part twelve

64 4 0
                                    

Tun safe Mami take shirye shiryen girki da gyran gida don tarban mijin nata. Maryam kuwa murna fal ranta zata ga abbanta
Karfe 12:00pm dai dai yakira Mami yasanarda ita ya iso hakan yasa ta dauki mayafinta tashiga mota zuwa airport don dauko mijin nata.

Gaba dayan su sunyi murna da ganin juna inda ya kawo tsaraba Niki Niki bayan sungama sakawa a boot nee suka dau hanyan gida.

Shigansu gida kenan inda yasa gate man shigowa da kayan da suka dawo dashi. Sai faman raba ido yake yi ko zai ga tilon 'yar nashi but she is no where to be found hakan yasa ya shige dakin ta da mamakinshi Sai ganin ta yayi tana kuka 😲

Haba mamana (kasancewar sunan maman shi Maryam taci shiyasa yake kiranta da mamana) nazaci yau ranar farinciki nee agaremu amma Sai naga akasin haka yafada Yana Mai tallafota zuwa jikin shi
Maryam nee tafara magana cikin shagwaba tana cewa haba ABBA yanzo kamin adalci kenan kakira Mami tazo daukan ka bayan ina gida Kuma ko tadauke ni mutafi tare

Haba mamana yanzu akan wannan kike kuka!  Naji nayi laifi Ni da Mami don Allah ayi Mana afuwa kinji mamana yakarashe maganan fuskanshi a marairaice.

Toh naji nayi maka afuwa Amma Banda Mami. Hhhh toh tunda anyi mun afuwa nagode Sai kukare da maminki  acan.
Nan tayi hugging abbanta tare da yimishi sannu da hanya

Nan yabarta yatafi dakinshi Wanda yasha gyara ga Kuma kanshin turare kala kala dayake tashi
Wanka yayi sannan yasa kanan Kaya ya sakko zuwa dinning inda yasamu kowa jiranshi yake

Sunci abinci cikin jindadi da annashuwa. Bayan sungama nee ABBA ya Ciro key na BMW ya mikawa wa Maryam. 
Baki har kunne tarasa na cewa hugging din abban nata tayi hade dayi mishi godiya da adduah  Wanda Shima yaji dadin adduan nata 

Ammi nee tafara magana inda takecewa alhaji Maryam fah 'ya mace nee bai kamata kana batata da  expensive abubuwa haka ba, bakasan ina rawuyan aure zai kaita bah.

Toh ammi idan Abba bai munba waye zai mun gwara kibari yayi mun tun kafin Mai rabawa ya raba ko ya kace Abba tafada tana Mai da dubanta gurinshi
Sosaima mamana idan ban Miki bah ai banida Wanda zanmishi ke kadai Allah yabani Kuma ina gode Masa sannan ina alfahari dake, rabi da Mami kishi take jeki dauko mayafinki mufita musha iska kinji mamana

Nan tahaura sama tadauki gyalenta kalan kayanta tasakko suka fita inda basusan inda zasuba karshe dai a sahad store suka tsaya inda suka shiga sukayi siyayya sosai basu dawo gida bah Sai kusan magrib duk da gajiyan dake jikinshi haka yabiyemata suka ringa zuwa gurare daban daban

Barkanku da dawowa Mami tafada bayan sunshigo gida inda gate man yashigo musu da kayan siyayyan nasu  yauwa amaryana barka da gida cewar abban Maryam ganaki tsaraban inda yayi Mata nuni dawani katowan leda
Dauka tayi tana Mai farinciki da godiya.

Shigewarsa yayi daki yayi wanka sannan yakwanta don huta gajiya.         Mami nee tayi sallama inda tashiga dakin dauke da fara'a a fuskanta.
Barka da hutawa abban Maryam
Dubanta yayi cikin nishidi sannan yace barka dai amaryan abban Maryam. Dan dariya kadan tayi sannan tace kayi hakuri bawai nayi maka magana dazu dawani nufi bane kawai gani nayi kaman bai kamata ayi ta bata Maryam da irin wannan rayuwanba tunda 'ya macene dole gidan wani zata koma. Idan muka Saba Mata da irin haka a gida taje gidansa taga akasin haka ai kaga abun bazai yi dadi bah Koh

Alhaji nee yadan numfasa sannan yace hajiya dagaskiyanki Nima bason Raina bane nake Mata irin haka Sai dai idan natuna ita kadai Allah yabani Sai inga toh idan banmata bah babu Wanda zanmasa.

Toh alhaji adai rage gaskiya tafada hade dayi mishi murmushi
Toh amarya angama.
Nan suka cigaba da hiransu irin na manyan mutane cike da kaunar junansu

Bangaren najlah kuwa tana gida Bata fita bah kasancewar lecturer su yabada excuse akan bazai Samu zuwa bah. Hiransu kawai suke da ammi inda take cemata amrah jiya takira Akan tanaso gobe kije Mata yini tunda weekend nee.

Ammi kinmata nee Nace Miki gobe zamuje paint ball inyasuo Sunday sai inje Mata Koh

Toh Allah yakaimu Sai kikira kifada Mata Sai Sunday Zaki zo kartayi ta jiranki
To ammi zankirata  zancemata zamuzo da basma ma
Ah ah kibarmu basma insamu abokiyar Hira kafin kidawo inyaso wani weekend din Sai taje Koh cewar ammi
Toh shikenan.

Suna haka Sai jitayi text yashigo wayanta.  Sarai tagane daga khalam nee massage din Amma abun da daure Mata Kai shine tasan batayi unblocking numbern saba ya akayi text din shi ya shigo? tambayar datake wa kanta Kenan.
Ganin sudden change daga gareta yasa ammi tambayan Koh lapiya
   Lapiya Lau ammi bakomai barinje daki indanyi bacci kawai tafada hade ta ficewa daga palon tayi dakinta.



# vote
#comment
#share
💃💃💃💃💃💃💃💃

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now