part eleven

63 2 0
                                    

Dafatan muntashi lapiya. Allah yasa haka amin
A kwana atashi yau Kwanan basma uku kenan a gadon asibiti Dr khalam yaki Bata sallama bawai Kuma don Bata warke bane Sai dai acewar sa tazama mishi access nagani najlah kullum. kasancewar Kullum takanzo kafin tatafi makaranta idan tadawo Kuma Sai tayi abinci tatafi dashi asibitin ammi takuma gida haka suka cigaba dayi inda kullum Dr khalam Sai ya shigo duba su amman yaki sallama.
Ammi tatafi gida inda najlah tazo, sunyi Hira da basma sosai har take tambayarta ko tana Jin wani ciwo. Ah ah tacemata gabadaya ta warke hakan yasa tatashi zata tafi office din Dr inda suka hadu abakin kofa hakan yasa tabashi guri ya shige tabi bayanshi, gaishe da marar lapiyan yayi inda ta amsa mishi da tawarke hakan yasa najlah cemishi dama gurinshi zata je don neman sallama.       Har ran shi baiji dadi bah Amma babu yanda ya iya dole ya sallemasu hakan yasa yakoma office yarubuta musu takardan sallama yabasu suka tattara suka tafi.
  Bayan sun Isa gida an gama gyare gyare suka zauna apalo Ana Hira inda sukaji horn mal Ali yabude gate suna zaune zaman jiran Wanda zai shigo Sai ganin nawal sukayi ita da hauwa sunshigo hakan yasa najlah tashi tatarbesu.    Basma taji dadin zuwan kawartata  hakan yasa suka tafi dakinta suka fara Hira inda nawal  takecewa basma lapiya kuwa kwana biyu bikizo school bah
Basma: wlhy banji Dadi bane dazo muka dawo daga asibiti
Nawal : ayyarh sannu Koh dama kwana biyu daban ganki a school bane Nace barin zo induba ko ba lapiya bah sannan wayanki Kuma a kashe.
Basma: Allah sarki kawas nagode barin kawo Miki ruwa.  
Bayan takawo mata abun motsa bakine sukacigaba da hiransu na makaranta
Bangaren NAJLAH da hauwa kuwa Suma hiran su suke Sha inda hauwa take tambayarta Koh tana da free time this week don tanaso suje paint ball.   Najlah tayi saurin amsawa da eh cos that's her favourite game, a weekend Sai muje koh.     Hauwa tace to Allah yakaimu.
Sunsha hira sosai Sai dayamma suka tafi kowa a gidan yaji dadin zuwan su.
Hauwa nakomawa gida takira khalam da Maryam tafada musu akan ta amince da fitansu a weekend. Khalam Baki har kunne saboda murna. Sai dai kuma gani yake kamar bazai iya jurewa bah har kwana biyu kafin yakara ganinta, Amma to yazai yi haka dole zai hakura
  Washe GARI
Tagama shiryawa cikin atamfan ta Mai launin pink and coffee inda tasanya coffee veil, flat shoe tasaka inda tadauki hand bag dinta Wanda tasaka car key da wayoyinta Sai dakin ammi. Bayan sunyi sallama nee ta dau hanyan makaranta. 
Ta isa lapiya inda suka shiga class aka fara karatu. 
Bayan sunfito nee Maryam take Mata magana Amma Sam taki kulata tun ranar da abunnan yafaru Dan gani take kamar zata Kara yimata magana akanshi Wanda ita Kuma bata son hakan.
Haba najlah fisabilillah abunda kikeyi ya kyautu kenan intayi Miki magana Amma kishareni bayan nace Miki Nima bansan da zuwansa bah Amma kinki yarda dani. Shikenan idan Kingama fushin naki akwai abundazan fada Miki.    Tayi shigarta mota tatafi.
Sai bayan tatafi nee najlah taji ba dadi tasaba sukan danyi Hira kafin a shige gida Amma yanzu Abu ya sauwa. Tarasa maiyasa takasa yarda dacewa ba ita ta kirashi bah.  To Amma idan ba ita takirashi ba waye ? Takasa bawa kanta amsa hakan yasa takira number Maryam din don tabata hakuri Amma taki dauka hakan yasa tashiga mota ta nufi gidan su Maryam din
Tana shiga ta iske mamy a Palo tana bada aika wa ma'aikatanta  kasancewar abban Maryam zai dawo washe gari
A girmame ta gaisheta inda Mami ta amsa da fara'anta sannan tashige dakin Maryam inda ta iske ta tana waya cike da jindadi da annori a fuskanta da alama Koh saurayinta nee hakan yasa najlah zama gefe guda tana jiranta tagama.  Sai datagama sannan tajuyi gareta tai Mata sannu da zuwa. 
Haba Maryam daga magana kawai Sai ki dau fishi abunki haka akeyi najlah tafada fuska a marairaice.
Maryam: toh bakene bah inata binki kinki yarda dani bansan Kuma makikeso bah shiyasa nadan Baki space.
Toh naji komai ya shige Koh najlah tafada tana kallon Maryam don Jin abin dazata fada
Eh komai ya shige shine abunda Maryam tafada. 
Barin kawo Miki favorite dinki Koh Maryam tafada hade da kashe Mata ido daya.   Kitchen tashiga tahada Mata coffee Mai Dadi hade da kanshi takawo Mata.      Taji dadin coffee din sosai inda suka ta Hira har bayan azahar kafin tayi sallah tayi niyyar tafiya gida. Har bakin mota Maryam tarakata kafin tadawo cikin gida inda Mami take fadawa Maryam gobe abbanta zai dawo.   
Taji Dadi sosai tayi farinciki inda takira abban nata take cewa Mami tafadamun gobe zaka dawo. KASH!!! Shine abun da abban nata yafada naso nayi surprising dinki Amma Mami ta kwapsa mun Amma Kar ki damu ba shikadai bane surprise din there are many more to come kiyi fatan indawo lapiya kawai.  Amin tace sannan takashe wayan tana zumudin dawowan abban ta.

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now