Tallah

535 18 1
                                    

Bambancin Halitta part 2

Duniya suna ta tara, ta Aljanu ko ta mutane wacce zasu zaɓa ta zama abun morewa a gare su? Sun yi rayuwa a tasu duniyar da suke jin babu kamarta a kowanne fanni amman yanzu da suka tsinci kansu a wata duniyar da ta zamo sabuwa garesu ta abubuwan da suka saci kamanninsu sai suka ga wata alfarmace ta musamman ta samesu..babban abin da ya fi ɗaukar hankalinsu bai wuce yadda suke ganin nama ko ina yana yawo ba, dan har wani ƙamshi-ƙamshi na musamman naman jikin mutane ya ke musu a hanci. Fatansu bai wuce yadda zasu cisu ɗanyu ba sannan su gasasu da kayan ɗanɗanon da suka ga suna amfani dasu wurin girki. Abun takaicin kuma bai wuce na yadda akai masu katanga ga cutar dasu ba har na tsawon wasu shekaru na gaba masu zuwa waɗan da suke da tsaiko a duniyarda suka faɗo a lokacin da suka gama aikinsu a wani wuri da Dondura suka kira Maƙabarta da su basu santa ba. Ban da ma maƙabarta abubuwa da dama basu sansu ba, dan haka ne suka yanke shawarar bibiyar mutane saƙo da lungu suna rayuwa dasu suna fahimtar kalar rayuwarsu. A cikin shekarun nan suka fahimci duk wani abu da ya kamata su sani su iya kuma sun iya ɗin ƙwarai.

Farfar babu abin da ya fi burgeta irin ta shahara dai ko a nan duniyar ta rayu cikin fitattu. Ta kuma samu abin da ta ke so duba da irin kyawunta da ta bayyana a cikinshi ta yadda kamannin kyanko kamar yadda ta ke da zaɓin canza sura sau ɗaya a rayuwa, lokaci kawai ta ke jira ta fara slaying ɗinta sai dai bata da tabbacin zamansu a nan idan sun gana da Dondura sai dai idan bayan buƙatarsu ta biya dole zata dawo ta yi slaying.
*************

Ta ina zai fara tsigeta a cikin rayuwarshi? Ta ya zai saka ta yi nesa da shi da duk wani abu da ya shafe shi? Nacin ta ya na mashi yawa har ya na neman zame mashi wani abu a ɓangaren rayuwarshi. Ƙwarai ya na buƙatarta amman kuma baya son ta kusa da shi.....

Ya ɗakko plate ya aje, Ya ɗaura wuƙa da cokula a sama. Ya dakko lemo mai sanyi ya aje sannan ya koma ya zauna..idan guguwar rashin hankalinta ta kawo ta gidan nan a yau, zai tabbatar ya ci abincin rana da naman jikinta...!

*********

A cikin duhun daren da kowanne ruhi ke hutawa, a can cikin tsohuwa kuma dad'addar mak'abarta da ta kwashe shekaru ba tare da an waiwayeta ba. Wani kalar shiru ne da babu ko kukan k'wari a cikin shi, haka babu alamun hasken da ya wuce na jinjirin wata.

Suna tsaye a tsakiyar mak'abartar a saman wani tudu da ba zasu kira shi kabari ba, saboda fad'in da yai ya kuma baje a k'asan.

Mama maima da ke tsaye kusa da Farfar kawunan su ne kawai suka bultso na macizai sauran jikin na mutane, ta yanki hannunta ta d'aga sama jinin na kwarara a wani kabari da ke k'asan tudun da suke. Bayan wani lokaci jinin ya tsaya sannan kabarin ya wage wani tandareren kai mai fad'i da gashin kanshi yai cirko cirko a sama ya b'ullo ya na lilo a sama sannan jini na kwarara ta idanuwanshi suna zubar da basa sauka k'asa..ba a ɗau lokaci ba gangar jikin da babu ƙafafuwa kuma babu hannu ɗaya ta kuma ɓullowa daga cikin kabarin sannan ta haɗe da kan da ke lilo a sama. Hannu ɗaya dake liƙe da jikin ya taɓa kan da ya juyo ya juyo da shi ya gyara zamanshi a jikin....

Me kuke jira? ku hanzarto a yi tafiyar daku. Labari mai cike da Soyayya, cin amana tare da sadaukarwa. Labarin da ya haɗa duniyoyi biyu tare da mabanbanta halittu ya bada labari mai ƙayatarwa. Ki sayi part 2, ki karanta part 1 free. Cancaɗi! #200 kacal

Account details

0035895672 stanbinc bank
Rabi'atu Abubakar umar.

Whats'app number domin tura shaidar biya.

08104652213

Ga waɗanda ba su da Account ma zasu iya tura recharge card na Mtn a Number ta sama.

Na gode🙏🥰🥰

#Pinky🦋

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now