*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_**_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*MACE MAI NEMAN ALJANNA WATTSAPP GROUP ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman a gare ku ALLAH SAKA MAKU DA ALHERI A KAN HIDIMA DA KUKE D AL'UMMA❤*
*🅿7-8*
Yaran da suka sha zoɓo su biyar ne reras jere tsakiyar yan
*ƘUNGIYAR ASIRIN* sai kuka suke yi saboda tsabar ruɗewa!.
Tsawa mami ta daka masu mai firgitar wa wanda ya saka su duƙe wa aƙasa kamar zasu faɗa cikin wutar dake ƙara kuruwa kamar ana zuba mai fetur.Kuyi ma mutane shiru ai ƙwaɗayin ku ya ja maku!,dama ina haƙe da ku irin cin zarafin da iyayen ku ke yiwa mummyna saboda rashin aihuwa,sai na kashe ku kuwa ma ya huta!.
Abunka da yara ne duka basu haura shekaru goma baa,ukun ma basu kai baa,ko wanne ya shiga rera marayar kuka mai ban tausayi sun ji an ambaci mutuwa ko wanne ya fara kiran"mumy,daddy!".
Suna ji suna gani mami ta bada umurni a ɗaure ko wanne cikin su jikin bishiyar dake jejin wanda ko wane bishiya akan babban rami a ƙasa mai zurfi wuta na tashi,saman bishiyar kuwa ƙarfuna ne masu tsini kamar allurai da ka ɗaga kai suna kallon ka jira suke kayi motsi su fara nasu aikin.
Dama saman tsaunin nan mami ta tashi sama kamar balbela hanunta riƙe da takomi,hannu ɗaya kuma babban ƙwarya ne ta nufi wurin da suke da zubar chaka ma kausar nan take zainab ta zabura daga baccin da ya fara ɗaukar ta a guje ta nufi sashin hajia lanti tana faɗin"kausar!"..
Koda ta shiga palon cike da ɗan mutum kowa yayi cirko cirko ana jimamin abunda ke faruwa,kutsawa tayi cikin mutane har ta isa tsakiyar palo inda yaran nan biyar ne kwance a ƙasa ciki ya haye kamar mai shirin haihuwa yau ko gobe!,mami na zaune saman kujerar data fara zama tun farko babu alamar tsoro ko damuwa a tattare da ita.
Ɗaya bayan ɗaya ta shiga jijjiga su babu mai motsi har ta iso wurin kausar ta ɗaga rigar ta,fasa ihu tayi tare da fido idanu a waje ganin alamar wuƙa an suke ta har jini ya bushe a jikinta!.
Cike da zafin nama ta nufi mami gadan gadan....,kawai ta kauce mata ta bugu da bango juwa ya kwashe ta ƙasa ta zube!
Mami ta isa wurin da take kwance tana shafa jikinta...,idan baki daina shiga hurumi na ba wata rana zaki yiwa rayuwar ki mummunar ila ne mummy!
Tana ƙoƙarin ɗagowa ta danne ta sosai!,a haba wanan ne kuma baki isa ba kawai kisha bacci lafiya sai da safe.
Babu wanda yabi ta kan zainab domin ba sonta ake baa,chirko chirkon da akayi jiran isowar jami'an tsaro ake yi an buga masu waya.
Abunda ya faru bayan fitar zinab a sashin hajia lanti shine;bayan mami ta gama ɗura masu zoɓon da yan mintuna suka fara amai!,idan wanan ya gama wanan ya fara tun ana ɗauka da zauƙi har suka galabaita kafin a nufi asibiti sun fita hayyacin su ba mai motsi.
Nan wuri ya kachame da koke koke sai kiraye kirayen waya...,aka tasa inna mardiyya mai aikin hajia lanti a gaba sai ta faɗa abunda ta zuba a ciki??
Rantse rantse ta shiga yi bata zuba komi ba domin ba aƙalla sun share shekaru tana aiki a gidan wani abu makamancin haka bai taɓa faruwa baa!.
Iyayen yara suka tirje akan lallai mami zaa bincika domin dai tare suka sha me yasa babu abunda ya faru da ita?.
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
PertualanganLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.