PART TEN

77 4 3
                                    

ASSALAMU ALAIKUM 'yan uwa barkan mu da wannan lokaci Mai albarka.
  Safiyar yau antashi da ruwa sosai agarin abuja Wanda hakan yasa najlah fasa Shirin tadakeyi nazowa makaranta ganin ruwan yaki tsayawa ga Kuma tsawa da akeyi yasa ta tafiya     Dakin ammi saboda  tsoran tsawan tadakeyi 😂 (thunder)( just like me🤣) inda ta iske basma suna ta Hira da Ammin hakan yasa ta zauna suka cigaba da hiran su cikin raha da jindadi.
Bangaran khalam kuwa yatafi asibiti abun shi inda ya iske patient najiranshi hakan yasa yayita aikin shi ko zai daina tunani najlah Amma inaaa yakan danyi jifa jifa.

Alhaji lawal ( baban khalam)ya dawo daga kasar France inda matar nashi hajiya saliha tai mishi tarba Mai kyau. Yaci ya Sha sannan yata zumbulawa matar nashi addau don sosai suke kaunar junan su. Bayan yayi wanka ya huta nee take fada mishi halin da khalam yake ciki akan maganar soyayyan shi.        Alhaji yaji dadin maganan don dama Yana ta adduan ranar da khalam zai amince yayi aure saboda sunyi takawo mishi tayin cousins dinsa Amma yaki. Amma alhaji wani hanzari ba gudu bah yarinyar fah kaman Bata sonshi don har blocking number sa  yace min tayi. To hajiya idan Banda abunki Bakisan soyayyan yaran yanzu bane 🤨 idan kikace Zaki shiga tsakaninsu ma kunya Zaki ji kirabu dasu dakan su zasu settling.  Amma fah alhaji..... Bata gamaba ya tsareta habe hajiya kinfiya shagwaba yaron Nan toh ko soyayyar ma Zaki mishi nee don Naga alaman Baki so yawahala.                    To Amma alhaji har zazzabi fa Naga yayi ranan, nikam ma harnace idan kadawo zamuje gidan su yarinyar amai tambaya!. Toh naji za'aje Amma bayanzuba harsai sun daidaita tukun.   Toh shikenan, hajiya tafada tare da cigaba da yimishi massage.

Wayan hauwane yafara ringing hakan yasa takarasa da sauri don Jin update akan plan din su. Maryam nee tafara magana inda take cewa
Maryam:Kuluwa kinsan meyafaru kowa?
Hauwa:Ni dallah malama kidaina cemin Kuluwa sunana hauwa
Maryam: to koma meye kekisani. Wai kinsan yarinyar Nan taki karban jakan nan
Hauwa: karki fadamun! Amma Naga Kullun magananta kenan akan tana sun tasiya
Maryam: hmm wlhy ina fada Miki Bata karba bah Amma yabani zan gwada Bata idan zata karba
Hauwa: toh shikenan idan takarba to idan kuma taki zamuyi chilling da ita ai gaba takaimu gobaran titi a Jos.    Nikam fah halin Najla yafara damuna, babu kalan samarin dabasa zuwa gunta Amma Ina Taki sauraran kowa kiduba idan kyau nee Yusuf yazu taki idan kudi nee Salim yazu taki idan mulkine yareema yazo taki nibansan Kuma metakeso  a rayuwanta ba🤷.    
Maryam : wlhy bake kadai bah Nima narasa meyake damunta.
Hauwa : koma miye  Allah ya kyauta.          Nan suka kashe wayoyinsu bayan sunyi sallama.
  Bayan ruwa ya tsagaitane najlah ta koma dakinta inda tayi sallah sannan tasakko tashiga kitchen don nema musu abun daza su ci. Dan wake nee yazumata Rai gashi dama amminta naso hakan yasa tafara Shirin yi inda basma tazo ta tayata da gyara vegetables.       Sungama sun jera a dining inda najlah takira ammi suka fara ci.  Sunci sunsha sannan basma tawanke plates takuma daki inda taji gaba daya jikinta ba Dadi Wanda batasan musababbin hakan bah, tun tana iya jurewa har abun yagagareta tafara ihu da Neman dauki,    najlah nee kawai tajita don Bata tashi a dining bah tunda tagama hakan yasa ta nufi dakinta da sauri don ganin abun dayasata ihu. Tana Isa ta isketa a kwance a kasa dafe da mararta gabadaya ta gama galabaita, inbanda nauyayan ajiyan zuciyar datakeyi zakace ta zarce(mutuwa) hakan yasa najlah komawa dakinta tadauko mayafi da car key dinta.   Yanda take sakkowa a steps ne yasa ammi fitowa don ganin Koh lafiya.  Najlah lapiyanki kowa kike irin wannan sauri kaman Zaki Fadi? cewar ammi. Cikin sauri tace ammi basma nee batada lapiya gaba daya Bata hayyacinta zamu tafi asibiti nee.
Cikin gaggawa suka karasa dakin basma inda ammi takama Mata ita suka sata amota Sai asibiti.
Ganin halin datake ciki nee yasa aka nufi emergency room da ita inda Dr khalam yayi treating dinta sannan aka maida ta resting room inda yafito yasamesu sunyi jugum jugum, gyaran murya kawai yayi sannan yace kusameni a office murna fal aranshi don yaga sahiba🤓. Nan take suka tafi office dinshi inda har rige rige suke gurin shiga.  Gurin zama yanuna musu inda suka zauna sannan yafara da cewa bawani babban ciwo bane ku kwantar da hankalinku kasancewar wasu matan idan zasu fara period Sai ya wahala su toh haka itama yakasance da ita Amma zuwa anjima kadan zata farka sannan Kuma ga wannan magunguna zata na Sha zai rage Mata pain idan lokacin zuwan period din yayi, kar kubari afara Mata allura saboda ciwon dayake Mata saboda idan infara zata zama addicted to it sannan Koda yaushe Kuma Sai anmata kafin tasamu sauki sometimes ma koda anmata baizama dole yayi Mata aiki bah don tasaba yi.

Najlah Kam kanta nakasa tunda
yafara maganan period gaba daya kunya ya rufeta sai ammi nee take amsa masa. Toh Dr mungode. Zamu iya ganinta?ammi tafada.    Eh kawai yace duk hankalinsa na kan najlah Wanda ita batama ganeshi bah cos lokacin dasuka zo duk hankalinta Baya jikinta.

Yeee hope y'all are enjoying.  Wanna see more votes and comment cos that's what keep me moving. ,❤️💃💃

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now