08

648 93 9
                                    



Na yanke shawarar yafe laifukanki..badan na rasa hanyar hukunta ki ba sai dan wasu dalillai da sukai maki alfarma, ki bar nan wurin da dukkan zucciyarki..karki ƙara saken da ƙaddara zata nuna mani fuskarki har abada!

Kalaman da su ke yawo akanta kenan tun da ta fiddo ƙafarta da ga office ɗin shi. Azahirin gaskiya abinda ta fi buƙata kenan  nesanta kanta da shi har abada kamar yadda ya faɗi, sam haɗuwar su bata taɓa barin bugun zucciyarta ya tafi daidai ba sai a yanzun da ta ke ganin ta rabu da kwallon mangoro ta ke jin kamar an sauke mata nannauyan gungumin da ya tokare mata zucciya da hanyayoyin fitar numfashi.

"Nudhar!"

Muryar saudat ta datse tunanin ta.

"Zaki tafi ne?"

'A'a zuwa na yi' ta faɗa a ranta, inba ta rainata ba tana ganin tayi hanyar fita kuma tana tambayarta akan abinda idonta ya gane mata?

Ta ƙaƙalo yaƙe ta buga mata.

"Hoto zakiyi mani idan ban takura ki ba"

' Dan Allah kiyi mani videon kamfanin inkinje yau ina son gani '

Muryar Amrah ta faɗo mata, tai murmushi daman ta na tunanin ta yadda zata fara ɗaga waya tai mata video a wurin kunya ta ke ji ita kam yanzu kuma ga dama.

"Kai ba komai bari nai maki"

Tai saurin ɗakko wayarta latsa video.

Kai innalillahi banga waya ta ba. Ta kama ƴan lalube-laluben jikkarta kafin ta kalla Nudhar

"Ina ga fa ɗazu na barta nan imda na ganki ɗazu muje in duba please, ajiye jikkarki bisa motar nan tunda kin riga kin tashi ba zaki koma da jikka ciki ba"

Bata kawo komai ba ta ajje jikkar ta ɗaura wayarta ma akai daga sama tunda taga wurin da security sosai.

Suna barin wurin, na cikin motar da baƙin gilashinta ya hana a fahimci akwaisu suka fito.

"Yi maza lalubo mana kafin su dawo"

Ɗaya ya faɗa yana waige waige ɗayan kuma ya saka hannu ya matsar da wayar ya zura hannun a jikkarta ya na lalube.

"Wallahi gashi"

Ya fiddo mabuɗen da suke buƙata ruwa a jallo!

"Aiki mai kyau, ban taɓa hango zamu taɓa buɗe office ɗin oga ba gaskiya haruna kayi aiki mai kyau saudat ma ta cancanci yabo"

"Kai dallah zo mu shige gasu nan dawowa"

Wanda aka kira da haruna ya faɗi ya na janye ɗan uwanshi suka koma motar suka rufe.

"Na baki wahala shaf na mance banzo da waya ba yau wallahi yi haƙuri"

"Babu komai bari nai maki da wayata"

"Bari wani lokaci sauri ma nake na cinye lokacina" 

Ta faɗi ta na barin Nudhar tsaye.

Mtsw! Taja tsakin takaicin vedion da batai ba ta ɗauki jikka da wayar ta tai gaba.

Ƙafarta tai mata wani irin nauyi a lokacin da take isa fita gaba ɗaya kamfanin. Ta ɗaga idonta sama ta na karanto.

Z. D passionate da ke manne ya na ƙyalli da ɗaukar ido.

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now