Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal04
Anisa tana can ta shiga cikin yan uwa, farin ciki ne ya cika ta, sam bata bi ta kan wayarta ba tana cikin jaka. Sai bayan isha ne tazo zata kwanta bacci ta dakko wayar. Aiko ganin missed call din Fauzan guda biyar yasa hankalinta ya tashi don baya missed call sama da biyu, tayi trying amman taji wayar a kashe saboda haka tace bari da safe sai ta kara kira.Tana idar da sallar asubah ta kara kiranshi don itama dai ba wani bacci ta samu mai dadi ba, ta kira shi sau uku bai dauka ba tace ta san ai ze biyo ta. Shiru har wajen karfe sha biyu bai kira ta, nan fa ta san matsala ta afku.Anisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta dawo gidanta. To in ta dawo dinma ai bata san me zata tarar ba don Fauzan akwai iya fushi, gashi bata taba yi masa irin wannan laifin ba a zaman shekara biyu da sukayi.
Nan wata shawara ta fado mata, ta dauki wayarta ta kira Fatima yayar Fauzan. Sun gaisa lafiya, sai take bata labarin yanda Fauzan yake hana ta zuwa gida ta Kwana tun farkon aurensu, "ko bikin Nawal da za ayi cewa yayi in bari ai tunda a Kano za ayi daurin aure da walima ba se naje Zaria ba, da aka zo zancen Kai amarya ma nan yace ai laulayi nake kar a wujijjiga ni a tafiya inje inyi masa asara. Haka ina ji ina gani na kara langwabewa da yan tafiya suka biyo min, aka tafi kaduna aka barni. Da jikina Yayi kwari Umma da kanta ta bugo mana waya akan ya kamata muje muga dakin Yar Uwata amman kirikiri Fauzan ya hana ni tafiya".
"Allah Ya sa na sauka lafiya, Fauzan ya rikice yace bazan tafi wanka gida ba, haka Umma tazo tayi min Kwana goma, da nayi arba'in kuma yace ai ance Nawal na da ciki saboda haka in bari in ta sauka sai inje, to yanzu Allah Ya sauke ta lafiya kuma wai yace bazan Kwana ba, nikuma kawai na hada kayana na taho"
Yaya Fatima tayi shiru tana jinjina bayanin Anisa can ta numfasa tace" gaskiya kam Fauzan bai kyauta ba, amman kuma kema da baki tafi ba kin dan kara bashi lokaci, yanzu tun bayan tafiyar ki kunyi waya? Anisa tace A'a, Yaya Fatima tace "to ki barni dashi zan masa magana, ki shirya washe garin suna zai zo ya dauke ki" farin ciki ya cika Anisa tayi godiya sukayi sallama.Anisa ta dan samu nutsuwa, ta fara walwala. Anyi suna lafiya ranar jumu'a, an sawa Yar gidan Nawal sunan mahaifiyar mijin ta Kabir, wato Zainab amman za a kirata da Nihal. Washegari da sassafe kamar daga sama taji muryar sa, jiki a sanyaye ta karasa yiwa Sahima wanka, sai ga Nuruddeen nan ya na fadin "yaya Abba yace ki sauri ki shirya ga yaya Fauzan nan yazo daukanki" Umma dai kallon yarta kawai takeyi tana mamakin wannan kalata ta mijinnata.
Sha daya daidai suka dau hanyar kano, suna tafe ba wanda yace da dan uwansa komai har suka iso Kano.Kamar jira yake su shiga gida nan ya fara zazzaga kwandon masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba " wato yarinyar nan kin raina ni, saboda Kinga ina miki lakolako, to daga yau kin dena fita unguwa, ko makota na haramta miki shiga, Idan sabga ce ta dangina ta taso ai su sun san halina zan ce musu na hana ki, inyaso a danginki idan da wanda ya isa ya tinkare n" bai karasa ba ta tari numfashinsa "idan Kai kana jin kanka ka raina dangin ka, to ni nawa dangin ba sa'anninka bane babu wanda zai tsaya yana sa'insa da kai baka da wannan matsayin"Me yasa kika fadawa yaya Fatima" ya fada da rarraunar murya,
"kinsan na fada miki bana son muna fitar da matsalar aurenmu (no third party) " tace "shi yasa kake cusguna min saboda ina hakuri ina shanye duk wata mugunta da kai min" shiru Yayi yana kallonta, sahima ta dauka zata canja mata diaper ta kuma bata abincinta.
😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020