part four

105 8 0
                                    

Bayan tashin ta abacci nee tayi sallahn la'sar taci abinci suka shiga Hira da Ammin taa
A bangaren sa kuwa in Banda tunanin najlah babu abun dayake yi. Ganin hakan bazai Mai bane ya tuna da cewar Maryam tabashi namaban ta ai take ya dialing Yana ta ringing baa dauka bah har wajen 5 missed calls hakan yasa ya hakura zuwa wani lokaci Koh tana aiki nee.
Dawowanta daki Kennan ta duba wayanta Wanda taga missed calls hakan yasa takira don taji waye.
Wayanshi nee yafara Kara alamun Ana Kira hakan yasa shi cirowa daga aljihun sa. Ganin Kiran daga Wanda bai yi tsammani bane yasa shi tattaro hankalinshi guri daya da kuma barin duk wani Abu dayake yi.
Assalamu alaikum  barkah da warhaka.
Wa'a laiki salaam barka dai, sunana khalamu Waheed. Nakarbi number ki agurin Maryam nee don in sanar dake halin dana ke ciki akan kin. Gabadaya nakasa samun nutsuwa tun ranar Dana fara ganinki, Najlah kitaimaka ki karbi kokon bara na koh nasamu sanyi araina.
Ai dajin wannan maganan takashe Kiran hade dayin blocking nambar sa,   Wanda hakan yasashi  tunani kala kala Wanda yakasa cimma matsaya.
Abun datake gudu ne yafaru dan da tasan shine  Koda Wasa bazata taba Kira bah Amma inaaa.
Maryam ce takirata takecewa haba kawata yanxu khalamu Waheed yakirani yake cemin Wai kin kashemai waya batare da kingama Jin Mai zai fada bah.
Toh Ni ina ruwa na. Ai kin sani bana son maganan Data shafi samari and yet u gave him my number.
To allah ya kyauta Najlah don bansan mezance dayafi hakan bah.
Amin cewar Najla. Gobe inason zuwa gida anty amrah kozaki rakani?
Badamuwa zan tambayi Mami
A haka suka kashe Kiran nasu.

Tana Gama waya da Najlah takira khalamu Waheed take cemasa kawartawa ce Sai a hankali batason ai mata maganan so ballanta aure gashi  naga Kuma Kai kaman dagaske kakeyi.
Ai wallahy Maryam dakin San yanda nake Jin son NAJLAH araina dabaki Fadi hakan bama. A rayuwata bantaba yadda da kalman so bah Sai haduwata da Najlah sosai nake kaunarta wlhy.
Toh kar kadamu inshallah zan taimaka maka gurin samun soyayyan ta fadar Maryam
Gaskiya naji dadin wannan maganan nogode Allah yasaka
Tace amin. Ehennn kafin namanta tace mun gobe tana son zuwa gidan aunty ta ya kake gani idan natura maka address din ka hadu da ita acan?
Kai Amma dakin Gama min komai Maryam gashi dama tayi blocking number na
Toh badamuwa zan turama
address din muhadu acan
Yakashe wayan Yana godiya wa Maryam.

Tagama shirinta tsaf kasancewar yau sunday ne ba school dama ta sanarwa ammi zuwa gidan aunty amrah.              Sungama break fast Kennan take cewa ammi yini fah yau zanyi don Sai bayan asr zandawo.
Toh emmatana badamuwa ai ga basma zatana daibemin kewa kafin ki dawo.
Ga wannan turaran kikaiwa auntyn naki koh.  Takarba tana Mai daukan car key dinta da jakan ta. Ammi nashige Sai nadawo, toh adawo lapiya .
Bayan tagaida shi ne ya bude mata gate Yana mata adawo lapiya.

Isarta gidan su Maryam Kennan tasamu Mami a Palo tana kallo. Cike da girmamawa tagaidata hade da tambayar Maryam
Maryam na sama ki haura ki same ta
Tace toh.
Ko knocking batayi bah tashige dakin ta tana Mai cewa ke kullum Sai anyi ta jiran ki Koh Sai kace Mai zuwa sama kiyi ta shiri, gashi Kuma duk Shirin ki saina fiki kyau. Takarashe maganan tana kashe mata ido daya
Toh ai dama ke Mai kyau ce najlah ban Isa hada  kaina dake bah tafada tana murmushi
A jere suke sakkowa suna raha.    Mami zamu wuce cewar maryam. Toh emmatana adawo lapiya koh. 

Suna Isa gidan aunty amrah suka ga mota a kofar gidannata ga wani hadadden guy a jingine da motan.
A cikin halin ko inkula Najlah tayi horn a bude mata tai shigewarta ciki.  Suna shiga ciki suka sami aunty amrah a kitchen tana hada breakfast cos  basu tashi da wuri. Ji kawai tayi anyi hugging dinta tabaya juyuwanta kenan taga najlah ai sosai tayi murnan zuwan su.
Haba Najlah nikam ma nayi fushi ace yau wata na guda kenan Amma Koh kizo ki duba Ni, is that how much you love me?.
Haba aunty wallahy bahaka bane kinsan munkoma school gashi banida wani free day this time around Sai weekend. Toh naji ya kike ya ammi ? Lapiya Lau ga wannan tace akawo miki.  Kai Amma nagode shiyasa nake Kara son ammi.
Nikuma Baki sona Koh takarasa maganan a shagwabe
Na Isa wane Ni ince banison my one and only najlah.

Tou idan kungama Sai kutuna Dani cewar Maryam tafada tana cinno Baki gaba. Allah sarki Maryam dina kiyi hakuri inafama dawannan kawartaki ne. Ya gida ya su mami? Lapiya klau tace agaida ki. Tou in amsawa

Yaukam saboda Najlah tazo ko break fast anhanani Koh?
Na isa wane Ni kunga barin je ingyara  cikin maigida na gwara ku cewar aunty amrah.
Ya Ahmad ina kwana suka fada atare
Lapiya Lau ya gida.
Kowa lapiya suka ce agaida ku. Toh muna amasawa.
Sweetheart nagama breakfast nizan wuce. Toh baby adawo lapiya Allah yabada sa'a.

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now