Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal19
Jikin Saudat yayi sanyi saboda kallon da taga Anisa tana yi mata. A zuciyar ta tace to ai gaskiya na fada. Basu Kara tanka juna ba sai da suka iso kan kwanar gidansu, Anisa tace "a nan zan sauka saboda zan dakko Suhaima a gidan Inna"
Saudat tana parking tace" kinga ko ina taso inyi miki zancen sabuwar me aiki na 'yar Togo, in kina so a samo miki, don akwai su da aiki, kinga ko wanka bana yiwa Nabil nake tafiya na bar mata shi, kafin na dawo kuwa ta gyara gida, tayi abinci, ta gyara Nabil ta goya shi"
Anisa tace "in na tashi bukata zan miki magana"
Motar Anisa ta iso Amma da daddare ne Don haka SAUDE Bataan Ankawo ba seda safe Amma da ta gani batai Mayana ba saboda bakin ciki
Fauzan ya duba motar Anisa ya ga ba wata matsala da ta same ta, har yace tazo tayi driving su je shunda store suyi shopping su dawo. Lafiya lau kuma suka je suka dawo. Yayi mata addu'o'in tsari yace itama ta dinga shiga da bismillah.Lafiya lau ta cigaba da zuwa makaranta da motar ta.
Saudat kuma taki yarda su kara haduwa da Anisa, wani lokaci sai ta yi niyyar fitowa, idan taji alamun bude gate din Anisa sai ta jira har sai ta tabbatar ta tafi sannan sai ita ma ta fito. Ko a makaranta rannan Anisa tana ganinta ta canja hanya don karsu hadu. A haka har suka yi wata shida. Abin yayi wa Anisa matukar dadi, Allah Ya raba ta da alakakai.Kwatsam yau sai ga ta ta shigo gidan Anisa, jiki a sanyaye ta fashewa Anisa da kuka. Anisa tazo ta dafa ta tace "Maman Nabil lafiya"
Da kyar ta yi shiru ta kada baki tace "wai ni Baban Nabil zai ciwa amana, wai aure zai yi, har saura sati biyu ma"Dariya ce ta so kwace wa Anisa, a zuciyar ta tace "yar gaban goshi kenan.
A fili tace mata "to Maman Nabil kiyi hakuri, ai Karin aure ba cin amana bane, kiyi addu'a Allah Ya sa wadda zai auro ta gari ce"
Saudat tayi mata wani kallo tace "tunda ba ke za ayi wa ba ai zaki fada haka, to in gaya miki sai inda karfina ya kare, ni nafi karfin ayi min kishiya"Wani Mallamin ta ne ya bata wani kullin garin magani yace indai tayi wanka dashi babu zancen yi mata kishiya.
Abin mamaki kuwa baban Nabil yace mata "gimbiya hankalin ki ya kwanta, mun samu matsala da dangin amarya an fasa aure"
Farin ciki ya cika ta, nan ta fara kokarin canja halayenta, tana ta kokarin faranta masa.
Taje ta samu Anisa tana fada mata tace "ai na fada miki na gama dashi" Anisa ta jinjina kai tace "eh gaskiya na yarda ke din babba ce a wannan harkar, Allah Ya baki ikon ganewa"A fusace Saudat tace "kin fini bukatar wannan addu'ar" ta tashi fuu ta fita, Anisa ta bita da kallo.A bangaren Tijjani kuwa ganin Saudat taki ta kwantar da hankalinta, yana ta tunanin yanda zai bullowa lamarin, sai yaji an sa ranar bikin kanwarta nan da wata biyu. Shine ya samu dangin amaryarsa ya nema alfarma akan su kara masa lokaci, haka aka sa date rana daya da na kanwarta.
