9

29 4 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal


09
Alhaji Abubakar da Dr Malami sunyi waya, sun nunawa juna farin ciki game da alakar da 'ya'yansu suka kulla, wadda zata kara dankon tsohon zumuncin dake tsakaninsu. Abba yace da Baba idan sun tashi su sami Yayan shi Alhaji Isa dake zaune a unguwar gwammaja shine waliyyin Anisa.

Baba yasa Fauzan a gaba yace "nayi niyyar in biya maka kudi ka koma masters, amman kai kuma yanzu ka dakko zancen aure, sai ka zaba daya don ba daidai bane inyi maka aure, baka da aikinyi kuma ga karatu kanayi" Fauzan yace zai yi shawara.Fauzan ya kira Anisa a waya yake fada mata yanda sukayi da Baba, Anisa tace"ai gara kayi masters din in Allah ya yarda kana gamawa za ka samu aiki sai muyi aure, nima kaga na samu dama da zan cigaba da karatu, maimakon daga gama secondary ayi min aure"

Fauzan ya dawo A. B. U Anisa kuma ta tafi Bayero University Kano (B.U.K). Medicine (MBBS) tayi applying, kuma duk ta samu abinda ake bukata amman saboda tangarda da tsarin ilimi yake dashi, komai an maida shi harkar kudi, sai suka bata biochemistry amman wai zata iya change of course in ta biya #10,000. Ran Abba yayi matukar baci don har yace ta fasa zuwa sai taje SBRS tayi IJMB in yaso tayi applying a ABU.Da ta fadawa Fauzan halin da ake ciki, yace mata tayi istikhara, abinda taji yafi kwanta mata a rai to sai ta zabe shi.

Anisa ta duba taga yanda admission yake wuyar samu, gashi ita ta samu zata yi sake, tace da Abba zata je BUK sai tayi change of course din. Da kyar ta shawo kan Abba ya yarda. Koda ta taho Kano har an fara lectures, mutumin da zai bata form din change of course kuma suna ta sabani bata same shi ba. Kawai da ta gaji taje ta karba admission letter ta biochemistry tayi Ran Abba ya baci sosai wanda shine karo na farko da ta taba batawa Abbanta rai. Tayi ta bashi hakuri dai har ya sakko ya dena fushi da ita.

Taci gaba da karatun ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da yake ma a gidan Hajiya Najwa kanwar Umma dake rijiyar zaki take zaune.

Duk bayan sati biyu Fauzan yake zuwa kano don yaga Anisa su sha hira. A haka har aka shekara daya da karatunta.Wata rana ne Fauzan yazo gidan hajiya Najwa gun Anisa, sai ya tarar da wani mutum a kofar gidan, Fauzan zai shiga gidanne da yake ya riga ya zama na gida sai mutuminnan yace masa "yawwa don Allah mallam kace ana sallama da Anisa" Fauzan ya bata rai yace "ita tace maka kazo gurinta? Mutumin yace "A'a, tun a makaranta nake ta binta taki ta kula ni, shine na biyo ta gidansu ko bata tsayawa da maza ne a waje" Fauzan yace" to mallam matar aure ce, sai kayi hakuri ka kara gaba" yana gama fadin haka ya shige ciki ya bar bawan Allah da kama baki.

Ranar nan dai ba ayi zance mai dadi ba, Fauzan yana ta faman mita "sai da nace miki ki dinga sa hijab da nikab amman kika ki, kina cin kwalliya kina zuwa school taya za ai a san da mijinki"
Anisa tace "da mijina kuma yaushe aka daura min aure ban sani ba?Fauzan yace  "indai daurin aure ne an kusa inshaa Allah" ya dauki wayarsa kirar sony ericson da mukullin babur (bike) dinsa ya fice. Anisa dai tace "yau Allah nagode maKa da wannan mutumi da Ka hada ni dashi"

Fauzan yana zuwa gida yaje ya samu Babansa akan lallai sai anje an sa masa ranar aure. Baba ya san rigimar Fauzan yace masa to gobe in Allah ya kaimu za aje. Washe gari kuwa Fauzan yaje ya sa Mama (step mum dinsu) a gaba sai taje tayiwa Baba tuni akan maganar su ta jiya. Ba shiri dai Baba ya Kira kaninsa Barrister Ibrahim suka tafi gidan Alhaji Isah. An sa shekara daya ga me yawan rai, ba yarda su baba basuyi da Baba Isah ba akan ya karba kudin an gani ana so amman yace duk Al'ada ce bazai karba ba, sadaki kawai za a karba shima kuma sai a wurin daurin aure.Don karbar sadaki a lokacin sa rana yana kawo matsala, shedan yana samun dama wajen nunawa masoyan biyu tamkar ai an daura aurensu ne, wai tunda ga waliyyai na bangare biyu sun hadu sannan kuma ga sadaki. Alhali akwai sauran abinda ake bukata, Kamar siga ta 'an baku, mun karba', da kuma tara jama'a a matsayin shaidu.

Fauzan fa shekara daya tayi masa nisa, nan ya koma wa Anisa da hijab Kala uku da nikab guda biyu, yace sai tayi masa alkawari su zata dinga sawa kullum in zata jami'a. Tace "nayi maka alkawarin sa hijab amman nikab kam bazan iya ba gaskiya" har zai fara yi mata fadannasa can dai sai ya koma lallama yace "kinga fuskarki ta cika kyau da yawa zata iya kawo accident shi yasa ya dace ki dinga killace ta" ya bata dariya tace "to naji zan gwada, in na sashi ne dauke min numfashi yake" yace "ai don baki saba bane"

Nan suka fara lissafin kwanakin da suka rage su zama miji da mata!!!

😍😍😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now