Soyayya Don Allah
(Love at first sight)
By Ummnihal06
Hajiya Aisha mahaifiyarsu Anisa mace ce mai tsananin tsafta, da son kwalliya. Allah ya buda mata harkar kasuwancin sutura irin su lesi, atampa da shadda Wanda kuma a gidanta take siyarwa, garage din gidan ta mayar shagonta. Tana da tsanani da zafi wajen tarbiyya, musamman Anisa da take babba ta sha wahala a gun umman, kafin ta gano cewa yawan duka da hantara bashi ke kawo nutsuwa ba a tattare da yara. Addu'a ita ce babbar makami wajen kula da tarbiyyar yara.Anisa nada shekara bakwai umma ta haifi Mufaddal, a lokacin Nawal nada shekara uku.Anisa nada kokari wajen raino shi yasa koda Mufaddal ya fara kwari Umma ta sakar mata kula dashi, tsakaninta dashi kawai tayi masa wanka sai in ya bukaci shayarwa ta bashi. Amman Anisa ita ce tsarkin kashinshi, ta goya shi yayi bacci. Haka kuma ta koya mata Shara, da wanki da wanke wanke. A irin wannan yanayin rayuwar Anisa ta kasance.Tun tana primary school Anisa ta san in ta tashi da asuba ta dora ruwan wanka, ta hada tayi wa Mufaddal da Nawal lokacin Umma tana goyon walida, kafin su gama shiryawa umma ta hada musu breakfast da lunch box. Da yake a staff school suke, wataran Abba ne yake kaisu wataran kuma su tafi da kansu. Don a yanzu zancen da akeyi, Anisa ita ke yin miya every weekend, idan ta dawo daga makarantar boko kuma tayi shara, in aka dawo daga islamiyya wataran tuwo yana jiranta zata dafa. Wanki da wanke wanke ne aka samo almajiri yake yi.
Haka rayuwar Anisa ta kasance, indai tana son zaman lafiya da Umma to ta kula mata da gida da yaranta ko tasha hantara da fada, a bangaren Abba kuma tayi kokari a makaranta. A haka Anisa ta rasa kanta, don bata san me ita take so ba a kankin kanta, bata san komai ba sai kokarin farantawa Umma da Abba. Don karatu kam Anisa tana yin shi sosai, yanzu tana jss 3 ne a demonstration secondary school dake cikin kongo, tunda Anisa ta fara secondary school 'A' take samu a kowane subject, musabakar karatun Alqur'ani kuwa taje har matakin jiha inda ta zo ta biyu a izu ashirin.
A hankali Anisa tana kara girma Umma tana sakar mata ragamar aikin gida, don har sai da kawayen umma sukayi mata magana tace ai ita mace ce in bata koya ba yanzu to sai yaushe zata koya. Abinda Umma bata gane ba, bai kamata ace ta sakar mata komai ba, kamata yayi su dinga yi tare.Ranar juma'a Fauzan yake zuwa ya gaishe da Umma don boys quarters din gidan ba a kusa yake ba, Abba kam suna haduwa a makaranta dashi kusan kullum.
Watarana ya hadu da Anisa, wataran kuma baya ganinta. Inma dai sun hadun gaisuwa ce kawai ke shiga tsakaninsu. Gashi ga dukkan alamu ya fuskanci akwai damuwa a tattare da Anisa, to amman bai san yanda zai fara jan ta da hira ba. Tunda koda yaushe tana tare da kannenta tana kula da al'amuransu sai yace to bari ya fara jan yaran a jiki, a hankali har ita ma ta saki jiki dashi. Cikin ikon Allah kuwa sai ga Anisa da Fauzan sun fara sabawa.Ranar wata juma'a yazo ya same ta a farfajiyar gidansu tana zaune ta kurawa bishiya ido, yana ta magana bata ji shi sai da ya Kara daga murya ne ta firgita yace" wai ke me kike kallo ne a bishiya" tace "baka san kallon koren bishiya yana kara karfin ido ba" yayi dariya yace naji wannan theoryn amman ki daure ki fada min damuwarki, tace "na fada maka ni ba abinda yake damuna"
Fauzan yace "to ni akwai abinda yake damuna" tace "to fadi inaji"Yayi tunanin ya fada mata ko a'a, wata zuciyar tace masa ka tsaya kallon ruwa kwado yayi maka kafa, nidai na gaji da taya ka jiran lokacin da Kake tunanin shi yafi dacewa da ka fada mata, kullum kana kwana tunaninta da rokon Allah ya sa ita ma tana sonka. Shi dai ya ture wannan umarni na daya bangaren zuciyarsa, yace ai karamar yarinya ce ita kuma kar ya kawo mata cikas a Cikin karatunta, zuciya dai tace kai ka sani.Fauzan yace "baki fada min taki damuwar ba nima bazan fada miki tawa ba" Anisa tace baka da damuwa kenan tunda nace maka ni ba abinda yake damuna"
Inda itama Anisa a zuciyar ta cewa take to me zance maka yake damuna, wata zuciyar tace kice masa Yaya Fauzan kaunarka ta hana ni sukuni, daya zuciyar tace haba dai zubar da aji kenan, Anisa tace da zuciyarta mudai cigaba da addu'a Allah ya sa ba nikadai nake wannan wahalar ba, in kuma babu alkhairi a tsakaninmu to Allah ya kawo min mafita mai sauki.
😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020