Soyayya Don Allah
(Love at first sight)
By Ummnihal07
Anisa da Rashida sun taso daga school, suna ta murna yau sun rubuta last paper a junior class, zasu zama seniors. Sunzo daidai wani gida ne da yake cike da shuke shuke kala kala ko cikin gidan ba a gani. Rashida tace "ance fa matar gidannan wai aljana ce, wai harda macizai da zakuna take kiwo a cikin gidan" Anisa tace "ba fa aljana bace kawai dai saboda baturiya ce shiyasa ake ce mata aljanar kongo, ko zamu gwada shiga muga in dagaske akwai su kura da kunamu a gidan" Rashida tace "shiga ke kadai ance karene yake mata gadi ko bishiya aka taba yanzu zai biyo mutum, kuma fa babu irin bishiyar da babu a cikin gidannan"Rashida ta tabo Anisa "kinga mutuminnan da ya kura miki ido ranar nan a wajen islamiyya, tana dagowa kuwa suka hada ido ya sha farar shadda da akai mata aiki da coffee din zare, hularsa da takalminsa ma coffee colour ne.Ya karaso inda suke da fara'arsa yace "yan makaranta an taso, to ya exams din? Koda yake ai nasan kannen nawa gurus ne"
Anisa tace "Yaya Fauzan exams lafiya lau alhamdulillah" ita dai Rashida sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, sai da Anisa ta taba ta tana fadin "Yaya Fauzan wannan ita ce kawata Rashida da nake baka labari" Rashida ta gaishe shi, ya amsa yayi musu fatan samun nasara a exams, yace musu masallacin juma'a zai wuce yayi musu sallama.Rashida ta Kalli kawar ta tace "kawata ai matsalarki ta kare, daman wannan shine Yaya Fauzan din naki, ai ko daga kallon da naga yanayi miki a yanzu na san shima tun a ranar farko ya kamu da sonki, lallai wannan SOYAYYA taku hadin ALLAH ce"Anisa dai jin kawarta kawai take, tace "to me yasa har yanzu bai furta min ba tsawon shekara daya fa kenan" Rashida tace amman ai ya nuna miki alamu da dama, yana sa ki nishadi musamman idan ya ganki cikin damuwa, idan yaje Kano yana tawo miki da gifts" Anisa tace "ai bani kadai yake kawo wa ba harda su Nawal "
Rashida tace "eh amman dai ai taki special yake kawo miki" kuma kince fa har waya kukeyi a starcoms din umma in ya tafi hutu, Anisa tace "ai dai shima sai ya gaisa da kowa sannan sai yace su bani, koda yake in na karba fa muna kusan awa daya yana ja na da surutu yana bani dariya" Rashida tace "to kin gani abinda nake fada miki kenan"Umma ta kula da shakuwar da ta shiga tsakanin Anisa da Fauzan har take fadawa Abba. Abba yaji dadi, amman yace da umma tasa ido dai akan Anisa kar ta sa shashanci a gaba ta fara wasa da karatunta. Wata rana kuwa Anisa ta dakko slum book da sukayi na gama junior school ne, ta ajiye zatayi wa Najlah tsarki Umma tazo ta dauka, a bayan littafinne umma taga ansa "FAUZANISA = WIN ANISA, let's see who's gonna win, Fauzan or Anisa "
Umma tace mata Anisa meye wannan nake gani, aiko Anisa ta kwalalo ido ta rasa me zata ce, Umma tace "yaushe yace yana sonki baki zo kin fada min ba" Anisa tace "bai ce yana so na ba"Umma ta dafka salati tace to ke kika ce kina sonshi kenan" Anisa tace "haba Umma rufa min asiri" Umma tace "to wallahi kar inji kar in gani, ki Kama kanki, kuma ki kiyaye randa Abbanku zai damko ki"Da Fauzan zai tafi hutu ne Umma ta bashi sako ya kai wa hajiyar ta dake kano. Bayan sun gaisa ne hajiya take cewa "kaine Fauzan din da ka sace zuciyar Anisa, Shatu sai farin ciki takeyi 'yar ta ta samu miji na gari" hajiya ta bar Fauzan da sunkuyar da kai. Ya fito daga gidan cike da farin ciki da yiwa Allah godiya. Washe gari ne da ya kira Umma suka gaisa yace a bawa kannensa ya gaisa dasu, daya bayan daya yake binsu daga kan Najlah, Walida, Mufaddal, Nawal sai habibiyar sa Anisa.Fauzan yace" wato ke bakya ma kewa ta najiki cikin nishadi da annashuwa"
Anisa tace "ina jin dadin hutunnan ne fa, gaskiya makaranta akwai wahala"Fauzan yace"ok bakya neman yayanki ko"
Anisa tace "ai na saba da rashin yaya a kusa dani kasan duk cousins dina suna kano"
Fauzan yace "ai ni ba cousin dinki bane"
Anisa tace "kuma fa haka ne, kai a cikin yayyen nawa Kai na daban ne, you are the best and the one and only" tana gama fadin haka ta rufe fuskarta.
Fauzan kuwa farin ciki ne ya ratsa shi tun daga cikin kwakwalwarsa har cikin tafin kafarsa, yace "Oh Anisa thank you for this declaration, nagode nagode.Anisa dai tayi shiru, can tace to sai anjima, yace Allah ya kaimu "my Lass" Nan ya barta da zuwa duba dictionary.
😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020