25-26

901 53 14
                                    

*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
       *NA*

          *L££MA*

wattapad
*@leemaMuhammad826*

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻

*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*To the many persons who have assisted in Inspiring and motivating me,reposting,sharing,following ,voting and comments of this little book of mine,heartfelt thanks are extended much especially;*

*Muhammad Kareem Kd(daddy)*
*Hassan ATK*
*Real hassena oganniya*
*Ummu abdallah*
*Majmiy jumare*
*Siyama Ibrahim*
*Jamila mopol*
*Saratu Musa*
*Aisha Abdullahi gwazawa (Mrs noor)*
*Aisha Isah Adamu(maman noor)*
*Mugirat Musa*
Husna kamshi*
*Aunty Maryam(maman Muslim)*
*Amina aliyu farin wata*
*Queen acid*
*Mrs ganza darling*
*Amira Raji*

*The catalogue of names is so extensive it cannot not be list all here,but I'm deeply greatful to all who have given of their love and time.*




*🅿25-26*

    Cike da borin kunya hajia lanti ta zaburo tana faɗin,sharri ne!, sharri yake mun bakin su haɗe da matar shi don a tuzarta Ni a gaban yarana!,amma Ni har mahaifina ya bar duniya bai taɓa shirka ba bare shiga wata
*ƘUNGIYAR ASIRI* ,mutum ne salihi bawan Allah bai riƙo da addini.

Ƙaryar banza kawai,"hajia mariya ta katse ta",ai dama na faɗa maku da kin san wanene tushen wannan mugun abun da baki nemi tonon asiri da ci mana mutunci ba!,ai yanzu kin ji ko?.

Don Allah rufe mun baki muguwar azzaluma ma irin ki!,waya kasa dake?,kai kuma tsohon banza idan har abinda kake faɗa gaskiya ne mene ne hujjar ka?.

Murmushi yayi irin nasu na manya sanan ya janyo wani ƙaramin akwatin ƙarfe irin na zamanin baya a gefen shi,duk yayi ƙura an ƙalgame shi da padlock.

Ina hajia lanti?,gani nan kusa da kai ai!,wanan akwatin na wanene?

Shiru tayi tana nazari...,sake  ɗago mata yayi"duba da kyau dai",na mahaifina ne,amma ina ka samo shi?,madallah ya furta yana ƙoƙarin murɗe padlock ɗin da hannu...,buɗewa yayi ya ɗago jan ƙyale mai ratsin baƙi  wanda yayi  ƙura sosai ,dogon tasbaha mai manya ɗiya wanda komin tsayinka idan ka zura a wuya zai ja maka ƙasa,takalmin jan fata sai wani ƙaton zube na azurfa sai ƙyalli yake daga karshe sai hoto black and white irin na zamanin baya.

Duba da kyau ki gani duka kayan wanene wanan?,shiru ya biyo baya tana mamakin yadda akayi ya samu kayakin domin dai tabbas duk wanda yasan mallam mahaifin su da wanan rawani,tasbaha,takalmi da zuben aka sanshi!,ba zata manta ba har laƙabi ake yiwa baban su da"mallam mai abun al'ajabi",sunan da ake kiran gidan su kenan domin duk mallaman dake garin ya banbanta dasu ta shigan shi,mu'amala da jama'a da kuma biyan buƙata nan take.

Ki buɗe baki kiyi magana domin koda mahaifin ki ya rasu aƙalla kina da shekaru ashirin da biyar a duniya bare kice baki da wayau na sanin shi.

Jiki a sanyaye ta furta,"eh duka kayan mallam ne",murmushi ya sake yi tare da ɗago babban hoton nan mai kama da cardburn paper na black and white ya miƙa mata,"duba ki gane idan akwai mallam a ciki sai kiyi magana".

Ai kuwa shine sanye da jan riga mai ratsin baƙi da rawanin nan a kanshi yana murmushi, zaune saman kujerar ƙarfe na azurfa,gefe kuwa ƙarama cephalopods(shugabar ƙungiyar su na  KKK KU KLUX KLAN).,sai sauran mutane na wanan
*ƘUNGIYAR ASIRI* suna taya shi murmar sarauta da aka bashi a matsayin mataimakin shugaban
*ƘUNGIYAR SU* ,yanzu kin yadda ko kina neman wasu hujjuji masu ƙarfi?

ƘUNGIYAR ASIRI☠️Where stories live. Discover now