👩❤️💋👨 *Zab'ina*👩❤️💋👨
*ko*
💔 *na Mahaifiya ta*💔*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** **
*Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wanda akafi sani da princess*
*~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*
*Dedicated* *to* *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.**Bismillahir rahmanin rahim*
*Page 5-10*
Kallo raini Aqsa ta watsa masa tare da cewa" malam sake ni."
Had'ata yayi da jikin bangon d'akin idon sa acikin nata yace;"ina miki magana kina wani wuce wa saboda kina ga kin fi k'arfin mutane ko."
Idon ta cika yayi da hawaye dan wallahi yafara isar ta, murgud'a baki tayi tace;" matar wani fa kake sawa a jikin ka ko baka san ni mallakin wanin ka bane to in baka sani ba yau nafad'a maka ni mallakin Asad ne kuma wallahi in Asad ya gane abunda kake min zai nuna maka kuskuren ka.....bud'e baki tayi zata yi magana ji tayi ya had'a bakin shi da nata bak'in ciki yasa hawayen idon ta gangaro wa dakyar ta ture shi tare da cewa Allah ya isa na mugu kawai d'an iska.. da gudu ta shiga d'aki bata tsaya ko ina ba sai toilet tafara brush tana kuka.....
Koda ta shiga d'aki dariya yayi yace;" yarinya kenan in kinga baki aure ni ba to Inna talatu ce tabar doron k'asa kuma ko ba ita ina da k'arfin da zan mallake ki kwanciya yayi akan kujera ya lumshe ido.
Umma kan tana zaune da autan ta a d'aki wai suna hira shigowa da gudu Aqsa tayi tana kuka hankalin Umma tashi yayi ganin yadda Aqsan nata ke kuka jaan ta jikin ta tayi tana rarrashin ta tare da tambayar abunda yafaru...
Har zata fad'a sai kuma ta tuna yanzu in tafad'a ran Umman ta zai b'aci kuma in tayi magana inna talatu zata fara masifar ta tana zagin Umman dariya ta kwashe da wanda hakan tayi shi iya fuska ne san nan tace;" Umma abu ne yafada'a ido na nayi nayi yafita yak'i shine nake kuka fa."
Tsaki Umma tayi dan abun yabata haushi mai da hankalin ta gun Aayan tayi suka ci gaba da hiran su ita kuma ta tashi ta koma d'aki tajima tana kuka sai da taji shigowar motar Asad kafin ta tashi ta shiga wanka.
A parlour Asad ya tadda Sahib gaisawa sukayi kafin ya tambaye shi ko Aqsa ta dawo gida, cewa;" yayi bai sani ba dai dai lokacin ta fito murmushi tayi tace;" meyasa sai ka tambaya bayan kasan bana fita sai na tambaye ka k'ara sa wa gurin tayi ta ajiye masa ruwan sanyi ita ma ta zauna hira suke tama manta da Sahib na parlour ransa b'aci yayi jin yadda suke nuna wa juna so tashi yayi yafita daga gidan ba tare da ya kula kowa ba, sai da Aqsa ta tabbatar da fitan Sahib takarai raya murya tasa fuskar tausayi tace;" baby wallahi aure bakeso dan Allah kayi magana asa mana rana Umma tajima da shirya wa ku take jira."
Kallon ta yayi yace;" aure kike so kika ce yau 🤔🤔anya kece kodai.....
Murgud'a baki tayi tace;" malam nidai na fad'a maka abunda nakeso kuma amin dariya ta bashi amma yana yi zatayi fushi haka ya had'iye dariyar ya yadda gobe da yamma zaa zo sa musu rana dad'i taji sosai dan wallahi ta gaji da Sahib da tana bashi respect amma tunda ya koyi tab'a jikin ta tafara tsanar sa , haka dai tasa Asad yatafi gida da wuri yau wai yaje ya sanar wa Mama da wuri kar ya koma late yasamu tayi bacci d'aki ta shiga tafara rawa Umma na tsaye tana kallon ta har zata mata magana sai kuma tafasa ta koma d'aki.
Har tafara bacci sai taji Aqsa na tashin ta tashi tayi tace;" fad'i damuwar ki kai ta sun kuyar san nan tace;" Zainab ce takira wai gobe zaa zo sa ranar bikin mu da Asad wani farin ciki mara misaltuwa Umma taji hamdala tayi tare da sujjadar shukur ta gode wa ubangiji ta kuma rok'i Allah yasa ayi da ita daga nan suka fara hira a nan Aqsa tayi bacci wayar ta na d'aki Asad ko sai k'ira yake bata d'aga wa ransa b'aci yayi sai yayi kamar yayi fushi sai kuma ya k'ara k'ira haka dai yayi bacci batare da yaji muryar ta ba."
