14

36 7 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal

14
Lokuta da dama Anisa takan ji haushi yanda Fauzan yake nuna mata cewa albarkacin Suhaima take ci. Amman daga baya ta gane sharrin shedan ne kawai, in ma albarkacin 'yar ta taci ai ita ta haife ta, ta godewa Allah ma da ya kasance mai tsananin kaunar 'yarsu. Wasu mazan ba haihuwar kawai sukeyi ba, amman basu damu da rayuwar 'ya'yan ba.

Rayuwa taci gaba, da dadi ba dadi, Anisa bata taba yin korafi, koda yaushe tana cikin walwala da farin ciki. Har sai da Fauzan wata rana suna hira yace" nikam ina mamakin hakurin ki Anisa, kina dadewa kafin kiyi fushi, kuma ko irin kyale kyalen nan naku na mata ke be dame ki ba, duk abinda aka baki sai ki karba hannu biyu kina godiya"
Anisa tace "to ai kana iya kokarinka yanda ya kamata, kuma ina rokon Allah kullum da Ya tsare ni daga fadawa tarkon shedan da yake kawata mana duniya muke shagalta wajen nemanta, muna mantawa da neman lahira. Hakuri kuma shima kullum ina rokon Allah Ya sa na kasance mai hakuri (sabrun jamil) me kyau ba Wanda zan dinga cutuwa ba.Kasancewar mijinta ma'aikaci dan salary bai sa sun ta'allaka akan jiran karshen wata in anyi biya sannan suji dadi ba.

Tsari me kyau sukai wa rayuwar su, abubuwan da suka zama wajibi na amfanin gida kamar kayan shayi, Man kuli da Man Ja, omo, sabulu, pampers, Maggi da gishiri su yake siyowa, sannan ya ware kudin cefane ya bata, ita kuma idan kudin basu isa ba kafin karshen wata sai ta cika da kudin sana'arta, su rufawa juna asiri.

~~~~~~~~~*~~~~~~~~~~~
Baba ne ya kira Fauzan yace yazo ya kai shi gidan gwamnati zasuyi meeting da gwamna. Bayan sun fito ne Fauzan ya ganshi tare da wani abokin shi suna gaisawa, nan yaje ya durkusa har kasa ya gaishe shi, abokin Baba yace "ikon Allah Fauzan ne ya girma haka, lallai an dade ba a hadu" Baba yace "Fauzan da yayi aure harda 'ya ma"
"Maa sha Allah, a ina yake aiki" inji aboki
"a banki, Fauzan wani banki ne ma"
Fauzan yace "access bank"
Aboki yace " haba Alhaji, me ake ci a banki banda wahala, yanzu ko ma'aikatar ka ba sai ka kaishi ba"
Baba yace "ma'aikata ta ko ta gwamnati, ita rayuwa 'yar abi sannu ce, a hankali har Allah Ya kaishi babban matsayi"
Aboki yace "aiko jiya da naje Abuja na hadu da Rep dinmu na fagge yace an bashi offer na Federal inland revenue service FIRS in ina da graduate in aika masa CV ya gani, Fauzan gobe ka kawo min takardunka"
Cikin murna yace "inshaa Allah zan zo goben kamar Karfe nawa" Aboki Yace "wajen bayan la'asar"
Baba yace "ai Rep dinnan yana kokari ina ma ace haka sauran suke kokarin taimakawa yaranmu da aiyukan yi ba suje suna siyar da offers din da aka basu ba, mungode Allah Ya saka da alkhairi"
Aboki yace "Haba Alhaji ai yiwa kai ne"Farin cikin da Anisa ta gani a tattare da Fauzan yasa ita ma ta biye mishi tana ta aukin murmushi tace "su Habibi ta samu ne" Yace "Habibtie kedai ki taya ni da addu'a, wani alheri ne ya kunno kai, amman sai ya tabbata zaki ji"
Tace "to Allah Ya tabbatar mana da wannan alkhairin"
Yace "aameen"
A zancen Fauzan wai mata barin baki ne dasu, basa iya rike sirri, shi yasa bai fada mata ba.

Bayan sati biyu kuwa sai ga Fauzan nan, yana shigowa gida ya doka wani tsalle, ya dire da rawa yana juyi, Anisa dai tana ta faman kyalkyala dariya. Can ya ciro takardar Offer ya bata, aiko itama ta tayashi rawa sun manta da Suhaima da take gefe tana ta tsalle tana tafi tana dariya. Ita ma suka ruko hannunta sukai tayi.

Bayan sun gama ne Fauzan yace "amman fa akwai wani hanzari ba gudu ba"
Anisa tace"me ya faru"
Fauzan yace "sokoto akayi posting dina"
Anisa tace " To ai ba matsala, daman ni na gaji da kanonnan, kuma ai ni da kakanni na a sokoto"
Fauzan yace "to ai ba dake zan tafi ba"
Anisa tace "haba wa ai kafa ta kafar ka, salon ka samu damar cewa zakai aure a can"
Fauzan yace" su gimbiya kishin ya motsa, to da wasa nake, nima bana son inyi nisa da Mama na"
Anisa tace "ka dai ji dashi

*****"SOKOTO 2017*****

Yau wata daya kenan da Fauzan yayi reporting a office dinsu dake unguwar zungeru a cikin garin sokoto. Sosai yake jin dadin aikin sa, don baiyi tsammanin zai sake haka ba saboda yayi nesa da 'yan uwansa, koda yake me zai dame shi tunda yana tare da iyalinsa.

A satin da yaje zai fara aiki ne wani abokin aikin sa Tijjani yayi masa zancen gidan da yake ciki a unguwar runjin sambo, yace masa part biyu ne babu kowa a daya part din.

Da farko Fauzan yaso ya doje saboda shi baya son zama gida daya da wasu a ganinshi akwai takura, amman sai yace to zaije ya ga tsarin gidan.

Da yake yaga zai iya yin demarcation yanda kowa zai yi harkarsa ba tare da ya takura wani ba, take yace yana son gidan. Dadin dadawa kuma yaga unguwar ba laifi tana da kyau ga wutar nepa ga kuma ruwan famfo. Da Dan nisa zuwa office dinsu, amman sokoto ba kamar Kano ba ce sai mutum ya iya zagaye garin kaf ba tare da ya samu hold up ba ko daya.

Sannan kuma akwai wani surprise da yake son zai yiwa Anisa.........
😍😍😍😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now