ƘAWATA CE!
Oum-Nass
ABOTA wani haɗi ne daga Allah. Abun ƙawa da kuma dace tun daga duniya har zuwa lahira.
Abin birgewa da yiwa ado a cikin kwalliyar ko wani mutum shine Abokinsa. "Wa ye kai?" Wannan wata shuɗaɗɗiyar tambaya ce da aka daɗe da daina yinta.
A yanzu abun da mutane suke tambaya shine "Wa ye abokin ka? Wacece ƙawar ki? Domin wannan ce damar da ko wani mutum ya ke samu. Damar da ta ke sawa a gane ka, da kuma mutuntakar da ka ke da ita. Haka wata rahama ce babba da muke samu a duniya wadda zata mana rakiyar har lahirar mu.Nima nawa labarin haka ya ke? Dole kafin ka san wacece ni sai ka fara sanin ko wacece ƘAWA TAH!.
ƘAWATA CE! Ɗaya tal da muka taso a tare da ita, wadda zata bani ko wani abu da yake mallakinta, ko da ace ta kai ƙololuwa wajen soyayyarsa.
NABEEHA NAMEER, 'Ya ta uku a wajen iyayenta, haka kuma mace ɗaya tal da suka mallaka, kasancewar duka yayyenta maza ne.
Ta samu dukkanin soyayya da kulawa a wajen ahalinta, waɗanda suke kewaye da ita da kuma waɗanda suke nesa da ita.
Mai sanyin hali, mai kyakkyawan murmushi, mai ƙarancin magana, marar jure futuna.***
"Ke kam kinji daɗi Nabeeha! Ko ina kika juya a gefen ki da bayan ki, soyayya ce zallah da jin daɗi. Lokuta masu yawa mutane suna cewa mutum ba ya cika goma, ba kuma ya samun fiye da goma na jin daɗin rayuwarsa.
Amma ke kin samu fiye da ɗarin. Haƙiƙa Allah yana son ki."Idanuwanta ta lumshe ta kai kallonta kaina, a lokacin murmushin da ke kan fuskarta ya sauya, kalar idanuwanta ya canja daga farare ta ɗora su tar a kaina.
"Kema Allah yana sonki NABEELA. Ya kuma baki keɓantaccan farin cikin da iyaye masu ƙaunarki, ya haɗa ki da yayyenki da za ku zauna ku binne a tare.
Haƙiƙa duk wanda kika a duniya Allah yana sonsa, ya kuma san da zamansa. Zai iya kasancewa ya fi sonki ma fiye da ni, shi yasa ya ajiye ki a matsayin da kike kansa."Kaina na girgiza, hawayen da nake ƙoƙarin dannewa ya gangaro akan fuskata, a hankali na miƙe tsaye na tsaya a jikin windon da ke ɗakin Nabeeha, ina kallon lambunsu da yake cike da shukokin kayan marmari kala-kala, sai kuma tsuntsayen da suke kuka mai daɗin sauraro.
Iskar wajen tana kaɗawa da ƙamshin kayan itatuwan da suke hurowa zuwa ɗakin. Idona na sake lumshewa wasu hawaye ma su zafi suka sake sauƙowa akan fuskata."Duka rayuwarki cike take da sa'a Nabeeha! Bata da haɗin da za a yi kwatancenta da irin tawa rayuwar! Ina so na yi karatu a makarantar da ta fi ko wata makaranta kyau, ina so na sa kaya irin wanda ɗiyan masu kuɗi da sarakai suke sawa! Ina so duniya ta san da zamana! Ina so hotona ya cika ko wani gida, ta yanda za'a ke bada labari na!"
Juyowa na yi na harɗe hannaye na akan ƙirjina ina kallon Nabeeha, kamar yanda itama take kallona da buɗaɗɗen baki."Wannan rayuwar sam ba tawa ba ce Nabeeha! Ko kaɗan ba ta dace da zubin halitta ta ba! Ta ko wata fuska ni ke sanye da launin kayan da suke ban-bara-kwai a jikina, duk yanda na so na ƙawata su akan su yi dai-dai da halitta ta sai sun mayar da ni kamar wata mabaraciya akan titi!"
Mamakin kan fuskarta ya kasa ɓoyuwa har a lokacin, kallona ta ke tana ganinta a matsayin sabuwar halitta da ban.
****
"Ina son ka Nu'aym! Sai dai son da na ke maka bai kai koda rabin wanda nake yiwa Nabeelah ba! Ita ɗin ƘAWATA CE! Duk duniya bani da ƙawar da ta wuce ita.
Ka so ni, tare da ƙawata, idan kuma ka ƙi ƙawata hakan na nufin ni kake ƙi!" Ta ƙarasa maganar tana nuna kanta.
Hannayensa suna zube a cikin aljihun wandonsa, idanuwansa sanye da farin gilashi, tun da ta fara maganar yake murmushi har zuwa lokacin da ta gama."Bana son Nabeelah. Ke nake so Nabeeha ba ƙawarki ba! Ko kaɗan ƙawancen ku babu riba, asalima ke kike cutuwa da ƙawancenta.
Kin bata komi na rayuwarki, amma babu abu ɗaya da zaki nuna wanda ta baki! Ya kamata ki farka daga mafarkin da ki ke, ya kamata ace zuwa yanzu kin yi karatun ta nutsu.
Kin san wacece ƘAWAR KI?""Na san wacece ƙawata Nu'aym! Na fi yarda da ita fiye da ɗa namijin da bashi da tabbas.
Tun yanzu na fahimci wa ye kai? Bana buƙatar alaƙa ta ƙara haɗamu! Bana son ganin fuskarka a gabana! Ka turo a amsar ma kayan lefen da ka aiko gidan mu, da duk wani abu da ka turo na auren mu. Ba zan aure ka ba Nu'aym!"Gilashin idanuwansa ya buɗe idanuwansa a buɗe yana kallonta "Auren mu saura sati ɗaya ki ke cewa na aiko a karɓar min kayan aure na?"
"Wallahi koda ace yau ne za'a ɗaura mana aure na fasa aurenka Nu'aym! Kai ba mijin da ya dace da ni ba ne, tunda har zaka aibata ƙawa tah!"
🌷🌷🌷
Ku shirya! Ku adana sulallanku, zai zo muku a farkon 1 ga watan Nuwamba in sha Allah, akan farashi mai sauƙi 300 naira kacal.
GIRMAMAWA
YOU ARE READING
ƘAWATA CE
ActionLabari ne akan ƙawaye biyu masu halayya ɗaya! Labarin sadaukarwa a inda bata kamata ba! Ƙauna marar algus! Yarda marar iyaka! Aminci marar gudana! Tafiyar hawainiya da rikiɗewarta! Idan kun fara zaku so jin tafiyarsa. "Ita kaɗai ce ƙawar da na tas...