20

33 6 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal

20
Inna Laure ce ta samo ruwa suka fara yayyafa mata suna shafa mata a fuska suna tofa mata Fatiha. Tana farfadowa ta sa kuka tana cewa "Innanmu ashe bakya so na, har da ke aka boye min wannan abu, shikenan yanzu "yan bakin ciki sai suji dadi, to ba inda zani na hakura da auren Tijjani gara kawai yazo ya sauwake m...."

Baba Ya daka mata tsawa, yace "wai ke mi ka damunki, ke wace ta da baki iya zama da kishiya. Ba a yin kishiyar aka auro Innarki, ita zuwa tayi ta tarar da wata, ke ki godewa Allah ke aka tarar" ya Kalli mahaifiyarta yace "ku tafi ki shirya ta maza yanzu zan maida ta gidanta da kaina"

bayan tafiyar su yace da Inna Laure da Anty amarya (kishiyoyin Innan Saudat ) "ku shirya tare zamuje" sannan Ya kira Tijjani Ya shaida masa suna nan tahowa yanzu.Amarya Maryam tayi musu tarba me kyau. Snacks da kaji da drinks ta zubo musu cikin plates, suna ta sanbarka don abinda Saudat bata taba yi musu ba kenan in suka zo gidanta. Ruwa ma sai sun roka.

Baba Ya hada su ukun yayi musu nasiha da fatan Allah Ya basu zaman lafiya, shi kuma mijinsu Allah Ya bashi ikon yin adalci a tsakaninsu, sannan suka tafi.

Bayan fitar su Baba, ta tashi ta shige dakinta ba tare da ta ce komai ba. Shigarta ne taga sabbin furnitures din da yayi mata, don tsofaffin nata gara duk ta ci su ko anyi musu painti bazasu moru ba. Ga kuma akwati guda biyu, ta bude ta ga kayan fadar kishiya ne. Tayi murmushi tace "kayi a banza " sallama Tijjani yayi ya shigo ta daga Kai ta Kalle shi ta galla masa harara tace "Mallam me ka shigo zaka min a daki "Ya samu gefen gado ya zauna yace "kwanan amarya ya kare, yau kwananki ne, gobe sai mu tattauna yanda rabon kwana zai Kama"batare da bata lokaci ba ta haushi da fada ta inda take shiga bata nan take fita bah a cikin Fadan take Cemasa ya koma can wurin amaryarsa ya kwana harda Karin zagi be tankata ba ya koma falo ya kwana.

Sallama Anisa taji kamar muryar Saudat, ta amsa daga daki ta fito ta ganta tace "ah Maman Nabil kin dawo ashe bismillah zauna mana"

Saudat ta harare ta tace "ba zama nazo yi ba, munafuka, muguwa, Ashe ba zaman tsakani da Allah kikeyi dani ba, kina kallo aka ci amana ta amman baki kira ni kin fada min ba. Da munafikin mijinki dashi aka hada baki"

Anisa ta daga mata hannu tace "kinga, baza ki zo har gidana ba ki zage ni kuma ki hada da mijina ba, ga hanya nan fita"

Saudat tayi shewa tace "Uwar son miji, ai ko baki fada ba tafiya zanyi kuma daga yau bani ba ke"

Anisa tace "Allah Ya raka taki gona"

~~~~~~~~~~~~~~~~~*~~~~~~~~~~~~~~

Tace "to jarababbe, ai ni na sallama ka, ka tafi inda amaryar ka bana son kwanan, don ba abinda zan baka, wato kazo ka tantance, to ba dani ba"

Ya mike "toh shikenan sai da safe"

Da sauri ta nufi kofa tace "lallai mutuminnan ka maishe ni sakarya, to ba inda zaka"

Yayi murmushi yace "to ki dena daga wa mutane murya dare yayi kuma ga danki nan kar ki tashe shi"

Tace "kodai kar amarya taji ina yi maka hukunci" ta Kara daga murya tace "ai wallahi daga kai har ita sai kun gane kuren ku, zanyi maganinku ne"

Bai kula ta ba ya shiga toilet din da yake a cikin dakin.

Da safe ne yake ce mata "na gyara miki can dakin na sa miki kujerunki"

Ta Kalle shi tace "ban gane ba, wanda suke parlor fa"

Yace "na Maryam ne"

Ta tashi a fusace ta fito ta shiga kitchen ta dakko ashana da kalanzir, ta fara zubawa a can carpet da kujera ya fito yace "Saudat kika sake kika kona mata kaya sai kin biya"
Bacin ran da ta gani a fuskarsa ya sa ta tsorata don shi ba mai saurin fushi bane. Karfin hali tayi tace " to indai ba tozarta ni kayi niyyar yi ba ka dawo min da kayana parlor na"Rayuwa tayi wa Saudat zafi, tayi biye biyen mallamai don ta kashe auren amarya da mijinta amman a banza. Ta sha tsokanar Maryam don ta biye mata suyi tashin hankali, amman taki kula ta. Haka shima mijin duk yadda tayi kokarin bata masa rai sai yayi kamar bai san tana yi ba, wataran kuma ya birkice mata yayi ta zazzaga mata masifa.

Ga wani abin takaici tare suke tafiya office. Saboda filin gidansu bazai dauki mota uku ba, sai Maryam ta bar tata a gidansu. Idan tana son zuwa unguwa sai driver yazo ya kaita.

Saudat duk hassadar ta da kyashinta baya damun Maryam don tana da kokari wajen ibada, kuma ita da zuciya daya take zaune da ita.

A bangaren Anisa kuwa, rayuwar ta sai hamdala. Ta kammala Masters dinta, result dinta yayi kyau, take suka dauke ta lecturing. Saudat duk hassadar ta da kyashinta baya damun Maryam don tana da kokari wajen ibada, kuma ita da zuciya daya take zaune da ita.

Sannan ta bude makarantar koyon girki da take gudanarwa ranar asabar da lahadi da yamma, sosai ta samu karbuwa a cikin garin sokoto.

Ga kasuwancin kayan sawa da sukeyi ita da Fauzan, atampa, laces, shadda, jaka da takalma na maza da mata, suke kaiwa 'yan office dinsu.

Saudat kam nadama ce ta cika ta, don yanzu ta yarda Anisa tayi mata nisa. Tana ta so tazo ta bawa Anisa hakurin rashin mutuncin da tayi mata amman ta kasa. Yau dai ta daure ta shigo tayi sallama. Anisa da ta baza atampopi tana ware su,ta amsa mata ba tare da ta dago ba don ta gane muryar ta.

Jiki a sanyaye ta zauna tace "maman Suhaima kwana biyu ya kike ya aiki"

Anisa tace "lafiya lau Alhamdulillah "

Saudat tace "Nabil ne yake ta zancen Suhaima, nace bari na kawo shi suyi wasa"

Anisa tace "Allah Sarki, Suhaima ko ta tafi makarantar islamiyya "

Saudat tace "ayya ita har an sa ta ashe, shima ina ta bin Babanshi yace wai ai bai iya magana ba sosai sai wata shekarar"

Anisa tace "Allah Sarki, ai shekarar kamar yau ne" ta cigaba da aikin ta.

Da Saudat ta ga dai bata samu fuska ba tace "to bari muje sai anjima"

Tace "ku gaida gida.

😍😍😍😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now