Soyayya Don Allah
(love at first sight )
By Ummnihal10
An daura auren Fauzan da Anisa a ranar sha biyu ga watan January (12/01/2013), a masallacin juma'a dake unguwar koki. Farin ciki a gurin Fauzan baya misaltuwa, abokan sa sukayi masa caa a ka, suna fadin ya shammace su, daman da biyu yake zuwa gidan Dr Mallami every weekend, shi dai yana ta musu dariya kawai.Ango da abokansa sunzo gidan kakannin Anisa, sunyi gaisuwa da godiya kamar yanda al'ada ta tanadar. Amarya da ango sun dauki hotuna gwanin ban sha'awa kowa sai tubarkAllah maa sha Allah yake furtawa.Fauzan yazo daidai kunnen Anisa yace "kin zama tawa, daga yau kin gama yafa mayafi sai hijab da nikab" tayi murmushi kawai a zuciyar ta tace kai ka sani.
Da yake duk yan uwansu Anisa daga bangaren Umma har Abba duk yan Kano ne, kamu kawai sukayi a Zaria ranar alhamis, da niyyar su taho kano ranar juma'a da sassafe sai ayi walima da kuleran a yammacin ranar, amman sai motarsu ta lalace a hanya, basu suka shigo kano ba sai bayan maghriba. Saboda haka bayan daurin aure za ayi walima da kuleran din.Sai gwaggo kakar Anisa wadda ta haifi Abba tace ai saidai a hakura da kai amarya yau sai washegari, don a samu damar gudanar da kuleran din yanda ya kamata. Don ita a ganinta idan ba ayi wannan al'adar ba to auren zai iya samun matsala.
Ai koda zance yaje kunnen Fauzan take yace "ina baza ta sabu ba wai bindiga a ruwa, wannan ai ganganci ne da yiwa sunnah katsalandan, ya za ayi an daura aure yau ace sai gobe za a kai amarya, bazai yiwu ba" ya dakko wayarsa ya kira Anisa.Rashida ta mika mata wayar tana fadin angonnan naki akwai naci. Tana dagawa ya fara ce mata "ki shirya da anyi la'asar 'yan daukar amarya zasu zo", tace "ai ance sai gobe" yace "inji wa" tace "gwaggo" yace "to bani gwaggon" Anisa ta kaiwa gwaggo waya tana ce mata angonki ne yake nemanki.
Cikin wasa da dariya suka gaisa, nan Fauzan ya fara cewa gwaggo ai babu kyau a daura aure yau amman baza a kai amarya ba sai gobe indai ba da wani kwakkwaran dalili ba, gwaggo tace "wa'azi kakeyi min kenan, to baza a kaita din ba, in kaga dama kazo ka sace ta" ta kashe wayar, Anisa bata ce komai ba ta karba wayarta ta bar inda gwaggo take kafin fada ya dawo kanta.Da Fauzan yaga bai samu dama ba a gurin gwaggo sai ya tafi gurin Babanshi akan sai ya Kira Abban Anisa ya sa an kai masa matarsa yau. Haka kuwa akayi.
Abba yaje ya lallaba gwaggo yace tunda an riga da an daura aure a kai masa matarsa. Da yake duk fadan gwaggo, akwai wata irin kauna tsakaninta da dan nata bata iya yi masa fada ko musu musamman saboda shima baya yi mata musu.
Abba yace da Baba amman 'yan daukar amarya su bari sai da daddare don gwaggo ta samu damar yin kuleran din jikarta da yamma.An kai Anisa gidanta dake tudun yola, madaidaicin gida ne mai dauke da dakuna biyu da bandaki a tsakiya, sai parlor da kitchen, sai dan tsakar gida da akayi wani bandakin don amfanin baki.
Abokan ango sun rako shi, sunyi musu addu'ar fatan samun zaman lafiya da zuriya dayyiba, sannan suka tafi.
Ma'auratan biyu suka yo alwala suka gabatar da nafila kamar yanda addini ya koyar, sai Fauzan ya kama goshin Anisa yayi addu'ar da Annabi (SAW) ya koyar idan mutum yayi amarya ko ya mallaki sabon abu (akwai ta a cikin hisnul Muslim).Washegari 'yan uwan Fauzan suka kawo mata kayan lefenta, a daidai lokacin itama nata yan uwan suka iso da kayan gararta. Hajiya Najwa ta hada alkaki, dublan, gumba, soyayyen kaji, drinks da tukuicin #20,000 ta bawa yan kawo kayan lefe.
Satin Anisa shida a gidan Fauzan ta fara zazzabi da ciwon kai, Fauzan yaje chemist ya siyo mata maganin malaria, saboda unguwar su sabuwa ce akwai sauro sosai. Tana sha kuwa ta danji dama, sai dai kuma washegari ta tashi da matsanancin ciwon mara, can sai ga jini kuma. Sai ta dauka ko period ne bata daga hankalinta ba sai da yamma wani abu ya fito mata a dunkule kamar yaɗi na nama. Ta samu roba mai kyau ta sa abin a ciki.Tana ta jimami me zai kawo wannan abin daga jikinta, nan ta tuna fa rabonta da menses tun kafin tayi aure, karatunta na biology ta tuna, kar dai ciki ne da ita, taje ta sha maganin malaria ya kawo mata abortion.
Da Fauzan ya dawo take fada masa halin da ake ciki, hankalinsa yayi matukar tashi, don shi yayi mamakin ganin nutsuwa a tattare da ita. Take yace ta shirya suje asibiti. Likita kuwa yana ganin abinda suka zo dashi da kuma bayanin da sukayi masa ya tabbatar wa Anisa da zarginta.
Likita yana ta fada, ya canja mata wasu magungunan, sannan yace taje ayi mata scanning, idan da sauran dattin cikin sai ayi mata wankin ciki. Anisa ta tuburewa Fauzan akan ita bata son wankin ciki, haka ya hakura ya kyale ta.wannan shine mafarin matsalar Anisa a zamantakewar aure, domin akwai sauran datti a cikinta, wanda ya hana ta daukan wani cikin, kuma sannan ya sa mata tsamin jiki, da kaikayin gaba musamman saboda tana amfani da ruwan sanyi idan zatayi tsarki.
😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
Soyayya Don Allah
General FictionLabarin masoya biyu, rayuwar auren su da haƙuri da juna #14 hausa 23/10/2020