures, kin san yawan kudin da suka samu wurin aikinga nasu ko. Ko satinga da ya wuce sai da aka basu alawus na dubu dari.Anisa tace "to kuma da aka basu sai shi kuma mijinki ya dauka ya baki ko"

Saude tayi dariya tace "yo ba dolensa ba, ai indai kikai amfani da wannan garin maganin, har ATM card dinsa sai ya bar miki a hannunki"

Anisa tace "ni bani da kudi yanzu sai dai ki bari zanzo in siya in na samu"

Saude tace "haba ai ba komi kyauta ni kawo miki, anshi nan, da madara zaki sha"

Anisa ta karba tayi godiya, a zuciyar ta tace ba abinda zansha.

Saude tace "yau da daddare zamuje shopping da baban Nabil, kema kice da baban Suhaima Ya kaiki sai mu tafi tare"

Anisa tace "ai ni bana zuwa shopping, shi yake zuwa ya siyo duk wani abu da muke bukata "Saude ta kwashe da dariya tace "amman dai Anisa secondary school dai kin kayi aka yi miki aure ko"
Anisa tace " me kika gani"
Saude tace "ai naga kawai mijinki wayo yake miki, abinda yace shi dai kika bi. Kin ganni nan sai abinda naka so akai a gidana, kuma shopping every month muka zuwa in zaba duk abinda raina kaso ,har kanne na da iyaye na naka yiwa siyayya"
Anisa tace "hakan yana da kyau ai, halan ke kinyi jami'a"
Saudat tace "awo nayi diploma a cikin danfodiyo, kin san miji na yana kauna ta shi ya biya min"
Anisa tace "gaskiya ya kyauta kam" ta tashi ta kawo mata ruwa da faten dankalin Hausa.

Ta cinye tsab sai kuma tace "ni kam ba a siyo miki dankalin turawa ne?
Anisa tace "kin san yanzu gabatowar azumi yayi tsada, kuma na hausan ma ai naga ana sarrafa shi kala kala, kinga ana dafa shi sannan a soya da kwai, ko a daka a fasa kwai a ciki a sa kayan hadi sai a soya shi kamar kosai, ko a daka a sa kayan hadi sai a dunkule shi kamar yam balls ana sawa a cikin kwai ana soyawa"
Saudat tace "kedai da iya girkinnan naki, amman dai gaskiya ki dinga sawa mijinki yana siyo miki kayan dadi, dankalin hausa fa basir yake sawa"
Anisa tace "ni kuma naji kamar ance na hausa yafi amfani a jiki, kuma ni abinci kowane iri ne aka kawo min bani da matsala ci zanyi"Suhaima ce tace "Umma abil kashami yayi cilali a wando "
Anisa ta tashi ta dakko ruwa da tsumma ta sawa yaron sannan ta goge gurin, take ce ma Saude "gaskiya ya kamata ki koya masa in yana jin fitsari yace zeyi, naga ai kamar sa'an Suhaima ne, ya shekara biyu ko"
Tace "eh, to ke da ba carpet a parlon naki meye na damuwa don an miki fitsari "

Kwafa kawai Anisa tayi bata ce mata komai ba.

Kullum haka hirarsu take kasancewa da makociyar tata, rainin hankali Kala Kala Saude take kawo wa Anisa, ga nuna ita 'yar gaban goshin mijinta ce, ga karyar boko. Rannan har tambayar Anisa tayi wai atamfofinta super guda nawa ne, Anisa tayi mata shiru kamar bata jita ba, sai ta cigaba da magana wai ai ita duk sallah sai mijinta ya dinka mata super England da super Holland.Da Anisa take bawa Fauzan labari yayi dariya yace "ai daga ganin wannan matar daga kauye ta fito, me shi ai baya fada sai dai a gani"

Anisa ta gama girki, tayi wanka ta ci kwalliya tana jiran dawowar megidan ta. Tana zaune take tuna zancen Saudat na dazu, a zuciyar ta Anisa tace "duk macen da ta dogara da maganin mata wajen juya miji tabbas tayi wa kanta gurguwar dabara, to randa babu maganin kuma fa? an samu matsala kenan. Zancen kuma wai ita namiji be isa ba duk karya ce, ko asiri mace tayi wa namiji wataran ai ze karye, kuma shi namiji ya san hanyoyi da dama da zaiyi maganin mace koda kuwa ya nuna mata kamar yana biye mata yana duk abinda take so, idan ya tashi kunsa mata wani bakin cikin sai ta rasa inda zata sa kanta.

shigowar motarsa taji, tana kokarin kwantar da Suhaima ita ma ta tashi tana fadin Abba ne, Anisa tayi murmushi tace 'yar gidan Abba shine. Suka fita suka taro shi ya karba Suhaima yana yi mata wasa.Bayan ya yi wanka yaci abinci ne yake ce mata "an siyar da kayan ki fa kuma sunyi daraja sosai, don har an turo min da kudin ma, ki shirya gobe sai muje ki zaba wasu a kasuwa" Anisa tace "to Allah Ya kaimu, daman na gaji da kwanciyar kasa"
Fauzan yayi dariya yace "kafin ki aure a ina kike kwanciya" tace "ai kasan ni yar gatan Umma da Abba ce ina da gado"
Yace "lallai kam yar gata"
Tace "amman fa gara da kace in siyar da kayana a Kano in yaso in muka zo nan in siya wasu, don wata kila a garin tahowa dasu duk su karye ma"
Fauzan yace "to daman tafiyar kusan awa shida, dubu nawa zan bayar a kwaso kayan, amman yanzu kinga sai ki sa sababbi ma abinki"

Furnitures lafiyayyu Fauzan Ya siyawa Anisa. Three bedrooms ne a gidan, ya sa kayan gado a daki biyu, daya dakin kuma ya sa kayan wasan Suhaima, bai sa mata gado ba saboda batayi girman da zata fara kwana ita kadai ba, cewa yai sai ta shekara bakwai tukunna. Parlon nan aka kawata shi da Turkish setting, gida ya fito gwanin ban sha'awa.Su Saude da yake bata nan ranar da aka kawo kayan, tayi shigowar tata ta safe da ta saba tayi kicibis da abin alheri, ai sai ta makale a bakin kofa. Anisa tayi tayi da ita ta shigo tace wai ai daman sauri takeyi Bari taje ta dawo. Haka ta fice ba Allah Ya sanya alheri.
😍😍😍😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now