Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal11
A shekara dayan da Anisa tayi a gidan Fauzan, ta fuskanci inda rayuwa ta dosa. Ashe da can bata san me cece rayuwa ba. Kullum tana cikin cewa "Allah Ya sakawa iyayenmu da alkhairi, lallai sunyi kokari. Ashe duk kukan dadi muke yi, bamu san gwagwarmayar da Abba yake yi ba ya biya mana kudin makaranta, yayi mana sutura, ya siyo kayan abinci, ga kuma kudin asibiti da na magani.
"Umma ashe ba karamin kokari take yi ba, aikin gida baya taba karewa, shara, wanki, wanke wanke, wanke toilets, girki, rainon yara. Da gaske dai ashe Umma gata tayi mata da ta koya mata aiyukan gida don da Anisa baza ta san daga ina zata fara ba. Ga Fauzan da iyayi, yafi son ya ga gida tsab komai an aje shi a muhallinsa, wani lokaci idan ya dawo gida kafin ya gama aje babur (bike) dinsa a tsakar gida ya fara mita, "wannan tsinsiyar me takeyi a nan ko zo ki dauke wannan kujerar daga nan kikai ta kitchen"Wataran sai da yamma likis zai shigo da ɗanyen nama ko kifi, ga shi ba sosai suke samun wutar nepa ba, haka dole zata tashi tayi aikin namannan. Da take gida cewa take yi ai Umma ita ta sabawa Abba da inya kawo aiki da yamma take yi, Anisa tace ai ita daman baza ta dauka ba,ashe abin ba daga nan bane. Mutum yayi hanƙoro ya samo, ai dole ki dafa masa tunda kina son farin cikin sa.
Ga Fauzan da tsananin kishi, sai ta shirya zata tafi makaranta, ta sa hijab da yayi matching da kayanta sai yace wai tayi kyau da yawa gaskiya baza ta makarantar nan ba yau. Sai da tayi da gaske tukunna don in ta biye mishi dena zuwa makarantar za ayi. Daga karshe dai yace sai dai ta dinka uniform ta dinga zuwa dashi.Anisa tana son zaman lafiya kuma tana tsoron abin da zai kawo mata cikas a karatunta saboda haka ba musu ta yarda, ya dinka mata yadi mai yashi kala uku (blue, green da brown) take zuwa makarantar dasu.
Sai ga Anisa da 'yan ajinsu suke gani 'yar gayu mai fashionable and descent dressing aure ya mai da ita yar ƙauye, ga nikab da safar hannu data kafa.Hatta turare Fauzan ya hana ta fesawa, gashi ana zafi, ga wani tsami da jikinta yakanyi da ita ma ta rasa dalili, ya hada ta da madarar turare da ya siyo a kasuwar kurmi wai in zata makaranta shi zata shafa a jikinta kuma kawai banda kaya.
Da yake a farkon aurensu bai fara zuwa aiki ba sai da sukai wata uku sannan ya samu aikin bankin da yakeyi.
Shima kansa bai san haka dawainiyar kula da iyali take ba, shi yasa abin yazo masa a baibai, dan kudin da ya samu a Islamic chemist ɗin kanin babansa da yake jira da kuma ɗan wanda Babansa yakan ba shi in sun hadu, su yake jalautawa.Shi yake kaita makaranta sai ya bata ₦200 yace ai zasu ishe ta taci abinci, ta kuma yi kudin motar dawowa gida. Da taga kudin basa isar ta kuma in tace ya Kara mata fada suke yi sai take dafa abincinta daga gida.
Taci gaba da hakuri da fatan Allah ya bashi aikin yi ko zaman su zai yi dadi don ta lura, matsalar rashin aiki ce ta sa Fauzan baya kaunar maganar kudi.
Fauzan ya samu aiki amman bata sauya zani ba, da tayi masa magana sai yace mata "kinga wannan gidan haya aka kama mana, dole in dinga yin saving ba sai shekara ta zagayo ba in rasa yanda zanyi, kuma ya kamata inyi fafutukar gina nawa nima"Lantana ce tace mata akwai wani program da akeyi a radio rahama FM, Mallama Tasalla tana fadan magunguna game da matsalolin mata.
