zabina ko na mahaifiyata

40 0 0
                                    

👩‍❤️‍💋‍👨 *Zab'ina*👩‍❤️‍💋‍👨
                   *ko*
                        💔 *na Mahaifiya ta*💔

*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** **

      *Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wanda akafi sani da princess*

       *~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*

*Dedicated* *to*  *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*

  
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

          

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu'ar Wanda Ya ji Tsoron Faruwar Wani Abu Mummuna saboda Kambun Baka*

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya ga wani abu da ya kayatar da shi ga dan uwansa, ko ga kansa, ko ga dukiyarsa, to ya roki Allah ya sanya albarka gare shi; domin kambun baka gaskiya ne.

*Bismillahir rahmanin rahim*

     *Page 25~30*


      Ganin yadda bata d'aga wayar tasa hankalin sa tashi yayi sosai dan ko abinci bai iya ci ba Key ya d'auka da niyar zuwa gidan su Aqsa,

    Zainab na masa magana amma ko jinta baiyi ba bare ya tsaya sauraron ta,

     Mama kan tab'e baki tayi ganin yadda yafita kamar wani wanda ya zauce.

    *********************************

       Koda suka shigo parlour da sauri Umma ta taso dan ta rik'e ta taji d'umin jikin ta amma kuma abun mamakin shine yau ko da Umma tazo kusa da ita Aqsa ta juya hanya batare da tace komai ba ta shiga d'aki ta rufe,

      Haka Nusaiba da Ahlum d'in ma suka bita a baya, bak'in ciki Umma taji sosai dan tasan Aqsa tana buk'atan ta da kulawar ta a wan nan lokacin amma kuma bata san abunda zai shiga tsakanin Alhaji Abdullahi da mahaifiyar shi dan Inna ta kware gurin fad'an rashin gaskiya zama tayi tana ruwan kwalla ji tayi hanu na goge mata hawayen bud'e ido tayi Aayan ta gani yana murmushi yace " Umma ta idon ki yana kuka."

      Murmushi tayi cikin k'arfin hali tace"Aayan abune yashiga idona kuma ma yafita kagani ta gwalo masa ido.

     Murmushi yayi sai ya tashi da gudu ita Umman tashi tayi ta nufi d'aki.

    Tana shiga d'akin toilet ta nufa ta tsarkake jikin ta tafito tasa kaya tare da feshe jikin ta da turare masu dad'i kafin tayi duk wani sallar da ake binta, bayan ta idar ta hau gado takwan ta kanta kuma ta d'aura a k'afar Anty Nusaiba bacci yafara d'aukan ta

      Tana fara baccin tayi mafarkin Asad yayi hatsari a firgice ta farka tana k'iran sunan sa rik'e ta Nusaiba da Ahlum sukayi dan shirin fita da gudu take da kyar suka sami kan ta , waya Ahlum ta d'auka ta k'ira Asad d'in sanar dashi halin da Aqsan take ciki tayi yace tabawa Aqsan zai mata magana ta mik'a mata cikin rawar jiki ta k'arba tare da cewa" hello mine."

Zabina ko na mahaifiyataWhere stories live. Discover now