Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal21
YEARS GONE BY.....
Anisa ta samu guri ta zauna tace "kinga Sa'ima sai kuka takeyi bari in bata ta sha. Kema da zaman kikayi da wannan katon cikin naki"Nawal tace "ni dai bari in tsaya a tsaye zasu fi hango mu, kin san Nihal da mita"
Tana rufe bakinta kuwa taji sun rungumo ta, suna fadin Mamii, sai kuma suka fashe da kuka.
Anisa ta taso tace "to kar ku yarda ita mana baku ga abinda ke gabanta bane"
Ta dube su tace "meye haka kuma, kukan fa, au kema Nawal kukan kikeyi"Nawal tace "Kalli fa yanda yarannan suka rame sukayi baki, gaskiya sai an cire su daga makarantar nan. Ni banga dalilin da su Abbanku zasu dage sai kunzo Hassan Gwarzo ba"
Anisa ta shimfida musu dadduma suka zauna tace "to ki cigaba da zuga su, shi karatu ai daman sai an sha wahala. Daga ke har su ku dena wahalar da kanku don Abban su sun gama yin amanna da tsarin makarantar nan dadin dadawa kuma ga haddar Alqur'ani da zasuyi"Sudais da Shuraim suka tabe baki suka ce "muna ta murna zamu zo gun 'yan uwanmu amman basu ma kula damu ba"
Suka kamo su suka ce "sorry brothers ya kuke"
Sudais yace "cool, muna can Abuja muna morewa"
Shuraim ya karasa masa "ku kuma kuna nan a kano kuna shan zafi" yayi musu gwaloSuhaima ta zungurewa Sudais Kai, haka itama Nihal tayi wa kaninta Shuraim suka ce "ai muma daga wannan term din bazamu dawo ba bari daddy yazo"
Nawal ta Kira Kabir a waya ta kwatanta masa inda suke, ya taho tare da leburori da yasa suka kwaso provisions dinsu da abincin da aka yo musu musamman saboda visiting din. Anyi musu snacks da soyayyiyar miya da za a bar musu.
Shima da gudu suka je suka rukunkume shi suna masa kuka, duk suka bashi tausayi ya samu guri ya zauna yace "haba yan biyu na kukan na meye"
Nihal tace "daddy ka taimakeni ka cire ni daga makarantar nan kar in mutu"
Suhaima ta kara da cewa "Allah daddy makarantar ba dadi, akwai wahala"
Daddy yace "to ai shi karatu daman wahala ce dashi, Nihalee bazaki mutu ba "
Ta kara shagwabewa tace "kawai daman ka dena sona daddy"Yayi dariya hannayensa rike da nasu yace "ku kara hakuri a hankali zaku saba, wannan ita ce soyayyar gaskiya, kuma indai kukayi kokari sosai result dinku yayi kyau nayi muku alkawari a Istanbul zakuyi hutu"
Sai kuma suka doka tsalle suna fadin "Allah daddy, da gaske. Ka san kuwa munyi kokari sosai a (C.A) test dinmu"
Yace "eh mana my beauties ko ku fa, amman da sai wani koke koke kukeyi"
Suhaima tace "Ya banga Abba na ba"
Daddy yace mata "bazai samu zuwa ba saboda suna da meeting da Shugaban kasa, amman yace zai zo next week ya duba ku.
Tace "toh shikenan ai daman na san dole ce zata hana Abba na zuwa"
Anisa ta dube su tace "to kuzo kuci abinci ko"
Nan suka shiga bawa iyayen su labarin makaranta. Sosai daddy yaji dadi musamman da yaji suna karatun Alqur'ani da asuba da kuma bayan maghriba.
Wayar Anisa ce ta fara ringing, tana dubawa taga Amarya maryam ce take kiranta. Da fara'arta ta amsa, bayan sun gaisa ne ta kwatanta mata inda suke. Basu dade da gama wayar ba kuwa sai gata nan tare da uwargida Saudat.
