part thirteen

58 3 0
                                    

Tun bayan sallah asubah datayi takasa komawa bacci. Jinta take cikin farinciki Wanda batasan musababbin hakan bah kodan fitan dazatayi nee ! Amma ai basabon Abu bane agareta fita da friends. Ganin tunani bazai Mata bane ta dauki alqur'ani Mai girama takaranta hade dayin adduan Allah yasa alkhairi ne wannan farinciki nata.
8 :00 dot tasakko da hada musu break fast ganin bawanda yatashi nee yasa takoma daki tayi wanka ta shirya cikin Riga da wando sannan tasa abaya kwalliya kadan tayi Wanda yakara fito da kyanta Sai dai ace Masha Allah.
Tana sakkowa taji muryan ammi a dining hakan yasa takarasa da gaidata cikin girmamawa sannan basma ta gaisheta.
gama breakfast dinsu kenan wayan najlah yafara Kara alaman ana Kira hakan yasa tadauka hade dayin sallama. Muryan hauwa da Maryam nee suke Mata magana a tare
Dafatan Kingama shiryawa don gamu nan a kusa da gidanku? Eh nagama Sai kun karasu sannan takashe wayanta. Dubanta yakoma ga ammi inda take cewa su Maryam nee suka Kira suji ko nagama
Toh Sai sunkaraso abun da ammi tafada kenan. Tana Gama rufe Baki suka ji horn inda najlah ta haura sama ta daukko jakanta.

Bayan ta sakko nee ta iske su a Palo suna gaisawa da ammi.
Ammi Bari muje Sai mundawo najlah tafada hade dayafa mayafinta sannan suka fice. Azatonta zataga motan Maryam Koh na hauwa Amma Sai bataga kodaya bah Sai bakowan BMW datagani Wanda batasan nawaye bah. Dubanta tamiyar gurinsu inda kowanne acikinsu ita yake kalla don Jin abundazata fada.
Waye yayi amarya acikin ku ne cewar najlah.
Hauwa nee ta nuna Maryam tace waye inba 'yar gidan Abba bah
Hmm gaskiya motan ta hadu namiki murna akashe lapiya shikuma Abba Allah yakara budi
Ameeennn suka fada atare inda suka shiga mota Maryam ne a driver seat tana Jan su.
Eatery suka biya suka saya snacks da drinks kafin suka shige

Cikin sauri yake shiryawa don ya Matsu yaga sahiba najlah. Kwana biyun dayayi bai gantaba har Karamin zazzabi yayi. Yagama shiryawa cikin dark purple jeans da ash T-SHIRT inda yasa takalminshi Mai kyau da tsada
Bangaren hajiya yayi yagaisheta sannan yanufi park yayi wa motansa key. Kusan 30 minutes yayi Yana tafiya kafin isan shi gurin

Da sahibarshi yafara tozali inda harsunfara game abunsu. Shiganta da yanayin rige bindigan nata yayi komai nata burgeshi yakeyi. Sunata game dinsu gwanin sha'awa da burgewa Maryam nee kawai ta lura da zuwansa.

Break time suka tafi inda tabude jakanta tadauki ruwa tasha. Tana Jin dadin wasan don kwata kwata Bata lura da zuwan shiba Wanda hakan yabashi daman Kara zagewa gurin kallonta don datasan dazowanshi dabazata sake har haka bah.

Sungama inda team din Maryam suka Fadi hakan yasa najlah take ta zolayanta itada hauwa. Kaya suka shiga canjawa inda kowa ya miyar da nasa kafin suka nufi hanyar mota, Sai a sannan nee najlah taganshi. Gaba daya tarsa me takeji data ganshi "bakin ciki nee, farinciki ne, haushine takasa babancewa"

Tsayuwa yayi Yana kallonta hartashiga mota kafin Shima ya shiga nashi yayi tafiyarsa, cikin nutsuwa yake tuki don ranshi fari yake tasss saboda yaga sahiba
Bangaren najlah kuwa tasa so agaba dole Sai sun fada Mata waye yake bashi information Akan abunda takeyi Wanda kowa yayi tsilli tsilli da ido yace bashibane atsakaninsu, hakan yasa taki yimusu magana har suka kaita gida Koh sallama Bata musu ba tayi shigewarta cikin gida.

Tafawa sukayi hade dayin shewa sannan hauwa tace koba komai yayana yayi farinciki daganinki and I can do whatever makes him happy Sai dai kiyi hakuri yarinya. Maryam nee takara dacewa hmm daga baya in Abu yakan Kama, soyayya tayi karfi har godiya za'a mana kibarta tagama haukanta tukun, nadan wani lokaci ne.
A haka suka tafi gida suna hiran hali irin na najlah

Khalam me ya Kira su yayi musu godiya sannu yacigaba da duba hotonan daya dauketa lokacin dasuka wasan. Sosai yake Kara Jin kaunar ta aranshi, bai taba neman Abu yarasa bah hakan yasa yake ji ajikinsa zai samu soyayyar najlah Wanda wani bangare na zuciyarsa ke karyata hakan

Hajiya nee tayi sallama a dakin nasa hartashiga ta zauna baisan tashigoba.
Karban wayan hannunsa tayi sannan tace wannan nee yarinyar. Daga Kai kawai yayi alaman eh
Dafa kafadansa tayi sannan tace ka kwantar da hankalinka inshallah idan alkhairi ce agareka zaka sameta sannan kacigaba da adduah kadaina saka tunani cikin ranka gudun Kar yaja maka matsala kaji. To hajiya inshallah zan daina kitayani da adduah. Ai addau ina Nan ina faman yimaka shi son. To nagode hajiya.
Banaso kana zama Kai kadai hakan yanabada kofar shigowar tunani daban daban kazo palo muzauna
Toh kawai yace sannan yashiga toilet leko kanshi waje yayi yace Sai nayi wanka nayi bacci tukun don nagaji sannan yarofe kofar.
Girgiza Kai hajiya tayi sannan tace Allah ya shiryamun kai. Ninatafi zan sa nawal takawo maka abincinka daki tunda kazama matar kulle.

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now