24

592 83 3
                                    





Tun da ya shigo ya fahimci ta zo, a yadda ya ga an gyare ko ina, takardun da ke babbaje ma ta jerasu tsab wuri ɗaya. office ɗin shi na ciki ne dai ya ga bata shiga ba yai guntun murmushi.

"Hakan bai hana in hukunta ki"

Ya samu wurin ya zauna, kaɗan kaɗan ya ke duba agogo ya na tsumayin fitowarta dan ya san ta na kitchen amma ya ji shiru.

Window din dake tsakanin su ta office ɗinta ya zuge ya ga bata nan, to ina ta je? Kaddai ace wani ya shigo mashi office. Amma in wani ne ai ba zai gyara ba za a harmutsa shi ne.

Ganin duk hasashen ya ƙi kaishi ya sa ya nufi kitchen ɗin sai ya jiyo motsi, ya koma ya laɓe ya na leƙawa. Hango ta yayi ta na ɗakko cup yai ajiyar zuciya, ya na ganin ta juyo yai saurin komawa da sauri ya je ya zauna ya na haɗe rai.

Gabanta ya faɗi ganin shi zaune, sai take jin kamar yaune rana ta farko da ta fara ganinshi tana jin duk ya cika mata wurin. A harɗe ta iso ta aje tray ɗin hannunta har wata zufa yake.

"Good morning"

Ta ce ta na kallonshi ta wutsiyar ldo.

"Waya ba ki sallamar barin clinic ?" Ya faɗi ya na tsare ta da ido.

"Na'am?"

"Eh" ya ansa.

Ta ƙasa sadda kai ta na kama ƙasan hijan ɗinta ta na nannaɗewa da yatsa.

"Don't make me to repeat my self.."

"Uhmm..uhmm kayi haƙuri"

Ya buga table ɗin gabanshi da ƙarfi har tray ɗin na faɗuwa flaks ɗin ya faɗo ƙasa coffen ya watse.

"Are you dumb?" Ya faɗi ya na miƙewa tsaye.

"Wayyo!" Ta ce ta na matsawa nesa da wurin.

"Na warke ne shine na tafi..kayi haƙuri wallahi ban ƙarawa"

"Ohh! Idan muyum ya warke sai ya sallami kanshi kenan ta hanyar guduwa?"

"Allah wallahi ba guduwa nayi ba. Tafiya nayi"

"Interesting!"

Ya tafa hannuwanshi.

"A gaban wa ki ka fita to?"

"Ba kowa"

"Au hoo, shine ki ke faɗin ba guduwa ki kai ba?"

Ya faɗi ya na tahowa, da gudu ta ƙara rugawa bakin ƙofa.

"Guduwa nayi. Allah ban ƙarawa amma"

"In kika ƙara motsi ɗaya sai na tabbatar kinyi nadama"

Ya ce ya na jingina jikin table ɗin bayan ya zagayo.

"Miye dalilin guduwan, ko kinga abun tsoro ne a nan?"

Ta girgiza kai. Ya yunƙuro kamar zai ta ho, tai saurin faɗin

"Babu abin da na gani, ji nayi na samu ƙarfi"

"Da kyau!" Ya faɗi ya na gyaɗa kai da murmushin da ta kasa fahimtar ko na miye.

"Zo gyara wurin nan" ya nuna inda coffeen ya zube da ido.

"To" ta ce amma bata ko motsa ba.

"Kin ji abin da na faɗa"

"Eh, to ka koma ka zauna"

Ya kauda kanshi gefe gudun ta ga dariyar da ke son kwace mashi ta raina shi. Komawa yai ya zauna ya kallo ta zo ta kwashe ta maida kitchen sannan ta zo ta share wurin.

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now