*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_**_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*Mutane nata tambayar page 9-10,kuyi hakuri mistake nayi wurin numbering nayi page 7-8 sau biyu idan ku ka duba labarin ya tafi dai dai,sai page na ranar Thursday ya kamata ya zama 9-10 na saka mashi 7-8 kuma.Ayita hakuri kuskure ne nagode❤*
TALLAH!!!
_*ƙungiyar brilliant writers na yiwa masu karatu abishir da sabon littafin ɗaya daga cikin haziƙar maruciyar da zai fito bada jimawa ba"RASHIB HAIHUWA(da ciwo)daga alƙalamin OUM FARHANA(habibah shehu)kada ku ku sake a baku labari*_
*🅿13-14*
Shiru ne ya biyo baya ko wane da abunda yake tunani a cikin zuciyar si har suke isa babban gida ya yi horn mai gadi ya buɗe tare da mashi barka da zuwa.
Tunda suka aje mota ya taimaka mata ta fito,samarin dake haramar gidan suke mata Allah sanya albarka(da yake ya kira kowa a waya ya faɗa masu),sai dai ta murmusa domin tana da alkunya,shike washe baki yana amsa wa har suka wuce inda mutane suke saura ƙiris su isa sashin hajia lanti yace,darling barin ɗauke ki nasan kin gaji da yawa ko?.
Waro idanu tayi waje,don Allah ka rufa mun asiri ina da kunya..,oh ni ne mara kunya ko?,wai naga ko irin ɗan alkunyar nan babu sai washe baki ka ke kana amsa gaisuwa.
Ah zee ALLAH ya amshi addu'ar mu na tsawon shekaru goma ha biyar yau ya azurta mu da samun namu rabon,jinin mu babu sirki!,kinga kuwa ba zan zama butulu ba ko?.
Haka ne,Allah ya inganta mana yasa rabo ne. Yawwa matata amin thumma amine,dai dai ƙofar hajia ya tura da sallama hanun shi ɗauke da kayan zainab....,tana zaune a palon tare da matar umar da yaranta suna karin safe.
Wuri zainab ta nema a ƙasa"ina kwana hajia,ina kwana aunty balki?",hajia bata amsa baa,ita balkin ce ta amsa a ciki bakinta cike da ƙosai ga kofin kunun gyaɗa gaban su,yaran kuwa shayi suke sha.
_wanan ya zama ɗabi'an surukan hajia lanti banda zainab,kusan kullum zasu kwaso yaran su a gidan zaa karya,aci na rana har na dare idan mazajen sun shigo nan zasu ci sanan su kwashi matayensu a tafi gida. Idan lokacin makaranta ne iyayen na wurin aiki daga makaranta aka ɗauko yara gidan zaa zube su sai dare a dawo dasu_Gaisawa suka yi da muhammad cikin girmamawa har da addua ALLAH raba lafiya balki tayi.
Hajia ta tsare gida hankalinta kwance tana karyawa,har ta gama suna zaune mai aiki ta kwashe kayan...,sai lokaci ta ɗago ta kalle su da kyau idanunta kur akan cikin zainab daga bisani tace,"ina mamin?",kallon juna suka shiga yi babu bakin magana domin hajia ta tsare su da ido,zainab ma kallon tuhuma take mashi!.
Cikin inda inda yace,ai na ɗauka tan nan wurin ki ....,da ka kawo ta yaushe?,"ta daka mashi tsawa!",ayi hakuri dai hajia wallahi koda na koma gida mun duba sosai a mai gadi bata nan,inda nasan za'a same ta naje bata.
Ƙarya ne wallahi kun yi kaɗan!,daga matar ka ta samu ciki sai a iza mun jika saboda ba sonta ku ke yi baa?,miƙewa tayi,na baka awa ɗaya duk inda take ka nemo mun ita!,tana kai nan ta wuce ɗakin ta cikin tashin hankali...,zube wa tayi bisa gwiwar ta hanunta duka saman kanta,sosai ta riƙe shi domin yana juya mata!
Mami!,mami ina kika shige ne?,idan kika yi nisa dani asirina zai tonu,kece rufin asirina!,shekaru ashirin ke nan ina ɓoye da wanan sirri don ALLAH kada ki guje ni zan tozarta a idon duniya domin kece maganin matsalata,cikinn nan na jikin zainab ba ƙaramin barazana bane a gare ni!.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
AdventureLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.