*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_*NA*
*L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*
*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*🅿15-16*
Ruɗani ta shiga,wani sashi na zuciyar ta na gargaɗinta da bin umurnin shugabanta,yayin da wani sashin ke ƙarfafa mata gwiwa ta koma wurin iyayen ta har sai taga halin da suke ciki sanan ta wuce!,sai dai muddin ta bijire wa umurnin shugabanta rayuwarta zai shiga cikin hatsari wanda zai sanadin rashin cikar burinta.
Idan tayi nisa da iyayenta a wanan lokaci da suka fi buƙatar ta komi zai iya faruwa ciki har da rasa cikin dake jikin mummynta ko rayuwarta.
Muhammad da ɗan uwanshi suka garzayo gida bayan sun fi abunda ya kamata a cikin gari,koda suka iso gidan basu wuce ciki ba sashin Abban su nan suka nufa...,da sallama suka shiga cikin babban palon.
_Dattijo ne fari sol mai matsakaicin jiki,cike da natsuwa da kamala,yana sanye cikin yadi fari da wando ,hanun shi riƙe da babban littafi na addini da alama nazari yake yi_
Wuri suka samu a ƙasa gefe suna jira ya kamalla.,sai daya kai aya sanan ya miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya suka gaisa,"ya iyalen ku?",da sauƙi dai ABBA domin wani al'amari ne ya tunkaro mu a yau ɗin nan..
Ba dai rashin lafiyar zainab ɗin bane"ya tambaya?",cikin jimami shafi'u(babban yayan su muhammad) ya furta,yanzu maganar da ake bamu san inda zainab ɗin take baa,domin dai muhammad ya barta a nan gidan ya fita hajia ta kira shi a waya wai bata gidan!,gashi ita mamin tun da safe baa ganta ba ,inda ya kamata mun duba bata har wurin yan sanda mun kai rahoto.
Girgiza kai yayi cikin ƙosawa da hali irin na lanti!,kun tabbata ita zainab ɗin basu tare da mami?,A'a ABBA ni da kaina na kawo zainab gidan nan ita ɗaya.
Yanzu me ya kamata ayi?,sanin kan ku ne mahaifiyar ku zaman kanta take yi babu sauran igiyar aure a tsakanin mu,bani da wani iko a kanta yanzu!,tafi jin shawarar mu akan nawa.
Amma ABBA mun riga mun kira sauran yan uwan mu zamu yi zama na gaggawa tare da ita a gaban ka,lokaci yayi da fitar tsabgar muhammad da iyalan shi,iya gwargwado yarinyar nan tana mata biyayya,ranar data gaji fa ba zaa ji daɗinta baa!.Haka ne shafi'u ALLAH maku albarka,sai ku sanar da ita ai.
Shafi'un ya wuce sashin hajiyar su....,har ɗaki ya same ta,tana ganin shi ta shiga faɗa zainab tayi mata rashin kunya!
Sai da ta kai ƙarshe yace,idan ba damuwa hajia mu haɗu sashin ABBA akwai shawara da zamu yi akan lamarin.
Jimmm ta ɗan yi,shi baban naku ya shirya ko kai?,hajia don Allah ki rinƙa ba ABBA darajar da ALLAH ya bashi ,ko ba komi akwai zuri'a a tsakanin ku an zama ɗaya bai kamata yadda kike ƙoƙarin tuzarta shi cikin jama'a wasu lokutan!
Dataka can wawan banza kawai,duka bunda yake mun bakwa gani ko?,kada ku wuce gona da iri,wallahi wallahi idan ku ka kai ni maƙura sai na bankaɗo wani ƙuli nashi wanda baku sani baa!,idan yaso kowa ma yabar ganin mutuncin shi domin shi da wanan makirar hajia mariya sune musababbin shiga na tashin hankali wanda har yau na kasa fidda kai na,ban san ranar da zai fita baa!.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
MaceraLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.