12

653 104 7
                                    



Tarin baƙin ciki,da nadamar yaddar da yaima Alh sukai tarar mashi a lokaci guda, ga matar shi da yake sonta iyakar iyawar shi tazo mashi da wani abu da bai san da zaman shi ba. Babban bakin cikin shi yadda yake ganin tsana kwance a idon lan uwanshi. Kusan sati yayi bai lafiya baya fita ko ina. To ya fita ma yaje ina? Bayan yanzu bashi da komai. A sarar da yaja masu ko ance ya ɗauki sauran kayan shagon ma bazai iya ba.

Inna ce kawai ta fahimce shi takuma basho ƙwarin gwuiwa, dan babu yadda batai da salisu ya tsaya suyi maganar fahimta ba amma yaƙi yadda, ya riga ya shaidi sa'eed a matsayin makaryaci, maha'in ci. Tunda gashi har matar shi da ɗan uwanta bai bari ba. Yaɗau zafin kiyayya sosai ya lafta wa sa'eed, daman ga zafin rashin samun aikin da baiyi ba sai abun ya haɗe mashi. Yanzu in ya bar gidan ma sai yafi wata bai dawo ba. Dan har inna fushi yake da ita, akan tana goyon bayan sa'eed.

Inna da taga abun nashi bana ƙarau bane ta matsa mashi da maganar aure. Daman ya na da wadda yake so tun makarantar su amma ita degree ta ke aji biyu. Ya matsa akai auren bayan alkawarin zai barta ta cigaba.

Nudhar kuma baban ta ke kula da komanta,duk da inna ta buƙaci su dawo gida amma ya nuna bayasan ɗaura mata nauyin su tunda yanzu ba wani abu yake dashi ba. Buga buga kawai yake dakyar yana samun kuɗin shi, sannu sannu ya ɗan tara ya buɗe ƙaramin shago cikin unguwa.

Rayuwa taci gaba da tafiyar musu,yau daɗi gobe da sauƙi. Har nudhar ta shekara shidda. A lokacin kuma bata da magana sai na maman ta. Kullumta ishi babanta ya kaita taga maman ta,saboda ƙawayenta suna labarin maman su a makara ita kuma bata da.

Kullum inna ta na faɗin,ya kaita ta ganta ko yaya ne tunda lokaci yaja wata kila sun gane gaskiya. Sai ya yanke shawarar zai fara zuwa yalleman ɗin kafin ya kai Nudhar.

Rashin mutunci yasha kwando kwando a yalleman, ya dawo ba tare da ya ga Surayya ba. Da ɗinbin baƙin ciki da nadamar zuwa ya dawo ringim.
Nudhar na ƙofar gidan inna tana jiran shi,dan inna ta faɗa mata zaije ya dawo akaita wurin mamanta. Tun da ta hangoshi daga nesa ta fallo da gudu wurin shi. Amma sai ji tayi an ɗauke ta ɗaf sama yayin da idon ta dusu dusu ya ke hango Babanta kwance cikin jini ga motar da ta buge shi nan ta tsaya.

Wani irin ihu ta fasa tana zillewa daga ruƙon mutumen da yai mata. Haka aka kwashe shi sai asibiti. Yasha jinyar kusan sati kafin ya fara dawowa dai dai. Ya faɗawa inna yadda sukai a yalleman yakuma roƙeta da karta kai mashi Nudhar wurin su ta wulaƙanta har lokacin da Allah zai bayyana gaskiyar koman daɗewa. A ranar Allah ya ɗauki ran Sa'eed.

Kukan Nudhar na yau daban na gobe daban, salisu ko ba waiwayar su yake ba. Tunda yai aure ya ƙara canza halaye ya koma wani salisun daban da wanda aka sani ,a fagen rashin mutumci da rashin kyautatawa koma waye,yayi zarra. Dayaji labarin mutuwar Sa'eed ma sai yace hakkin shine ya bishi, ya kara nesanta kanshi da gidan inna karma ace ya ɗauki Nudhar. Dan haka inna ta saka mashi ido kawai,dan dama tana da yar sana'ar ta. Da ita suke ci tana ma Nudhar buƙatun makaranta.

Nudhar na da shekara sha bakwai inna ta fara ciwoce ciwoce,kullum jikin babu daɗi. A lokacin ta na aji shidda a secondary saboda tsallaken aji ɗayan da akai mata.

Kullum damuwar inna bai wuce na yadda rayuwar Nudhar zata cigaba ba bayan ranta. Allah ya gani tayi iyakar ƙoƙarinta wurin ganin ta haɗata da kawunta salisu amma fir yaƙi yadda. Dadai taga Ko yaushe tana iya amsa kiran mahalicci ta tusa salisu gaba da faɗa. Tace mashi dole ne bayan ranta ya riƙe Nudhar har auren ta. Inya sake ya koreta daga rayuwar shi bata yafe mashi ba. Jinta kawai yake batare da ya saka abin arai ba dukda baiji daɗin furucin ba.

Da maganar su ba ayi sati ba ciwo ya rikice bata iya yiwa kanta komai, Nudhar ke mata duk abinda take buƙata. A haka Allah ya kaɗo salisu gidan ya firgita da yanayin da ya ganta, ya kaita asibiti.cikin dai wannan jiyyar rai yayi halin shi bayan ta jadda da mashi Ruƙon Nudhar har ya auradda ita tare da karatun ta karya tsaida. A gaban Nudhar ɗin da take ta faman zubar da hawaye.

NOORUN NISADonde viven las historias. Descúbrelo ahora