part six

77 4 0
                                    

Sunci abinci game dayin raha sosai Wanda kowa Yana saka baki a cikin hiran da'a kiye Banda najlah da hankalinta ke kan wayanta. Sosai taso barin palon Amma aunty amrah tahanata hakan yasa tacigaba da chatting abunta.
Bayan sungama ne yayiwa aunty amrah sallama akan zaitafi hakan yasa tamai rakiya zuwa bakin kofan palon tare da mijin nata tana Mai godiya da ziyara daya kawo mata don taji dadin zuwanshi. Komawa ciki tayi tabar mijin nata tare da abokin nasa inda yake tamishi tambayoyi, iya sani na dakai bantaba ganin ka sake haka kana Hira bah, especially inda mata a gurin, ina miskilancin naka yatafi kodai akwai wani Abu akasa ne, naga harwani Satan kallon najlah kakeyi kodai kodai? Hmm.Yakarasa magana yana daga mishi gira.    Hmm Ahmad bazaka gane bane nakamu wlhy, yarinyar Nan tasa narasa nutsuwata akanta gaba daya Sai birkitamun lissafi takeyi gaba daya harnafara ramewa akanta gashi ko kirana batason gani dan tamayi blocking nambata.   Ahmad yakalleshi Yana jin  jina kai aboki Sai kayi hakuri fah don haka lamarin mata yake, kayi ta adduah Idan rabonkane Allah zai baka sannan karega saka damuwa aranka kaci gaba da trying Allah zai shige maka gaba. Ya amsa da Amin. Ance maka dama asama ake samun soyayyan bakaga irin wahalar Dana sha bane ko ance maka daga kace i love u kawai Sai acemaka i love u too nee ai inafada maka Sai ka wahala mutumina mukan munyi namu wahalar gashi hartashige yafada Yana dariya. Kai Amma Ahmad nikam bazan iya wahalar dakayi bah. Hmmmm khalam kenan Bata kamaka bane idan harda gaske kana sonta babu abunda bazakayi bah. Kuma hakane fah aboki. Su karashe magana suna dariya. Nizan shige cewar khalam. Toh nagode kagaida gida. Yauwa, am Dan Allah kacewa amarya nagode. Toh zataji muma mungode. Nan yafigi motanshi bai tsaya ako ina ba Sai gida inda ya iske hajiya a Palo tana zaune suna kallo tareda kanwan tashi nawal.
Cikin girmamawa ya rusuna ya gaida hajiyar shi ta amsa mishi cikin fara'a. Zama yayi akujeran kusa da hajiya inda kanwartashi tagaidashi amsawa yayi cikin jindadi hade da cewa takawo mishi ruwa. Hajiya ne tafara magana inda yamaida dubansa gareta. Khalam Wai meke faruwa ne kwana biyu duk naga karame kazama wani iri gaba daya kaman wani Abu nadaminka.  Kasancewar bai Saba da karya bah musamman ga iyayenshi ya amsata da eh tabbas hajiya akwai abunda yake damuna. 
Toh inbanda abunka ai zuwa zakayi kafadamun nifa mahaifiyarkace babu abunda bazan iya maka bah Sai Wanda yafi karfina. Yanzu dai ina ji fadamun meke faruwa.
Wata ajiyar zuciya ya sauke sannan yasakko daga kujeran dayake Yakoma kasa kusa da kafanta sannan yace hajiya wata yarinya nakeso Amma Sam hankalinta baya kaina gashi nikuma nagama nisa akan sonta ji nake zan iya rasa Raina idan narasata    subhanallahi yakake irin wannan maganan khalam meyakawo maganan rasa Rai kuma inshallah zaka sameta idan itace alkhairi agareka, kaci gaba da adduah kaji Amma banaso inkara Jin maganan rasa rai kaji koh! Ya amsa da toh hajiya nadaina. Sai sannan ne yafara Sosa Kai alamun Yana Jin kunya.                Banson tsiya Sai yanzu ne zakaji kunyata, nikamma dai zanso inga wata lucky girl nee haka da yarona yafada tarkon ta haka nayi nayi maganan aurenka Amma kullum Sai kace min lokaci baiyiba, Sai yanxu nee lokaci yayi Koh tafada tana murmushi irin nasu na manyan mata.  Eh hajiya Sai yanxu Allah yakawo mun Wanda nakeso Amma da kinata hadani da kannena kawai yafada Yana Mai sipping ruwan da nawal takawo mai. Kaji min yaro su zainab din nee yara ko kuwa hauwan?. Nidai yanxu tunda nasama Wanda nakeso ai shikenan  ya karasa magana acikin shagwaba. Toh Allah yasanya alkhairi hajiya tafada. Ameenn hajiyata nagode kiyita min adduah yafada Yana Mai tashi izuwa part dinshi kasancewar shi kadaine namiji agidan.
Bangaren NAJLAH kuwa Sai lokacin dayatafi ta sake tafara magana inda sukayita Hira da aunty nata da Maryam har lokacin sallah yayi, bayan sunyi sallah nee takecema aunty nata zasu tafi gida, taji dadin zuwansu sosai harbataso tafiyansu bah don sun debemata kewa.
Bayan sunshiga mota ne Maryam take cewa najlah that guy seems quite interested in u why can't you give him a chance? Ya next week hauwa zata dawo yaushe kike gani zamu fita? najlah tafada trying to avoid wancan
Maganan. We will decide idan tadawo, first answer me tafada rai adan bace. Wai Maryam meyasa kikeson damuna damaganan guy din nanne nafada Miki banaso banaso Sai yaushe Zaki gane hakan Dan Allah ki kyale ni nashakata.    Shiru Maryam tayi tana sauraronta hade da jimamin hali irin na najlah tarasa gane meyake damunta gabadaya batason kalman so a rayuwanta. Da ita khalam yace Yana so da bawani Bata lokaci zata amince don guy din burgeta yakeyi Kama daga yanayin dressing dinshi ,magananshi  harmada tafiyanshi Amma gashi Sai wahalar dakanshi yakeyi akan Wanda bata Masan me kalmar so yake nufi bah. Tun halin najlah na burgeta akan rashin kula guys har abun yafara Bata haushi gashi Kuma guys nagani a fadane ke zuwa gunta Amma ita koh ajikinta duk a zuciyarta take wannan maganan, Bata ankara bah Sai gani tayi sun karaso kofar gidan su sukayi  sallama. Kowa yakama gabanshi

Sakin Wawa🙄Where stories live. Discover now