*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_**_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*MASU YAWAN NEMAN WANAN LITTAFI DAGA FARKO DON ALLAH DAI SU YI SEARCHING NA A WATTPAD@leemaMuhammad826,ZAKU SAMU UP TO DATE DOMIN SABODA IRIN HAKA NA BUƊE WATTPAD ƊIN BA DAN NA TAƁA AMFANI DASHI BA SAI DAN IRE IREN MASU NEMAN LITTAFI DAGA FARKO.INA FATA ZAA RINƘA MUN UZURI DON ALLAH DAI*
*🅿37-38*
Kuka yake yi na fitar hankali,yana buga kan shi a jikin motar!,zainab me yasa zaki mun haka?,dama soyayyar da kike nuna mun na ƙarya ne akwai ranar da zaki iya rabuwa dani?.
Jin shirun yayi yawa yasa shafi'u ya biyo bayan shi....,nan ya tsaya cike da mamaki!, ɗan uwanshi mai yawan fara'a da nagarta yau shine ki zub da hawaye akan mace?, ƙara sowa yayi tare da yunƙurin ɗaga shi ya jingina shi a jikin motar tareda buɓe wa yazaunar dashi a gidan baya,ya zagaya shima ya shiga.
Muhammad ka zamto mai tawakkali da yadda da ƙaddara mana!,sanin kanka ne baa kyauta mata ba kuma kasan halin matar ka akwai taurin kai sosai,amma na tabbata maka nan da ɗan lokaci sai tayi nadama kuma zata neme ka!. Suma iyayen nata nasan ɓacin rai yasa suka biye mata domin babu iyayen kirki da zasu so aurar da mace ta dawo gaban su.
Idan zaka iya mun wani alƙawari muhammad ka yi ƙoƙarin cdanne soyayyar zainab kawai ka riƙe addua da aikin ka wallahi ita da kanta sai ta neme ka!,ba dai a abuja take karatu ba kuma dole idan hutu ya ƙare zata dawo makaranta?,sanan kai ke ɗaukan nauyin karatun?,wallahi muhammad kana zaune zainab zata neme ka idan har ta ɗauki karatun da muhimmmanci,sauran ka bar komi a hannu na zan kula dashi yadda ya kamata.
Nan take yaji zuciyar shi tayi sanyi sanyi,yasan ɗan uwanshi zai iya yin komi akan farin cikin shi!.wanke fuskar ka kada ka sake ta gano kana cikin damuwa.
Haka kuwa akayi ya wanke fuska suka shiga cikin gari yawo....
Mama da zainab suka dawo cikin gida aka bar alhaji barau da baba wanda ke ƙara kwantar mai da hankali akan suyi hakuri tunda saki ɗaya ne zasu daidaita kan su idan sun dawo cikin hankalin su.
Mama ta kalli zainab zuciyarta bai mata daɗi ba da wanan saki domin ita uwa ce mai jajircewa akan tarbiyyar ƴaƴanta,bata ƙaunar suyi abunda zai zub da mutuncin gidan su a idanun duniya!
Yanzu ke wanan saki da kika matsa sai an maki menene fa'idar shi?,idan yan uwa,ƙawayen ki da makwaɓta suka tambayi dalilin zaman ki a gida me zaki ce dasu?,wanan abun da kika yi ba aikin hankali bane fa!,babban tonon asiri sirrin da ake ɓoyewa ne domin zancen duniya baya taɓa ɓoyuwa!.Gaskiya na raina wayau'nki,ina laifin kice ya baki ɗan lokaci kayi hutu a gida. Daidai hankalin ki ya kwata kuma an lura sun tuba da gaske sai ki koma ɗakin ki tunda sun yi nadama.
Gaskiya da nasan saki kike nema ba zan taɓa baki goyon baya baa!,ko mahaifin ki ai ba haka yaso baa,an baki dama ne ki ɗan huta a gida.maganar gaskiya ki canza tunani tun wuri idan an kwana biyu ki kira mijinki yazo ki koma.
Jin maganganun da mama ke faɗa akan zainab yasa safiyyah ta fito...,hawaye ta fara yi itama dai bata ji daɗin yadda yayanta ta nemi saki baa.
Zainab kam ko a jikinta domin burinta ya cika,zata ba muhammad da ƴan uwanshi mamaki koda ta koma makaranta ba zata taɓa neman su baa.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
PertualanganLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.