18

557 77 1
                                    

NOORUN NISA
( Light of the women )



Subscribe my youTube channel please.👇🏻

https://youtu.be/ABjHKTccoss

Happy birthday to someone who is smart, gorgeous, funny and reminds me a lot of myself... i owe so much to you. #Aysha Al'ameen #Mr. S🥰 #Atattauna🥰 ILYSM Qawata.








Cikin kwana biyun nan idan ta ce da natsuwa ta yi su ta yi ƙarya, tabbas ita ta yadda za ta taimakawa mummy amma har yau tunani da fargabar hakan ba su barta ba. A cikin kunnuwanta akai komai na makarantarta har nan aka zo akai mata passport da komai ma, amma bayan komai ya kammala sai mummy ta ce ba sai ta je ba. Daga can za'ai mata sai dai a kawo mata result kawai. Ba dai dan taso ba ta haƙura tunda ƙarƙashin alfarma ta ke.

Tunda su ka tsara shirinsu sabeena ta tsiri zama part ɗin Daada ko yaushe, musamman idan ta fakaici zaid ya kusa dawowa aiki sai ta zari mayafi ta tafi dan tasan can yake wucewa kai tsaye, sai ya ci abinci ya huta kafin ya ke tafiya.tunda sukai aure bazai ce ya taɓa ɗanɗana girkin matarshi ba. Ita ma gaba ta kaita tunda ba wani iyawa ta yi ba.

Daada ganin matarshi kusa, ya ke sa ta ce sabeena ta haɗo mai abinci. Da wannan damar ta ke amfani ta girgije abin shanshi da maganin Dr. Ta kawo mashi, kusan kwana biyar hakan ke faruwa. Daada ido ta zura ma sabeena ta ga iyakar gudun ruwanta, har wane lokaci zata ɗauka ta na burus da lamarin mijinta akan cikinshi dan sam ba ta cika son saka baki akan lamarin yaranta ba ma bare jikoki saboda gudun shiga hakki, ta kuma san akwai lokacin da dakanshi zai buƙaci hakan. Sau tari takanyi mashi hannunka mai sanda ko dan ya fahimta amma ta kula shiɗin ba komai ya ke ganewa ba sak ɗan fari dai, shiyasa ta ke bin komai sannu har lokacin da zai gane dan kuwa abinci ba ma na sabeena kaɗai ke bai taɓa ci ba kusan duk gidan ma abu ne mai wahala ya ci wani abu a sashin wasu gara ma Aunty Nafeesa da su ka fi shiri da ita fiye da kowa, sai kuma in yaje gidansu sameer da hajiar su ke tusashi gaba sai ya ci abincinta tun bai sakin jiki har ya saba, to wuraren nan ukku ne ya ke cin abinci cikin daɗin rai.

A cikin kwana biyar ɗin nan kuma ya ke ciwon ciki akai akai, tun bai ɗauki abun da muhimmanci ba saboda ayyukan gabanshi har ciwon ya fara tsanani a dare ya hana shi bacci.

Washe gari ya faɗawa baffa aiko ya ce maza ya je ya ga likita kar abun ya fi haka. Hakan kuwa akai kafin ya je office wurin Dr. Bash ya fara zuwa dake shine family doctor'n su.

Ba tare da ɓata lokaci ba Dr. Ya shaida mashi appendix ne yai mashi yawa dole ma a yi aiki da wuri. Kai tsaye ya amince da aikin a gobe bayan ya faɗawa baffa.
Dr. Kuma ya ɗauki waya yaiwa mummy albishir, dan daɗi kamar ta taka kan jariri. Ya na kashe wayar ya kira abokinshi Dr. Daniel ya shaida mashi gobe za a fara aiki tunda ya cika mashi kuɗi da aljihu waɗanda mummy ta bayar.

Kamar yadda aka faɗa mashi gobe aikin haka ya shirya yazo, Daada ce ƴar rakiya. Akai mashi allurar bacci dr. Daniel yai aiki hankali kwance aka zuƙi abinda ake buƙata aka shaidawa Daada an gama aiki gobe za a sallame su. Kafin goben kuwa kusan gaba ɗaya Dando Family na asibitin kowa na nuna bajintarshi akan Zaid ɗan masu gida, mummy kau ta fi kowa zaƙewa a wurin tunda ɗanta ne kuma suriki.

Koda a ka sallameshi ma Daada hana shi zuwa office ta yi tace sai ya kwana biyu ya huta dukda bawani ciwo ya ke ji ba.


Nudhar kuwa tunda mummy ta faɗa mata gobe ne aikin hankalinta yai matuƙar tashi harta nemi yin gardama, amma dake mummy mai wayau ce da ta shallake tunanin ta sai ba ta bata damar hakan ba, tare da yi mata alkawurra kala kala a ciki harda taimakonta na ƴancinta gidan kawu da kuma maidata ga mahaifiyarta ta kuma tabbatar ta ansheta da hannuwa biyu, bata tsaya anan ba ta ƙara mata da alkawarin ɗaukar karatunta na gaba harta gama.
Da waɗannan kalaman hankalin Nudhar ya kwanta, amma tunani da al'ajabin abinda zai faru bai barta ba tunda ance aiki kala biyu za'ai mata daga rainon ciki, ai ita ma matar yakamata ai mata aikin ko? Amma sai ta ga ba haka ba ita kaɗai ce za'ai mawa. Ganin dai ba wanda zata tambaya ya bata ansar da zata gamsu sai ta hakura da wasi wasi ta cigaba da addu'a kawai ya bata ikon cika masu burinsu ko dan nata ma ya cika ta dunga ra'ayin kanta kamar kowa.

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now