*🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_
*NA**L££MA*
wattapad
*@leemaMuhammad826*_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*
*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*
*🅿47-48*
Ƙarfe shida na yamma a garin abuja tayi wa muhammad da hajiyar shi,gidan su ya nufa kai tsaya domin ajeta ya gaisa da abban su sanan ya nufi gida...Zainab kuwa yinin ranar haka ta yishi sukuku saboda ta lura mayah na mata wani gani gani wanda bata san dalili baa,ita ramatu ta kwashe yaranta tunda rana sun wuce can gida zasu jira isowar hajiya wuri yayi shiru daga ita sai mayah wace ke wani yatsine yatsine!,bata da wurin zuwa dama tun zamanta abuja sai gidan yusrah wace itama a sanadin muhammad ta ƙulla aminta da ita wacce matar abokin shi ne.Yunwa take ji sosai kuma da alama mayah bata girka komi baa.
Sai da suka gama cin abinci sanan shafi'u ke labarta mashi zuwan zainab wace yanzu haka take gidan shi.Wani farin ciki yaji ya mamaye zuciyar shi kenan Allah ya karɓi addu'ar shi matar shi ta dawo gare shi!,yaya gaskia ina matuƙar son zainab saboda haka ba zanyi wasa da wanan daman ba kawai zan mayar da auren mu tunda wata ɗaya kenan da sakin bata gama idda baa.
Dakata moha,kada ka sake zainab ta gano zumuɗin ka a kanta,baa yiwa mata haka nan inaso ka nuna baka ma san Allah yayi ruwanta ba a duniya,idan zaka iya kada ka sake ku haɗu domin dai na tabbatar maka zainab nan da ɗan lokaci zata neme ka da kanta idan taci wuya.
Gaskiya ba haka yaso ba amma dai ba zai iya bijire wa yayan shi bane.Shikenan zanyi ƙoƙarin yin yadda kace.
Sai da suka yi sallar isha'i sanan suka yi sallama da hajia kowa ya nufi gidan shi da alƙawarin ba zasu bari hajia tasan zainab na gari ba saboda zata ɓata masu shirin su.
Da yunwa ya ishi zainab da zanta ta shiga kitchen ta girka ɗan indomie,mayah na zaune palo tana kallon ta har ta gama ta zubo a plate ta kawo wurin mayah"bismillah ga abinci",aciki ta amsa bata ci.
Wuri zainab ta samu gefe ta zauna har ta gama ci tana zancen zuci kawai ita zama gidan ya isheta ba haka ta tsara wa kanta baa,saboda me zata dawo ƙarƙashin ƴan uwan tsohon mijinta tama zama har yariya ƙarama sa'asar ƙanwarta safiyyah na mata rainin wayau!.Ya zama dole a yau ta bar gidan ba zata iya ƙara kwana baa.
Alamar tsayin mota ya dawo da ita daga tunanin da ta shiga yi..,suka shigo har yaran suna yiwa mayah oyoyo,suka gaisheta lokacin iyayen sun shigo nan suka gaisa.Sha'fiu yace kiyi hakur mun jima bamu dawo baa,basu iso da wuri bane amma yanzu yana gida kina iya zuwa zan kai ki tunda dare yayi.
Ba damuwa nagode da ƙoƙarin ku,kawai ka bari zan tafi da kai na daga nan zan wuce masauki na...
Aunty zainab da kin bari yaya ya kai ki tunda dare yayi abun hawa zai maki wuyar samurai,"cewar mayah",da mamaki zainab da ramatu suka kalle ta domin dai tunda zainab ta zo gidan ba wata maganar arziki ke shiga tsakani su ba har gaisuwar ma da kyar take amsa wa.
Ita mayah tayi haka ne saboda kishi,bata so zainab ta tafi ita ɗaya su keɓe da muhammad kada wani abu ya shiga tsakanin su!
Ka barshi kawai zan tafi ba matsala ai.Ɗakin ta koma tare da haɗo kayanta ta fito kenan suna sallama da mutanen gida taji alamar tsayuwar mota....,tana ƙoƙarin fita ne suka yi kiciɓis da muhammad!
YOU ARE READING
ƘUNGIYAR ASIRI☠️
AbenteuerLABARI NE WANDA YA ZO DA SABON SALO MAI MATUƘAR RIKITAR WA,BAN AL'AJABI, FADAKARWA,ILMANTARWA TARE DA NISHADAN TARWA.