*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*
*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*🅿11-12*
Kallon zainab yayi cikin kulawa"kiyi hakuri mana Darling har wani lokaci",kamar zata yi kuka ta zame ƙasa daga saman kujera,yanzu ka mun adalci kenan?,wattani nawa rabona da iyaye na?,idan kai aka yiwa haka ya zaka ji?.
Wattani kika ce,akwai wacce zata share shekara bata ga iyayenta ba kuma suna a gari ɗaya bare ke da akwai taraza sosai a tsakani.
Cikin ɗaga murya ta fara magana, daɗin auren bai kai mun nan ba da zan man ta da iyaye na har tsawon wani lokaci ban waiwaye su ba,kamar yadda na faɗa maka idan kaga ban tafi tare da kuba zamu haɗu a can!
Ɗaki ta wuce abunta Mani nata kwasar dariya...,uhm mami taurin kai yayiwa mammyb ki yawa na rasa yadda zan shawo kanta. Kada ka damu daddy zan maka maganin ta yadda ko kara ka aje ba zata sake tsallake wa ba!.
A'a ban saki ba domin Ni al'amuran kima sun fara bani tsoro,wai meke damun kine?,dariya tayi kuma"kada ka tashi hankalin ka babu abinda zai faru da kai,sanin abinda ke damuna idan lokaci yayi zaka ji kuma ka gani sai da safe daddy!".
Ɗakin ta kawai ta nufa yana wurin zaune cikin mamakin ta ..,daga bisani ya kashe kayan wutan tare da rufe ko ina ya wuce ɗaki.
Tana kwance hankalinta ba kan waya
kamar bata da wata matsala a rayuwa,zee tashi ki haɗa mun ruwan wanka, ɗan guntun tsaki taja,nifa bana son damuwa kawai baka da halin ganin mutum yana hutawa sai ka dame shi!.Nike damun ki zee?,bayan kai akwai wani ne cikin ɗakin nan?,uhm Allah baki hakuri in shaa Allah zai haɗa ki da daidai ke ya wuce Ban ɗaki....,gyara kwanciya tayi tare da cigaba da surutai ƙasa kasa.
Yana tsakiyar wanka ta kwala ihuuu!,babu shiri ya dauro towel sauran jikin shi da komfa...,saman gadon ya haye tare da riƙo ta"meke damun ki?",zan mutu mara na ciwo kamar zai fashe!",hanunta duka biyu riƙe kam a marar ta.
Innalillah wanan masifa dame yayi kama,da an fita wanan a shiga wanan?,ya Allah idan wani laifi na aika ka yafe ni!,yadda take ihu haɗe da nishi sama sama yasa ya ƙara fita hayyacin shi domin yana matuƙar son matar shi abubuwa ne suka zo masu wani iri.
Bai tsaya sauya mata kaya ba kawai ya ɗaura babban hijab saman kayan bacci dake jikinta,ya saka jallabiya tare da ɗaukar wallet da key mota tana rungume a jikin shi ya nufi hanyar fita....,kiciɓis suka yi da mami a palo"ina kaza kai ta daddy?",ɗauko hijab ɗin ki asibiti zamu bata da lafia,ba zan barki ke ɗaya a gidan ba dare ne.
Ban zuwa ko iya,itama ai babu abunda ya same ta , ka rasa yadda zaka yi da ita ne sai nayi maka maganin taa!,kawai ka kuma ciki zuwa da safe zata warke sumul.
dakata!"ya daka mata tsawa",na rantse da Allah idan wani abu ya faru da ita,zan manta da soyayyar da nake maki sai na dauka mummunar mataki a kanki tunda na lura ke hatsabibiyar yarinya ce!.
Ni ɗin daddy?
tsaki jaya tare da nufan hanyar fita domin cikin halin da zainab ke ciki baya tunanin ko hajiyar shi tazo zai iya ƙyale zee haka nan.
Sai daya saka zee a mota sanan ya rufe mami ta waje sanan yayiwa motar gear...,ydda ya rinƙa horn yasa mai gadi buɗe masa gate da wuri.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
AventuraLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.