Daddy yace da yaran "kuzo mu koma can mu bawa su mami guri"Saudat an sha kwalliya wuyannan cike da Gwal da zobe da awarwaro. Suna cikin gaisawa aka kirata a waya, bayan ta gama tace musu "to bari in tafi kawata ce take nema na"
Suka ce "to ya Nabil din fa zamu zo ai mu duba shi a boys section din"
Tace "yana lafiya, wannan zata raka ku ai ta san ajinsu" ta fada tana nuna Maryam sannan tayi gaba.Nawal tace tabdi "wannan fa tace miki, gaskiya kina raga mata"
Maryam tace "ai ita gani take yi kamar tsoronta nake ji, nan kuwa bata san wawiya na mayar da ita ba"
Anisa tayi dariya tace "kawai dai kin saba ne da halinta"
Maryam tace" Ni daman saboda ke nazo mun dade bamu hadu ba, kwanaki da nazo Abuja ke kuma bakya kasar"Anisa tace "nima naji dadin ganinki, don kayan da mukayi order sun iso, ranar litinin ma nayi niyyar aika miki naku, amma uwargidanki bata cika kudinta ba"
Maryam tace "kar ki damu, Baban Nabil zai cika miki, shi Allah Ya dorawa"
Anisa tace "ai baya jin kudin, sanata ne fa "Maryam tace "kune ai manyanmu, ke PhD holder, mijinki FIRS chairman "
Nawal tace " Allah Ya sa nima dai mijina wani ne da naji haushi irin yadda kuke koda kanku haka"
sukayi dariya suka ce "sorry CEO Nawal Mall, matar CEO Kabir and brothers rice mills.
Maryam tace "yauwa kinga kuwa kar in manta, Baban Nabil yace yana ta kiran Fauzan wayar sa a kashe zancen shinkafarsu ta birnin kebbi, ance an gama gyara ta har an loading gobe motocin zasu taso.
Anisa tace "Fauzan suna meeting da Shugaban kasa, amman bari in fadawa Kabir sai suyi magana "
'yan biyun Maryam ne suka zo suka ce "mama nan kika zo muna ta neman ki"
tace "ina nan. Ina kuka baro yusra da yasir"
suka ce "suna gurin maman su, ta basu cake mu kuma tace uwar mu tazo ta bamu shine fa muka taho nemanki"
Anisa tace "Oh Saudat me hali bazai dena ba, yanzu a cikin jama'ar nan inda sun bata fa"
Maryam tace "sai tafi kowa jin dadi. Ai Alhamdulillah ma yanzu kowa da gidanta, ba abinda yake shiga tsakanina da ita. Kayannan ma kawai don babansu ne amman so nake mu dena kasuwancin tare"
Nawal tace da yaran "Hassan da Hussain kuzo ga abinci ku ci kunji"
Anisa tace "kasuwanci da ba ke zaki biya ba, kawai kar ki damu. Allah Ya hada ku ba yanda zaki, ga yara a tsakaninku baza ku taba rabuwa ba"Maryam tace "ban miki ma Allah sanya alkhairi ba fa, naga pictures din Sabon gidanku na nasaraw GRA, Kai maa sha Allah, gida kamar a turai, TubarkAllah, Allah Ya sa rai aka yiwa"Anisa tace "aameen ai a can ma muka sauka, kizo muje ki gani, kawai ma ki kwana gobe sai ki tafi"
Nawal tace " uwargidan ta fa"
Maryam tace "daman ba tare muka zo ba kowa da driver dinsa, Kara kawai nayi mata nazo visiting din danta, darajar mijinmu kuma, inba don haka ba ko neman inda suke bazanyi ba"Anisa tace "ki cigaba da hakuri, Allah Yana sane dake"
Maryam tace "kinga ni yanzu bana damuwa fa, tsakani na da mijina akwai so da kauna da fahimtar juna Alhamdulillah, sam ita bata gaba na"
Nawal tace "jarabawar rayuwa ce kowa da irin tasa, amman idan mutum yaji tsoron Allah, Ya barwa Allah lamarin sa sai kiga komai yana zuwa masa da sauki. Ji dai Anisa da Fauzan da suka sa Allah a lamarin su yanzu duk sun cinma burin su a rayuwa. Babban abin sha'awa kuma yanda kullum suke nunawa junansu kulawa da girmama juna duk da kowannen su yana ji da kudi da ilimi"Maryam tace "kedai ki bari kawai Nawal, soyayyar su tana birge ni, na dauka idan aka shekara goma da aure an gama soyayya sai zaman hakuri da zaman 'ya'ya kuma"
Anisa tace "haba dai, ai soyayyar tafi dadi lokacin musamman ma idan soyayyar don Allah aka gina ta ba don wani abun duniya ba"
Suka ce "zancen ki hakkun Dr. Anisa Ta Alhaji Fauzan Shugaban gidan kudi"
Duka suka sa dariya.
Alhamdulillah anan Nakawo Karshen littafina me suna SOYAYYA DON ALLAH (LOVE AT FIRST SIGHT) da fatan Anji dadin karantawa ankuma dauki darasin dake Ciki....
For comments and feedback follow
I. G @ummnihal2
Facebook @ Asma'u sharubutu
Wattpad @ummnihal
I'll be waiting for ur messages love uh all,ur feedback is important🌸and it will surely encourage me to release d next book😍😍
BINABASA MO ANG
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020