part five

95 8 4
                                    

Bayan fitanshi a gida kenan ya hadu da abokin nasa dabai taba tsammanin ganinshi ba. Karasawa gurinshi yayi Yana Mai fitowa daga motannasa. Wai nikam gizo nee kokuwa dagaske nee khalam nee agabana cewar ya ahmad(mijin aunty amrah). Ah ah ba gizo bane nine dai kake gani, Nan suka gaisa aka fara hiran yaushe gamo. Nikam ma khalam fushi nakeyi dakai
Toh nashiga magana cewar khalam, menayi Kuma ?
Haba ace aure na guda bakazo bah sannan baka kirani bah cewar ya Ahmad.
Lallai nayi laifi Ahmad kayi hakuri saif yafadamun maganan aurenka Amma lokacin ina London nee banjima da dawowa ba.
Toh naji ga gida na Nan mushiga Sai ka gaisa da amaryan tawa.
Gaban khalam ne yafadi ga Kuma bugun zuciyarsa daya karu Amma duk da haka wani sanyi yake ji aransa Jin cewa gidan dayaga Najlah tashiga Shima zai shiga.
Ahmad nee yakatse mashi tunani da cewar Bismillah shiga motan naka Sai kayi parking aciki.
Okey shine kawai abunda ya iya  fada. Bayan sunshiga sunyi parking nee suka shiga cikin gidan dauke da sallama abakinsu.
Amrah nee ta tarbi mijin nata da kuma abokin nasa cikin fara'a tana Mai bashi gurin zama. Bayan sun gaisa nee ta tashi don dauko Masa drink a kitchen.
Two musketeers( sunan da aunty amrah kefada musu kenan) haryanzu ba'a gama abincin 'yan gayun da'ace za'a yin bane gashi nayi bako. Aunty amrah yanzu za'a Gama sauran kadan cewar Maryam. Ai inafada Miki idan bakon nan yaci abincin nan Sai yamanta hulan sa saboda tsaban Dadi cewar najlah. Sukayi dariya aunty amrah tadauki drinks takaima khalam suka cigaba da hira.
Shikuwa duk damuwansa baishige ace ya ga najlah bah don yatabbata nan gidan tashiga Amma gashi Koh muryanta baijiba tunda yashigo.
Ita kuwa Maryam Tana ta addu'ar Allah yasa khalam ne yayi karfin halin shigowa gidan. Tana sanzuwa palon ta leka Amma wata zuciyar tana cemata ai hala khalam ma yayi tafiyarsa don sunjima da shigowa gidan bazai yi ta zaman jira har wannan lokacin bah. haka dai taci gaba da aikin ta Amma hankalinta na palo Banda najlah data ke tafaman aiki hankalinta kwance Bata Masan make faruwa bah.
Bayan sun Gama ne Najlah tashige toilet tawatsa ruwa kafin tafito tasanya abayanta pitch colour tadanyi simple makeup sosai tayi kyau, dama abunka da mai kyau bare ankara da kwalliya.
Kasa nutsuwa yayi yayinda yaji zuciyarshi kaman zata balle sabida tsaban bogon da takeyi a kirjinsa, yasan hakan dayake ji bazai rasa nasaba da zuwan najlah bah. Aikuwa tun bai karasa tunanin dayakeyi bah Sai gatanan  takaraso palon yayinda kanshin turaranta mai sanyaya zuciya ke tashi kadan kadan. Kanshi a kasa ya gagara dagowa saboda tsaban shauki dayake ji na ganin Najla.     
Da Zuwa palon tanima guri tazauna hade ta gaishe da bakon data gani not knowing khalam nee. Dagowan dazaiyi da niyyar amsa gaisuwan nata suka hada ido dashi, wani irin Dadi ne ya ziyarci zuciyarshi Wanda haryashiga tunanin hoping that the moment could last forever. Maryam nee ta katse Mai tunaninshi dacewar barka da Zuwa Sai sannan ne yamai da dubansa ga Maryam hade ta kashe mata ido daya sannan yace barka dai, suka gaisa, Sai sannan ne yamaida dubansa zuwa inda najlah take Amma inaaa harta tashi ta koma daki.
A ranta take ta kunkuni, tarasa meyasa duk inda zata Sai wannan mayen yabita, meyasa duk sanda take farinciki Sai yanemi spoiling mood dinta, meya kawushi gidan aunty ta kodah abokin ya Ahmad ne? Duk ita kadai take makanta wannan tambayoyin ganin bamai Bata amsa ne tadauki wayanta tabude Instagram tafara charting da hauwa har take cemata next week zata dawo 9ja.
Shigowan Maryam nee yasa ta maida dubanta ga kofa, kizo aunty amrah nakira abinda tafada kenan tafita batare da taji me najlah zatace bah.         Tafita ne dafatan cewa bakon yatafi Amma ina ko data Isa palon dashi tafara hada ido hakan yasa tayi saurin kau da kanta tana mecewa aunty amrah gani.
Haba najlah kowa nazaune a Palo Ana Hira Amma kinkoma daki kinyi zamanki gashi ko abincin 'yan gayun Baki bawa bakon nawa bah.
Ai aunty bakon kine keyakamata kiyi mishi hidima bani bah tafada tana Mai zama kusa da Maryam.
Toh ai naga kune kuka girka shiyasa Nace barin Bari kizo ki serving dinshi. Sauka tayi tajawo stool ta ijeyi kusa dashi tafara zuba Mai abinci hada da pineapple drink din dasuka hada. Tayi hakan ne don batason aunty amrah tacigaba dayi mata magana.
Shikuwa gogan idunsa nakanta hartagama ta koma gurin zamanta.  Sunkuyar da kanta kasa tayi Batason dagawo, dun duk sanda tadaga idonta Sai sun hada ido hakan yasa ta dauki wayanta taci gaba da charting da hauwa.
A hankali yake Satan kallonta Wanda harsai da ya Ahmad yafara gane wani Abu game da kallon nashi.
Sosai yaci abincin bawai don Yana jin yunwa bah saidai don yaji an ce najlah nee ta girka, yaji dadin abincin sosai.
Ya Ahmad ne yakatsemata charting tahanyar cewa Ni baza'aban abincin 'yan gayun bane Koh ni badan gayen bane? Yafada Yana fadada murmushinsa.
Ai wannan hakkin matarka ne ya Ahmad sufada suna dariya dukansu.

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now