Sauran sati daya bikin kanwar Saudat tace masa tana so ta koma gida saboda hidimar biki wai baza ta iya jeka ka dawo ba wahala zata sha. Sosai ya bata rai yace bai yarda ba, sukai ta sa'insa sai da yaga ta bata rai sosai sannan ya ce "to shikenan, amman ana gama biki zaki dawo"
Nanma ta bata rai tace "sai ta huce gajiya tukunna"
Da kanshi ya taya ta hada kaya don ya tabbatar batayi mantuwa ba, kuma yace ta bashi key dinta na gida don ya san halinta sai ta iya zuwa ta yar.
Tayi murmushi tace "kuma fa haka ne, ka sanni idan biki yayi biki"
Washegari ya sa aka zo aka kwashe kujerunta da kayan gadonta ya kaisu gurin carpenter yace kujerun a canja musu yadin, gadon kuma ayi mata sabon painti.
Bata gayyaci Anisa ba kuma bata yi mata sallama ba saboda bata son taje taga gidansu bayan ta gama yi mata karyar ita 'yar masu kudi ce.Shi yasa sam Anisa bata san wainar da ake soyawa ba.
Sai ranar daurin aure Fauzan yake fada mata zai je daurin auren Tijjani. Jiki a sanyaye tace"haba abin da mamaki, jiya naji alamu ana ta shiga da kaya gidan, sai nayi tunanin ko gyara ake mata"
Fauzan yace "to sai ki kiyaye bakin ki don ga dukkan alamu bata sani ba"
Anisa tace "a ina zan ganta tunda ta tafi ba sallama ba waya"
Sukai sallama ya tafi daurin aure, ita kuma yinin ranar dai haka ta dinga jinta ba dadi a zuciyar ta tace "daman haka abin yake, ba ni za ayi wa ba amman naji zafi, ina ga in nice, tayi maza ta kawar da zancen, sai can kuma tace Allah ya basu zaman lafiya, muma in tazo kanmu Allah Ya bamu ikon jurewa"
An daura auren Tijjani da amaryar sa Maryam, wadda abokiyar aikin sa ce. Ita ke yo masa girki ta taho masa dashi office, shi yasa baya damuwa da komawa gida da wuri. A hankali soyayya ta shiga tsakaninsu, gudun kar su fada tarkon shedan ya sa suka yanke hukuncin yin aure.Ta so ya kama mata wani gidan amman yace ai gidansa akwai space, gara ya hada su guri daya. Ba musu tace ta yarda. Yace sai ta dauki daki biyu, uwargida kuma a bar mata parlor da daki daya.
Koda yan kawo kaya suka ga parlor empty, sai suka jera mata kujerun a nan, ya so ya sa a kwashe, amman da yaga parlon yayi kyau sai kawai ya kyale.
Saudat tana can ana ta shan biki, bata san wainar da ake toyawa ba. 'yan uwa da abokai saboda suna jin tsoron masifar ta babu Wanda ya iya tinkarar ta da zancen auren mijinta.
Yan uwan Tijjani mata sun zo sunyi wa iyayen Saudat Allah Ya sanya Alkhairi, nan taji suma iyayenta suna yi musu Allah Ya bada Zaman lafiya Allah Ya bashi ikon yin adalci.
Sai tayi tunanin ko zancen kayan lefen kanwar Tijjani da aka kawo sukeyi don me mata zata aura.
Satinta daya bayan biki sannan ta shirya da nufin komawa gidanta. Iyayenta suka zaunar da ita suna yi mata fada akan tayi hakuri da abinda zata je ta tarar, kar tace zata je ta tayar masa da hankali, shi aure nufi ne na Ubangiji, kuma ta godewa Allah ma mijinta yana sonta don baiyi nufin tozarta ta ba, ga kuma kayan arziki da yayi mata duk don a zauna lafiya. Baba yace "saboda haka kar inji kar in gani ki zauna lafiya da mijinki da amaryarsa"
Wani abu ne taji ya tsikare ta tun daga Kanta har cikin kafar ta, take jikinta ya fara rawa, ta rusa wani irin ihu sannan ta fadi sumammiya.........
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020