*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*
*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*To those that love this little book and me,may it's reader have no cause to say their time is but lost,may it persuade some that go astray to turn their foot and heart to the right way and find that discipline by which life can be successfully lived and good character formed.It is the Hearty prayer of"L££MA" to the readers and everyone out there💖*
*🅿23-24*
Kamar yadda kuka sani Ni asali na buzu ne haifaffen garin yamen dake jamhuriyar Nijar. Tun inada shekaru sha biyar a duniya iyayena suka yi hijira zuwa nigeria,Sokoto state a wani ƙauye mai suna boɗinga.
Cikin ikon ALLAH baffa na ya samu karɓuwa ALLAH ya haɗa shi da wani attajirin ɗan kasuwa a cikin birnin sokoto mai suna alhaji mu'azu wanda keda matar aure ɗaya amma ALLAH bai basu haihuwa baa.
Mahaifiyata ta kasance mai aikin wanke wanke da shara,baffana kuwa shike kula da gidan gonar su tare da dabbobin su mai tarin yawa saboda ya kasance mutum mai gaskiya da amana.
Har muka shekara muna jin daɗin zama dasu sai baffa na ya nemi alfarma zai kwashe mu zuwa ganin gida tunda an kwana biyu duk da yana yawan yin aike a kai akai. Alhaji ya nuna rashin amincewar shi domin bai san inda zai sake samun mutum mai amana irin baffana baa,nan dai suka yi shawara ni da innata zamu tafi mu yi kwana biyu.
Shirye shirye sosai hajia aisha tayi mana na zuwa gida da yake a gidan gona muke kwana an bamu ɗaki biyu ai kuwa cikin daren ranar yan fashi suka shigo gidan gonan nan take suka harbe baffana a gaban mu,suka buga mun gindin bindiga nan take na sume innata ma ta faɗi a sume suka kora shanayen masu yawa sosai.
Abunka da wajen garin ne baa san abunda ya faru ba sai da safe labari ya riski alhaji mu'azu wanda yazo a hargitse aka kwashe mu sai asibiti domin bai kula da ɓarnar da aka mashi baa.
Cikin ikon ALLAH na farfaɗo amma anyi mun ɗinki a goshi,innata kuwa tayi ɓarin ciki yayin da ALLAH ya yiwa baffa na rasuwa.
Sosai aka tausaya wa innata domin kuka take na fitan hankali idan ta koma garin mu bata san e zata faɗa baa,ba lalai bane a yadd mutuwar Allah yayi a wanan lokaci da ilimi yayi ƙaranci!. Haka dai aka shirya baffa na zuwa gidan shi na gaskiya muna ji muna gani.
Iya bincike baa gano ɓarayin nan ba,akace inata bata da takaba domin cikin wattani uku ne ya zube mata ,sai hajia Aisha da mijinta suka ɗauki soyayyar duniya suka ɗaura mun suke kula dani innata kullum zugum sai kuka.
Bayan wattani uku da faruwar haka alhaji mu'azu ya shirya da niyyar raka mu gida wurin dangin mu cike da abun arziki,hajia aisha ta ruƙi a bar mata ni ta saka ni a boko.Alhaji yace bashi da wanan dama saiya nemi izini wurn dangin baffa na.
Cikin ikon ALLAH muka isa ƙasar yamen har gidan kakkani na wanda suka haifi baffa na,hannu biyu aka amshi alhaji bayan innata ta masu bayanin ko shi wanene. Daga bisani ya masu bayanin abunda ya faru!, dama basa jin hausa sai innata ta sake masu bayani da yaren mu.
Abun ka da mutanen dori babu ilimi ba tawakkali suka shiga zage zage wai innata ta haɗa kai da alhaji an kashe baffa na don taga mai kuɗi ne tana son auren shi,zagi iri iri daga bisani suka ce sai an fiddo masu da gawan ko a biya diyya.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
AdventureLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.