13

747 87 7
                                    

Alhaji hayat Qaseem Dando haifaffen garin Dutse a jihar jigawa. Alh hayat Dando ,babban ɗan kasuwa ne kuma ɗan boko da yai suna ciki da wajen jigawa harma da wasu ƙasashen ƙetare saboda shige-shigen shi na kasuwanci da hannu jari a ɓangarori da dama.

Ya kasance ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifan shi, shi kaɗai ya tashi a gaban su kafin mahaifiyarshi ta rasu. Dan haka duk wani rainon shi da wahalarshi baban shine sun sha wahala matuƙa, hakan yasa shi dagewa da neman nakan shi da kuma ilimi saboda baban shi ya ji daɗi.

Tunda arzikin shi ya fara tasowa ya gina masu ƙaton gida shida mahaifin shi ya kai shi makka. A lokacin mahaifinshi bai da gurin da ya wuce ya ganshi da jikokin shi, yasha faɗa mashi ya nason yaga ya tara zuri'a yakuma killace su a tare dan ya yaye mashi kaɗaicin shi. Saboda farin cikin mahaifin shi ya auro matar shi yar sudan alokacin da harkokin shi suka kai shi can. Hajia Shareefa yar gidan mutunci da karamci, tana da kirki sosai.

Haka suka cigaba da zamansu tana kula da mahaifin mijin ta tamkar shine ya haifeta. Shekara na zagayowa ta haifi ɗanta namiji, kusan Alh Qaseem ya fisu murna da samun ƙaruwar, ranar suna yaro yaci suna Khaleed. Ba yadda Hayat baiba akan ya sa sunan shi amma yace a'a ya bari sai an ƙara wani.

Bayan shekara uku ta samu wani cikin, murna sosai Alh Qaseem ya yi ganin zuri'ar shi zata tashi,Sadda ta haihu sai ya zamo mace ce, yaso maida sunan baban shi amma Allah bai nufa ba a yanzu ma dan haka yarinyar suka saka mata Ramlat. Shekara biyu ciff tayi suka haifi Qaseem cikin ikon Allah ba abin da bai ɗakko ba a kamannin Kakan shi dan haka Hayat ya ke matuƙar son shi, haka ma ga Alh Qaseem sosai yake son takwaran nashi. Daga shi sai Harith, sai autan su Umar. Daga nan haj shareefa bata sake haihuwa ba. Ko a haka ya gode ma Allah kuma ya ɗauki ƙudirin inganta rayuwar yaran shi ya haɗe kansu dan cika burin baban shi.

A hankali ya fara masu gini a wata sabuwar unguwa da bata cika gine gine ba, filine mai girman gaske aka yanka wurin ginin, dan haka tun da ginin ya fara miƙawa kowa ya kalla yasan ba karamin kuɗi ake kashewa ginin ba, haka mutane zasu so ganin kammaluwar shi. Burin shi kawai baban shi yaji daɗi ya yi rayuwa mai inganci a tare da su.

Bayan gama komai na gidan,suka fara shirye shiryen komawa. Yara sai murna suke zasu koma sabon gida. Sai dai Allah bai yi nufin Alh Qaseem zai yi rayuwa a cikiba, Allah yai mashi rasuwa.

Mutuwar ta girgizasu sosai,sunyi kukan rashi. Daga ƙarshe Alh Hayat Dando ya yanke shawarar bazai koma gidan ba tunda mahaifin shi baya raye. Sai ya fara kokarin gina wani a kusa dashi, abu kamar wasa ginin yayi kyau a wuri ɗaya sai ya cigaba da saye filayen duk dake nan ya na haɗewa ya na faɗaɗa gidan da niyyar in yaranshi suka tashi su zauna ciki da zuri'arsu, amma akwai tazara sosai daga sashe zuwa sashe. cikin kankanin lokaci gida mai sassa da girma ba na wasa ba ya tashi. Sai duk parts ɗin suka zagaye na farkon da ya farayi amma sai ya fisu girma da kyawu tunda shi da niyyar dukkansu su zauna ne da mahaifinshi. An ƙawata gidan sosai ta yadda aka malala titi daga farkon gate ɗin zuwa ƙaton parking lot ɗin da aka yanka ga dukkanin gidajen. Sanan aka bishi da ƙananun duwatsu da fitulu masu birgewa. A gaba ɗayan filin da zai kai ka sashe zuwa sashe kananun fararen duwatse ne masu salƙi a barbaje sai flowers ɗin da ke zagaye da bangwayen. Daka shigo sunan _DANDO VILLA_ da ke manne yana walwali zai fara kashe maka ido cikeda birgewa, Hakan ne ma ga gate na baya inka zagaya.

Babu wanda baisan da Dando villah ba a garin, da haka mutane sukai ta taruwa unguwar har ya zamo kusan unguwar na ansa sunan dando villah ne.

Kullum sai Qaseem ya ishi baban da shidai su koma gidan daya fi girma, shi yafison shi. Sai yai dariya yace ai wanda yake son zama dashi a gidan yanzu babu shi, shiyasa sai dai ya zauna kusa da shi. Sai ya tambaye shi to wazai zauna ciki da duk sauran gidajen da babu kowa ciki. Shikuma yace nasu ne in sun girma su zauna. Sai yaita dariya yace shi ƙaton yake so to. Da irin haka sai Alh Hayat yace ta ya bashi shi inya girma ya zauna, ƴayyunshi sai su dinga faɗin gidan Hayat, Da ya ƙara wayau sai yace shi ma ɗanshi zai bawa. Sai ayita dariya.

NOORUN NISADonde viven las historias. Descúbrelo ahora