16

34 8 0
                                    

Soyayya Don Allah
(love at first sight)
By Ummnihal

16
Anisa tayi matukar mamakin abinda Saude tayi mata, amman ta kawar da zargin da takeyi na ko hassada ce ta sa ta aikata hakan.

Yau kwana shida kenan Saudat bata kara shigowa gidan Anisa ba. Da take fadawa Fauzan sai yace "aiko dai baki kyauta ba, kika san ko bata da lafiya ne ai da kika ga bata shigo ba sai ki je ki ga ko lafiya"

Tace "to ai gani nayi inda bata da lafiya ne, mijinta zai fada maka"

Yace "kin san ba sosai muke haduwa dashi ba, ina riga shi fita, kuma a office ba department dinmu daya ba, in an tashi kuma ba gida yake tahowa ba cikin gari yake tafiya, sai bayan isha yake dawowa"Anisa tace "ba ze dawo gidanshi yaci abinci ba?
Yace "to kin san kowa da nasa irin tsarin"
Tace "shi yasa matar sa ba abinda ta sani sai harkar kayan mata, abinda kadai yake shiga tsakaninsu kenan, ai ba haka tsarin aure yake ba"
Yace "to ki dinga bata shawara yanda zata dawo da hankalin mijinta gare ta, daga haihuwa daya bai ci ace miji ya fara kauracewa gidansa ba"
Tace "hmm ita ai gani takeyi kamar nice ban san abinda nakeyi ba"
Yace "to Allah Ya kyauta, ki kokari anjima ki je gidan ta kiga ko lafiya"
Tace "to habibi "

Saudat tana jin sallamar Anisa tayi mata banza sai da me aiki tazo ta bude mata. Bayan sun gaisa Anisa take tambayar ta ko lafiya kwana biyu, a ciki ciki take bata amsa wai lafiya kalau. Anisa tace "to shikenan ni zan tafi"
Saudat na daga kishingide a kan kujera tace mata "to ki gaida gida " Watan azumi ya kama, yanayin gari ya canja, yamma nayi garin yake cika da kamshin soye soye yana tashi. Hankalin Saudat ne ya kasa kwanciya, bazata iya zama ba sai taje gidan Anisa taga halin da take ciki. Yau tayi niyyar har dakunan ta zata leka.

Sallama tayi bata jira an amsa mata ba ta tura kofar ta shiga. Anisa tana kitchen ta amsa mata tace kin ganni nan a kitcen ki karaso.

Tana shiga ta karewa kitchen din kallo tun daga sama har kasa. Kwata kwata an canja masa fasali kamar ba iri daya ne da nata ba. To ita kitchen dinta ko kanta babu, wannan kuwa an zagaye saman shi da kanta yayi L shape. Ga kayan amfani nan kala kala, komai sabo ne, kuma anyi arranging dinsu gwanin ban sha'awa.Anisa ta basar da kallon kurillar da taga anayi wa kitchen dinta da fara'arta tace " yau maman Nabil ce a gidan mu, kuna nan kalau ya Ibada"
Saudat tace "lafiya lau"
Anisa ta debo dankalin turawa zata fara ferayewa da peeler Saudat tace "mu gani minana kuma wanga abu"
Anisa tace "abin feraye dankali ne"
Ta jujjuya shi ta miko mata ba tare da tace komai ba. Anisa ta karba da niyyar ta fara feraya amman me, sai ji tayi abu ya karye, raga raga abinnan yai a hannun ta yanda bazai taba gyaruwa ba, Saudat kuwa ko a jikinta kamar bata ga abinda ya faru ba. Anisa ta dakko wuka ta cigaba da aikinta. Saudat tana zaune tana tayi mata iyayin da ta saba.Anisa tace "haihuwa ta daya me zanyi da me aiki"
Tace "ai wannan aikin duk ba naki bane, kamata yayi yanzu kina kwance, me aiki ce zata miki komai"
"wannan ba tsari na bane gaskiya, sai nayi kamar yara uku sannan zan dauki me aiki kuma ba wai zan sakar mata gida na bane in tafi in kwanta, zata dinga taya ni aiki ne kawai, muna yin komai tare" inji Anisa
Saudat tace "ke kika sani, ana nuna miki hanyar hutu, kina kin bi, ban san randa zaki waye ba, koda yake baki shiga jami'a ba kinga yanda yan gayu suke rayuwar su"
Anisa tayi dariya tace "ke a jami'ar kika koyo gayun kenan, ni da naji ance yan jami'a "yan iska ne"
Saudat tace "ke ji jahilcin ai irin na wanda basu san boko ba.  Kinga ni dakina naka son in canja ma fasali, Shina nicce bari in tambaye ki yanda kinka tsara naki"Anisa ta kwatanta mata amman sai cewa tayi to ki nuna min mana in gani. Ta taso ta bude mata daki daya, ta gama kare wa dakin kallo cike da bakin ciki. Tace "dayan fa,
Anisa tace "dakin miji na ne, kuma duk tsarin iri daya ne"
Tace "to me miji" bata kula ta ba ta Kama hannun Suhaima da ta gama cin abinci ta tafi wanke mata. Da Saudat ta tabbatar bata ganin ta sai ta murda kofar daya dakin ta leka, ta jawo a hankali ta rufe.

