Hankali ɗage ya fito psychiatric ɗin gabanshi na faɗi, kar wani abu ya samu yarinyar mutane ta dalilinshi. Wayar sameer ya kira bai ɗaga ba, sai kawai ya yanke shawar tadda Sameer ɗin kamar yadda yace mashi da fari.
•••
Bayan kukan da ta ci da bubbuga ƙofa ba taji alamun kowa ba ya sa ta fara zagaye ɗakin da tunanin hanyar fita. Motsin da take jiyowa a waje ya saka ta taka ta leƙa ƴar ƙaramar tagar ɗakin, Sameer ta hango ya na ta leƙe-leƙe kamar yana neman wani abu. Daga nan ta dinga ɗaga mashi hannu amma bai ganta ba baya iya juyo ihun kiran sunan shi da ta ke ma. Ta na ji ta na gani yabar wurin, wani sabon kuka ya zo mata ta na hango Faarah a ranta ta rasa tunanin da zata yi akan maganar mubarak bayan yaran ta da take son su kasance da ita da ta kwammace su mummyn sun kasheta ta huta.
Bakin ƙofar ta koma ta ce gaba da bubbugawa. Sameer ya gaji da zagaye bai ga alamar ma mutane na zaune gidan ba dan duk ƙura ma.Ya zo zai shiga Psychiatric ya hango Nudhar ɗin da wata suna gudu an biyo su, da sauri ya bisu dan ya ɗauketa amma kafin ya isa sai ya hango wata mota ta tsaya sun shiga, sai yaci gaba da bin motar har suka iso unguwar da babu wasu gine-gine duk ciyayi motarshi ta tsaya ya na gani suka karya kwana. Dole ya fito duba motarshi hakan ya ɗaukeshi lokaci mai tsawo kafin ya samu ta tashi. Kwanar da yaga sun bi ya nufa yana zagaye tunda daga nan bai san ina sukai ba, ciyayi kuma sun hana ya ga sawun su.
A cikun haka ya hango wannan tsohon gidan, kamar ya wuce tunda gidan bai yi akamar akwai mazauna a ciki ba sai dai zucciyarshi ta dinga ingizashi da ya duba.
Kwaɗon da aka rufe gidan ya ja,sai kuwa ya buɗe da alamun ya tsufa ya gaji cikin alamun da suka ƙara nuna an daɗe ba a shiga gidan ba. Haka dai ya shiga ya gama zagayen shi ba komai har zai wuce ya ji kamar ana buga abu.
Yaita bin sautin har ya isa ga ƙofar da ke kulle da kwaɗo, sai da yai amfani da dutse ya samu daƙyar ya ɓalleshi ya na mamakin abin da ke cikin ɗakin..mamakin shi ya sarƙe da yai ido huɗu da Nudhar.
"Nudhar..?" Ya faɗi yana fiddo ido.
"Tashi mu je" ya ƙara faɗi
Ta shiga girgiza mashi kai, da mamaki ya ke kallon ta da son jin dalili.
"Faara..amrah" ta faɗi cikun kuka
"Su waye su? Mai sukai maki?"
Ta ƙara girgiza kai ta ce
"Ɗiya ta ce, ƴan biyun Aabid..da ƙawata Amrah ya kama su idan na tafi ba zai barsu ba"
Da sauri ya tsugunna gabanta ya ce
"Aabid ƴan biyu ne?"
Ta gyaɗa kai.
"Ta yaya? Duk taya hakan ya faru ya akai Zaid bai sani ba? Kina iya faɗamani ke asalin wace ce da abin da ya haɗa ki da su mummy?"
Kai ta gyaɗa ta shiga bashi labarin yadda ta tashi gidan kawu,auren da zai mata haɗuwarsu da mummy har zuwa yadda suka rabu. Ta kuma faɗa mashi yadda sukai yanzu da Mubarak.
Jijjiga kai ya ke cike da Al'ajabin labarin, hakan ya tabbatar mashi kuma su mummy zasu iya yin komai dan cimma manufarsu,haka shima mubarak ɗin. Ga yadda ta faɗa mashi yadda sukai da Mubarak ya fahimci in da suka dosa su duka..dukiya kawai, kowa so ya ke ta zama tashi ba tare da sun duba Alkairan Baffa a garesu ba. Mubarak ya sauƙaƙa mashi niyyarshi akan Nudhar, yadda ba ta da kowan nan Zaid ne kawai Zai iya zama gatan ta. Su biyun su na buƙatar junansu, Za su zama garkuwa ga junansu. Komai zai faru ba zai taɓa bari Zaid ya rasa Nudhar ba.
"Kar ki damu, idan ya zo ki faɗa mashi kin amince..zan kula da komai"
Ta ɗago ta kalle shi da sauri, ya gyaɗa mata kai.
YOU ARE READING
NOORUN NISA
General Fictionƙaddara mai ƙarfi ta haɗa su biyun ba tare da sanin ɗayan su ba. a lokacin da wata ƙadarar ta kawo su ga juna sai suka zama tamkar suna ganin hanjin junan su ne saboda ƙiyayyar da sukewa juna. amma kowannen su ya na mamakin yadda yake jin kaddarar...