**Kwatsam kuwa taji matar tana cewa, ai duk ladabi da biyayyar da mace take yi wa namiji, da kwalliya, da tsabta, in dai da akwai sanyi (sabara) a jikinta, to lallai zata rasa gane kan mijinta. Matar ta lissafo abubuwan da suke kawo sabara tace, tsarki da ruwan sanyi, yawo babu takalmi, zama akan tantagaryar siminti ko tiles, rashin gyaran jiki bayan mace tayi bari ko ta haihu.Nan take Anisa taji tamkar da ita ake, don wani lokaci Anisa har da pure water mai sanyi tana tsarki a makaranta idan mutane suka cika a bakin famfo a masallaci.****
Kuma tabbas ita lokacin da tayi barin nan a baya babu wani wankan jego da tayi, kunya ce ta hana ta fadawa Umma, shi yasa abubuwan nata duk suka tabarbare.
***Nan ta samo magungunan sanyi da matar ta lissafa, ganyen magarya, ganyen sabara da ganyen lalle ta jefa ɓari ɗaya na tafarnuwa, ta tafasa su, ta zuba ruwan a babbar roba ta shiga.Cikin ikon Allah sai ga wani farin zare ya fito daga jikinta, can sai ga wani dunkulen nama nan, Anisa ta cika da al'ajabi dai ranar. Tayi kawana uku tana yin haka, sai ta koma yin sau biyu a sati. Sosai Anisa taji dadin jikinta, taji sauyi sosai a jikinta****.
Bayan sati uku sai ga period, tana gamawa kuwa ta samu ciki. Farin ciki mara misaltuwa a gurin Fauzan, ya fara tarairayarta kamar gaske, sai kuma yazo ya dena.
Idan tace masa tana son abu sai yace mata bashi da kudi, ta daure taci abin da take dashi a cikin gida.
Sai daga baya Anisa ta gano, ashe wani azzalumin aboki Fauzan yayi, shi ne yake ce masa ai mata duk yanda ka bi dasu haka zasu zo maka, ba ayi musu lakolako. Kuma kar ka yarda mace ta san samun ka, zata sa maka ido ne.Hankalinta ya tashi da taji suna wannan wayar. Da ta Kira Ummanta take fada mata ita fa ta kasa gane kan Fauzan, duk wani abu da ya kamata tana yi masa, amman yau yayi kyau gobe ya birtse.
Umma tace mata "Anisa rayuwar aure tana dauke da jarabawa kala kala, kuma in dai zaki dinga duba alkhairan da kika yiwa mijinki kina comparing dinsu da rashin kyautawar dashi kuma yake miki, to in gaya miki gaskiya, zaki fadi jarabawa.
duk wani abu da zaki yiwa mijinki kiyi masa don samun yardar Allah, duk wata matsala da ta bijiro miki, ki nema maganinta a wajen Allah. Matukar kika sallamawa Allah lamarinki, kin gama tsira.
Ki tashi da daddare kiyi kiyamullali koda raka'a biyu ce, ki fada wa Allah damuwarki, ki dinga yin azumin Nafila na litinin da alhamis, ki rike addu'o'in safiya da maraice kinayi kullum.ki kasance mai yin salloli biyar na farilla akan lokaci, tsakaninki da mijinki ki rike gaskiya, kar ki yarda ha'inci ya shiga tsakaninku don duk randa rashin yarda ya shiga tsakaninki da mijinki to tabbas an samu matsala, sai a karshe kuma ki rike hakuri ya zame miki makami"Anisa taja dogon numfashi tace "Umma nagode Allah Ya saka da alkhairi, Don Allah Umma ki yafe min duk rashin jin maganar da nayi miki, wallahi yanzu na gane ba karamin kokari kikayi damu ba"
Umma tayi dariya tace "da saura ma ai, sai kin dandani laulayi, goyon ciki, nakuda da kuma raino zaki gane "Anisa tace "ai ina kan dandana laulayin ma" tana gama fada ne ta rufe fuska
Umma tace "Alhamdulillah, Anisa shine baki fada min ba ina nan ina ta lissafa, na damu shiru, kina shirin yin shekara babu wani labari, to Allah Ya sauke ki lafiya"
Tun daga ranar kullum sai Umma ta Kira ta taji ya jikinta, tana cewa ta kula da kanta.
😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020