Haka ta bar gidan Anisa cike da bakin ciki da fargaba. Lallai sai tayi da gaske kar Anisa tazo ta fara raina ta kuma. Bata kara tsinkewa da lamarin Anisa ba sai da taga tayi baki, ji tayi ana ta horn ta leko ta ga ko suwaye, motoci ta gani lafiyayyu masu numfashi guda uku a kofar gidan Anisa. Maza ta gani dattijawa su biyu da matasa hudu sun fito daga motar, sai ga Anisa nan ta fito da farin ciki tazo ta gaishe su Sannan suka shiga ciki.

Suna tafiya kuwa Saudat ta shigo take tambayar ta su waye. Anisa tace "Abba na ne da kaninshi, samarin kuma 'ya'yan yayarsu ne. Abba yazo workshop ne ya taho dasu don suga inda nake mu dinga zumunci"

Saudat ta jinjina kai a zuciyar ta tace wato dai wannan 'yar masu kudi ce.

Da sallah kuwa haka 'yanuwan Anisa dake cikin garin sokoto sukai ta zuwa gidanta, saboda mahaifinta yana da zumunci sosai, indai ya samu lokaci yana zuwa inda suke, musamman in akai rasuwa ko daurin aure ko in aiki ya kawo shi.Abubuwan da Saudat take ma Anisa sun fara bata tsoro, don wani lokaci gani take kamar tana yi mata asiri. In dai ta shigo mata to sai wani abu ya lalace, ko tana kallo Nabil zai dauki kayan wasan Suhaima ya lalata. Har sai da Anisa ta ke kulle dakin Suhaima idan suka zo.

Sabuwar wayar da Fauzan ya siya ma Anisa ce haka kurum ta dauke, da aka kaita gurin gyara kuwa sai cewa sukai ai injin ya buga. Daman tunda Saudat ta ga wayar hankalin Anisa ya kasa kwanciya don tun da aka siyo mata take ta kaffa kaffa da ita.Anisa tace da Fauzan "ka samo mana maganin mayu, in yiwa gidannan hayaki, ina kyautata zaton matar nan kambun baka ne da ita"
Yace "ke dai kawai zato ki ke, kuma wa yace miki ana magani da hayaki, duk aikin shedanu ne hayaki. **Annabi (S A W) cewa yai mutum ya samu ganyen magarya guda bakwai ya daka ya sa a ruwa ya tofa surorin tsari kamar su Fatiha, Ikhlas, Falak, Nas, ayatul kursiyyu da amanar rasulu. Indai mutum ya tsarkake zuciyar sa ya kyauta niyya ya yi imani Allah zai tsare shi daga sharrin duk wani abin ki, ya sha ya shafa a duk jikinsa, sannan yabi duk kusurwar gidansa ya zuba ruwan, inshaa Allah babu abinda zai cutar da mutum. Zan samo miki ganyen magarya da ruwan zamzam sai ki kokari kiyi mana*****

Tace "to shikenan Allah Ya Kara Kare mu"
Yace "aameen"
😍😍😍😍😍😍😍

Soyayya Don AllahWhere stories live. Discover now