Washa gari da yamma magabatan Asad suka zo aka sa musu rana wata biyu Alhj Abdullahi wato baban Sahib ne ya zauna da manyan Asad d'in sunyi taro sun tashi lafiya koda a ka koma aka fad'a wa Asad cewa yayi wata biyu yayi nisa aiko Mama tafara yau taji ikon Allah yaran zamani basu da kunya wai Asad ya dubi idon ta yace wata biyu sunyi masa nisa Zainab dai dariya Asad da Mama suke bata in suka fara fad'an su..
Wai waye..
Asalin Aqsa, maihaifin Aqsa Alhaji Yusuf d'anbalago d'an kasuwa ne yaje cin kasuwan cin sa a kano cikin bici ya had'u da Hajiya Hauwa wato Umma da kyar mahaifiyar sa Inna Talatu ta yadda da auren saboda Hauwa yer talakawa ne ita kuma ya'yan ta suna da kud'i kamar baza ayi ba dai dake Allah yayi matar sa ce aka d'aura aure lafiya sun d'au gurin shekara biyar kafin Allah ya basu haihuwa 'ya mace suka sa mata Nusaiba daga nan suka sake jimawa kafin su sami Aqsa bayan Aqsa kuwa sai da suka d'ibi shekara ashirin aka samu cikin Aayan haka Laraba matar Alhaji Abdullahi da Inna Talatu suka had'a kai suka je gurin malami daga nan kullum mahaifiyar su Aqsa ba lafiya ciki kuwa sai da ya shekara hud'u a jikin ta kafin ta haife shi dake Allah yayi zaizo duniya."
Bayan shekara da haihuwar Aayan akayi auren Nusaiba bayan auren da sati satiAllah ya Karb'i ran mahaifin su daga nan Inna Talatu ta takura musu hakan yasa lokacin da Sahib ya dawo daga England Inna Talatu tace sai dai ya zauna a gidan dan tana sanin abunda suke aika tawa a cikin gidan haka ko akayi.
Tun ranar da Sahib yafara ganin Aqsa yaji ba macen da yake sha'awa sai ita dama a England yasa ba har kar mata ganin ya kasa samun fuska a gun Aqsa yasa yafara kai hanu jikin ta amma kullum zagin sa take tun bata raina shi ba yanzu ta raina shi yasan tana da saurayi amma baisan har shirin aure suke ba saboda baya shiga sabgar da batashi ba.
Tunda ga randa aka sa musu rana kullum sai Mama ta had'a Aqsa da Asad ta musu fad'a su sani zaman aure ba kamar soyayyar waje bane akwana a tashi yau saura sati biyu bikin koda Aqsa taje gurin Mama k'arfe hud'u nayi Asad ya kaita family House d'insu dan yau tana da meeting,
Tunda ta shiga gidan Inna Talatu take kallon yadda Sahib yake kallon ta har ta isa gefen Aayan da Nusaiba ta zauna cikin nutsuwa kanta a k'asa dan tasan Inna Talatu zata zage ta kamar kullun in ma bata zage taba Laraba step mom d'in Sahib zata zage ta haka a kafara meeting wanda a k'arshe Alhaji Abdullahi yasanar da auren Aqsa,
Alhaji Abdullahi na rufe baki Sahib yashiga d'aki yana huci kamar zaki wai kishi yake aiko Inna Talatu da Laraba suka bishi danjin abunda ke damun sa hawaye yafara tare da kwantar dakai a k'afar Inna Talatu wai shi Aqsa yakeso kuma zai iya mutuwa a kanta daga jin haka hankalin su ya tashi suka shiga rarrashin sa, wanda a ciki Inna Talatu tace;" d'an gwal in kaga baka auri Aqsa ba to nice nabar duniya hakan yayi bala'in kwantar masa da hankali dan yasan yadda suke sanshi, ya goge hawaye ya d'ebi kai ya jaririn jaki ya fito lokacin kuwa kowa ya watse a gurin meeting d'in,
Mota yashiga ya tafi, inna Talatu kuma da Laraba suka fara zaman tunanin yadda zasu fitowa al-amarin.
Gida Anty Nusaiba da Aqsa suka koma a parlour suka samu Umma zaune da kayan yara wai tana dubawa Aayan kayan da zaisa a gurin auren.....
Next page....
