[10/18, 2:48 PM] Princess👸🏻👸🏻: 👩❤️💋👨 *Zab'ina*👩❤️💋👨
*ko*
💔 *na Mahaifiya ta Sabuwar Rayuwa*💔*ciga bane*
*** *** *** *** *** *** *** *** *** *** ******Daga alkalamin🖊️🖊️ Habiba Ahmad wanda akafi sani da princess*
*~kirkirarren labari ne kuma bashi da tsayi~*
*Dedicated* *to* *sis Khareema ~(my dangin kuma tu~*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*🖊
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ 🖊 *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*Bismillahir rahmanin rahim*
*Page 85~90*
Cewa yayi sorry tare da fita daga d'akin dafe kai ta yi tace" ya ganni.
Abun ya bashi mamaki sosai ganin ta a d'akin k'iran Zahra yayi dan yaji daga gare ta.
Jin yadda ta amsa masa da Khareema ce matar sa yaji yana mamaki, wani dad'i yaji a k'asan zuciyar sa wanda bai san dalilin sa ba, Zahra kuwa ta koma parlour dan dama Mummy ta kira ta.
Tana zuwa parlour Mummy tace ta fad'a wa Khareema ta shirya zasu fita shopping, wasu abubuwan da take buk'ata zuwa k'arshen sati ta koma gidan ta cikin ladabi, Zahran ta tashi ta nufi d'akin Khareema, a zaune ta same ta riga da wando tasa da Zahra ta fad'a mata zasu fita sai ta d'aura black d'in kimono da black veil,
Tare da Zahra suka isa parlour sai da ta gaishe da mummy kafin tace" mun shirya d'ago ido Mummyn tayi tare da cewa kin tambayi mijin ki?
Kai a k'asa tace " mummy ban ganshi ba ni ban ma sanshi ba.
Cikin mamaki mummy tace"jiya ku kwana d'aki d'aya amma till now baki san mijin ki ba to kije teras zaki same shi ki tambaye sai kizo ku tafi zan bawa Zahra aikan.
Hanya ta kama tana tafiya a ranta kuwa tunanin mijin da zata gani take.
Tana shiga teras d'in taga Don zaro ido tayi tace billu a ranta.
Juya tayi ba tare da ta tambaye shi ba da ta dawo tace wa mummy ai ta tambaye shi, ita kuma tabar shi suka tafi.
Bayan wasu lokuta kuwa Don ya sakko yana tambaya ina Zahra nan mum tafad'a masa tare suka fita da Kharerma cikin mamaki yace ina suka je?
Ita ma tambaya ta mayar mar da lokacin da taje tambayar ka zata fita bata fad'a maka inda zata je bane?
Mamaki tambayar ta bashi dan rabon sa da ita tunda ya barta a d'aki tana sa kaya murmushi yayi yace "kawai cewa tayi zata fita I thought ma bata fitan ba.
A ransa kuwa cewa yayi lalle khareema zata dawo zanyi maganin ta.
**** **** *** **** **** **** **** **** **** **Hmmmm rayuwa fa ta sanja Inna da Laraba basu da abokan fad'a hakan yasa suka dawo fad'a da junan su rigimar yau daban ta gobe daban har suka jawo wa Alhaji Abdullahi ciwon zuciya amma hakan bai sa sun koma hankalin su ba,
Sati biyu ya k'ara Allah ya masa cika wa,amma hakan baisa sun nutsu ba sai kuma suka koma fad'a kan dukiya.
Sahib kuwa bama sa ganin sa bare yasan me sukeyi.
**** **** ***** ***** **×****×****× *****× *
Tunda su Umma suka tafi baa sake jin d'uriyar su ba kamar ma baa tab'a halittar su ba.
**** ***** ***** ***** **** ***** ****** ***** ***
Yana zaune a parlour da Mummy suna hira sai ga su Zahra sun dawo tunda yaga kayan jikin Khareema yaji ransa ya b'aci saboda yadda ta d'aura belt d'in kimonom yasa shape d'in jikin ta fitowa sosai.
Mai da kansa yayi k'asa yana kallon k'afar sa har suka ajiye kayan kafin mummy tace" kekuma da kika je tambayar sa sai baki fad'a masa ina zakuje ba sun kuyar da kai tayi saboda tasan k'arya tayi kuma ya kamata Allah ne kawai yasan irin fad'an da zaiyi yanzu.
Ba k'arfi ajikin ta tabud'e leda zata fara cire kayan ciki mummy tace"aa kinga duk abunda kika siya ai kinaso ne meyasa sai kin nuna min shi Zahra taya ta kukai d'aki.
Har suka d'ebi kayan jikin ta ba k'arfi suna shiga d'aki kuwa tace " Zahra nayi k'arya wa billu 😢
Ido Zahra ta bud'e tare da cewa kinsan ba abunda ya tsana irin k'arya kuwa meyasa kika yi?
Idon ta cike da hawaye tace" dana je sai nakasa k'arasa wa gurin sa bare na tambaye shi shine na dawo muka tafi.
Sai lokacin Zahra ta tuna tunda suka shigo kansa a k'asa yake bai d'aga ba.
A jiyar zuci tayi tace" to bari kiji de yanzu in ya shigo yana fad'a karki ce komai har ya gama sai ya sakko zuwa anjima sai ki bashi hakuri,amma ki daure karki tanka shi in yana magana please.
Tashi Zahra tayi har zata fita sai ta kuma cewa am sure shigar da kika fita dashi ma baya so sai yasa ya sunkuyar da kai ya b'ata rai yana da kishi sosai ban miki magana ba saboda kince kin tambaye shi I thought ya ganki da kayan kuma ya barki.
K'ara tsorata ta jin hakan kallo kawai tabi Zahra dashi har ta fita.
Dan tsoro kasa cire kayan ledan tayi tana tunanin abunda zaiyi.
Tana cikin tunanin nan taji sallamar sa kasa amsawa tayi ta juya tana kallon jikin gado.
Zama yayi ba tare da yace mata komai ba, har aka k'ira magrib ba wanda ya iya magana a d'akin tashima yayi yafita.
Rashin kulatan da yayi ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba da kyar ta iya tashi tayi sallarma dan zuciyar ta cike take da tunani.
Har su daddy suka dawo akayi sallah har a ka zauna a dining table Khareema bata fito ba daddy tunda ya dawo yake tambayar ta amma ko da Zahra taje duba ta samu tayi, tayi bacci abun yaba su mamaki yau Khareema ce tayi bacci bayan isha.
Har suka shiga bacci bata fito ba.
Yau tsawon kwana uku baya kulata abun fara damun ta yayi ta yanke wakan ta shawara zata je ta same shi