part fourteen

60 1 0
                                    

A kwana a tashi asaran Mai Rai  yau gashi kusan wata uku kenan khalam nata fama da annoban cutan kaunar najlah Wanda taki bashi hadin Kai hakan har ya kai shi ga kwanciya a gadon asibiti inda yafara samun matsala a zuciyarsa.

Hajiya Amina ta yanke shawarin zuwa gidan su najlah koda babansa bai dawoba don alhaji ma"abocin tafiye tafiye nee. don bazata iya jure gani a gaban idonta dan nata yafadi ya mutu saboda soyyaya ba shiyasa ta yanke shawarin zuwa bayan khalam ya ji sauki
Yammacin yau d'akin da'a kwantar da khalam cike yake da jama'a. Maman hauwa da hauwa da nawal gaba daya suna zaune jugum jugum suna jiran farkawanshi
Jim kadan ya farfado, Bayan salatin da yayi sunan najlah yafara ambata inda hajiya ta kalli maman hauwa take cewa  kin gani koh! Kingani koh hajiya abunda nake fada miki Kenan soyayyar yarinyar nan zata haukatar mun da 'da inbanyi dagaske bah. Kuma a hakane alhaji yake ce inbari har Sai sunyi settling kafin aje nemamishi aurenta, da rabon nashi setting din Sai a kiyama nee.

Maman hauwa lallashin hajiya kawai takeyi tana cemata muyi tamasa adduah hajiya inshallah zai samu sauki
Basu ankara bah Sai jisukayi yana

Hajiya najlah! Hajiya najlah. Ina sonta ina kaunarta abun da yake iya fadi kawai kenan

Maryam nee takira Dr inda tasanar  mishi da cewa ya farka.  Atare suka shigo cikin dakin  ita da doctor.
Allurai yasake yi mishi inda yace da hajiyan khalam tasameshi a office
Kafin fitanta har yasake komawa bacci. Cike da tausayin Dan nata tatafi office din doctor inda yayi mata nuni da gurin zama tazauna.
Gyaran murya Dr luqman yayi sannan yace hajiya gaskiya babu wani cigaba damuke gani a wannan jinya kullum jikinshi 'karuwa ya keyi Wanda hakan ya ta'allaka ne dawani Abu dayasa aranshi.    Shawari na guda daya anan shine ke mahaifiyarsa nee yakamata ace kinfi kowa sanin abun dayake so da kuma akasin haka. Idan har kin San akwai abun daya nema yarasa to yakamata kuyi gaggawan bashi don yana dab da samun ciwon zuciya.
       Hajiya nee ta numfasa sannan tace inshallah Dr zanyi iya bakin kokarina inga nasama mishi abun dayake so inshallah.     Da haka ya rubuta Mata magunguna ta shige pharmacy ta saya sannan takoma dakin cike da tausayinsa aranta

Gaba daya hankalin hauwa ya tashi ganin yanayin da ya khalam yake ciki, har cikin ranta tana sonshi amma ganin hankalinsa baya kanta yasa tayi watsi da soyayyarsa dayake addabanta sannan ta dau alwashin taimaka Masa a soyyaya.
Idanunta cike da hawaye tayi dialing number Maryam tasanar da ita halin da khalam yake ciki.     Ba'a jima ba Maryam tayi tattaki takaraso asibitin inda taga kowa acikin su kaman baya hayyacinsa, sosai tausayinsu ya kamata. Ta tausayamusu sosai kafin idonta yakai ga babban abun tausayin wato khalam gaba daya ya rame yayi baki yafita hayyacinsa duk dan akan soyyaya 😣😥.
Gaishesu tayi sannan takoma da dubanta gurin hauwa tace meke damunsa haka ?
Hauwa: hmm meke damunsa inba soyayyar najlah bah
Maryam: innalillahi abun har yakai haka nee
Hauwa: gashi kuwa kina gani.
   Maryam nee ta tabe baki sannan takira najlah tace Mata kizo kelina hospital room 13 hauwa nee bataji Dadi bah batasan inda take ba ma. Tana Gama fada takashe wayanta batajira abun dazata fada bah

Bangaran najlah kuwa acikin wadan Nan lokutan ta dan fara kula khalam Amma Bata sake mishi kasancewar kowani Rana Sai ansamu coincidence din dasai sunga juna, Sai dai inbata fita daga gida bah.       'Dan kwana biyun  dabata ganshi bah har  wani iri take ji Amma taki bari yadameta saboda batason abun dazai dameta.
  Makullin motanta tadauka sannan tadauki hijabi tasanya ta nufi dakin ammi tasanar da ita Akan hauwa ba lafiya sannan ta dauki hanyar asibitin.   
      Tun kafin isarta take Jin yanayin ta ya sauya. Tarasa wani irin feeling nee yake ziyartanta, fargaba nee, tsoro nee gaba daya takasa tantancewa.
Ahaka dai da Isa dakin, jikinta ba kwari.
Ganin jama'a dayawa a dakin sannan Kuma bataga hauwa a gado bah kuma ba Maryam adakin yasa tagaida mutan dakin tasa Kai zata fita a tunanita room number ba daidai Maryam tafada mata bah.

Sunanta da aka Kira nee yasata maida hankalinta tajuya don ganin Mai kiranta. Gani tayi batasan kowa bah taya akayi suka San sunanta daga gaishesu kawai. Komawa tayi ta zauna sanna tace da hajiya na'am.  baki gane  waye a kwance acan ba Koh hajiya tafada.  Sai sannane najlah tadaga ido ta kalli Wanda yake kwance.      Zuciyarta ne yafara bugu da sauri gani datayi kaman khalam nee Amma ta dan basar sannan tace  wannan ai kaman khalm nee ko
Ehhh hajiya ta amsa mata
Allah sarki meyasa meshi haka cewar najlah
Hmm hajiya nee ta girgiza Kai alaman takaici nacin ta arai, Ashe ma yarinyar dayake hauka akanta batamasan yanayi bah.    
Ciwon zuciya nee yake damunsa hajiya tafada a takaice
Allah sarki Allah yabashi lapiya
Hajiya ta amsa da Amin
Nima nazo duba kawata nee ba lapiya inaga tayi mistake nee gurin fada mun room number barinje induba ta najlah tafada yayinda  take kokarin fita daga dakin
Girgiza Kai kawai hajiya tayi sannan tace to Allah yabata lapiya da haka tafice a dakin ranta ba Dadi ganin yanayin da khalam yake ciki.

******************************"""

Toh reader's yakuke gani zai kasance ga Najlah ga maman khalam ga Kuma khalam.
**********
Waiting for ur comment below and don't forget to *** vote***** share
Naku a kullum
****Teeete01 💞

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now