Kawu ne riƙe da waya a hannu mami na karanto mashi number da aka anso ya na sakawa a wayarshi kafin ya danna mata kira.
"Assalamu'alaikum" a ka faɗi bayan ɗaga kiran.
Mami tai saurin matsowa ta na mashi nuni da ya buɗe muryar wayar ta riƙa ji.
"Kawu ne" ya faɗi ya na sauraren jim ɗin da tayi kafin gaidashi. Ya amsa ya na ɗaurawa da faɗin
"Ke shikenan ko ƴar waya babu, ba zagayowa gida?"
Bai jira ta ce komai ba ya cigaba da cewa
"Komai ki ke gobe ki ajiyeshi ki zo gida..a goben da safe, ki na ji na"
"Eh" ta amsa mamaki na cinyeta.
"Yauwa Allah na"
Kawu ya faɗi ya na ajiyar zuciya bayan ya aje wayar.
A jiya su Alh kabir sukai mashi dirar mikiya bayan shaidun da suka samu na rashin kulawar da ya ke da ita ga ƴan unguwa, dan duk wandan da za a tambaya game da zamanta gidan suna faɗin wani lokaci su na ganin ta wani lokaci a'a har aka samu wanda ya faɗa masu korartan da ya so shi a wasu shekarun baya. Hakan ya ɓata masu rai su ka isa gidan kawu basu ko gaisa ba su ka titsiyeshi akan lallai sai ya fito masu ƴarsu. Duk munafincin su dai aranar kaca kaca akai masu shida mamin kafin su bashi damar kwana ɗaya ko su haɗa shi da hukuma. Daga nan basu zauna ba su ka cigaba da neman nata kafin goben su dawo ayi mai yiwuwa.
Bayan fitarsu ne Hasinah ke faɗa masu zasu iya anso Number ƙawar Nudhar ɗin agun ƴar uwarta da ke nan unguwar tasu. Sai da mami ta hanɓarata da ƙafa dan takaicin tun-tuni ba ta faɗa masu ba sai da aka ƙare masu cin mutunci.
Da hakan ne har Allah ya taimakesu su ka samu Number Nudhar ɗin. Yau ko ba komai zai yi bacci a nutse.
•••
Bayan Nudhar ta aje kiran, Amrah ta kira ta shaida mata yadda sukai da kawu. Ita ma tai mamaki sannan ta ce to ta samu Daada ta faɗa mata, in ya so goben sai su je.Linke kafet ɗin da ta gama sallah ta yi, ta fita parlourn. Baffa da Zaid kawai ta iske su na maganganun su na Company
"Sannu da aiki Baffa"
Ta ce mashi ta na ɗan russunawa.
"Yauwa Nudhar, babu dai wata matsala ko?"
"Eh, daman dai kawu ne ya kira ni yanzun. Ya ce wai inje gida a gobe"
"Toofa" ya faɗi tun da yanzu ya san labarin Nudhar ɗin.
"To Allah ya kaimu goben lafiya"
"Ameen" ta ansa sannan ta koma ɗaki.
••
Washe gari da safe ma haka ta shiga kitchen, sai dai ta iske Zuhra ciki dan wasu lokutta ta kan shigo tai wa Daada girki tun daga na safe har dare, Wani lokacin kuma Azima. In basu samu shigowa ba ta yi abin ta.Tare sukai aikin da Zuhra su ka gama, a parlour ta iske Zaid ba ta ga alamar ko wanka yayi ba ma balle ya shirya fita Office. Dan jallabiya ce a jikinshi. Tadai a je mashi break ɗin bayan ta gaidashi, shi kuma yai mata godiya ta wuce ba tare da ta ansa shi ba.
Wurin sha ɗaya da rabi ta gama shiryawa Amrah ta shigo su ka fito. A nan ta shirya barin su Faara dan daman tun da tai masu wanka su ka fita da Zuhra.
"Kun shirya" Daada ta faɗi.
Su ka amsa Da "Eh"
"Zaid ka tashi ka kai su to"
Kamar jira ya ke ya miƙe kuwa, ba ta san ma sadda ya je har ya shirya ba tunda ta barshi ya na break ɗazu. Ta harare shi, shi kuma ya kashe mata ido ɗaya. Ta yi gaba ta ƙyaleshi.
YOU ARE READING
NOORUN NISA
General Fictionƙaddara mai ƙarfi ta haɗa su biyun ba tare da sanin ɗayan su ba. a lokacin da wata ƙadarar ta kawo su ga juna sai suka zama tamkar suna ganin hanjin junan su ne saboda ƙiyayyar da sukewa juna. amma kowannen su ya na mamakin yadda yake jin kaddarar...