Ruwan da taji an maka mata a fuska ya saka ta buɗe idanuwan ta. Miƙa ta so yi taji da aɗaure cikin mamaki ta bi hannuwanta da kallo da su ke a ɗaure ta baya. Ta ɗaga kai ta kalla mutanen gabanta, macen da ta ɗakkosu ce a mota tare da Halima da suka gudo a tare. Abinda ya ɗaure mata kai yadda taga halima cikin kwalliya tasha ƙananun kaya abinta sai wuwulla ido ta ke cikin ƙwarewa da nuna ita ɗin ƴar duniya ce.
"Halima?" Ta faɗi da mamaki ta na kallon ta.
"Shhhh!" Ta faɗi ta na ɗaura yatsanta a bakin ta. Ta kalli budurwar da suke tare tace.
"Kira shi"
Ba tare da ta ce komai ba ta shiga daddana wayar hannun ta.
"Ta farka" ta ɗan saurara kaɗan kafin ta ce "Ok" ta kashe wayar.
Kallon halima ta yi suka fice daga ɗakin, zuwa cen halima ta dawo da plate ɗin abinci shinkafa da miya sai salad akai ta aje mata da ruwa pure water.Zagayawa ta yi ta kwance mata hannuwanta ta ce
"Ki ci abinci"
Ta juya, har ta kai ƙofa Nudhar ta ce
"Zan yi sallah"
Da hannu halima ta nuna mata bayi ta wuce. Alwalla ta yo da ta iso ta iske kafet tai sallah ta rw da roƙon Allah ya warware mata matsalolinta dan Al'amarin su mummy sai addu'a ce kawai zata ƙwace ta dan dai tasan ba wanda zai mata wannan abun sai su. Yadda cikin ta ke murɗawa da kukan yunwa ya saka ta jawo plate ɗin abincin ta fara ci cikin sauri-sauri ta cinye ta sha ruwa. Ƙofar aka buɗe wani ya shigo.
Tunani ta ke inda ta taɓa ganin fuskar, ya katse mata tunani da faɗin
"Kar dai ace kin kasa tuno ni?"
Ya zauna bisa kujera ya na mata murmushi. Yanzu ta tuna inda ta sanshi, cikin ƴan uwan Zaid a asibiti. Kallon mai kake so kai kuma tai mashi.
"Suna na mubarak khaleed Dando! Cousin brother na Zaid. Ni ne babba cikin jikoki a familyn Dando"
"Mai kake so?" Ta faɗi kanta tsaye.
Hannuwa ya taɓa ya na ƴar dariya.
"Saurin me kike? Ai dalilin ne ya sa kike zaune a nan. Ba zan maki wani ɓoye-ɓoye ba zan faɗa maki komai da abinda ke faruwa da abinda nima nake so"
Ya gyara zama.
"Kamar yadda na faɗa maki nine babba a cikin jikoki, babanmu shi ne babba a cikin iyaye ma. Kowa ya san da sanin babba shine magajin gida ko ma ina ne, amma nia namu familyn dam ba haka bane, kin san dalili"?
Ta girgiza mashi kai.
"Son kai ne tsantsa tare da nuna banbanci ƙarara, abin da ya sa na faɗi haka kuwa ban tashi na ga babana ya na jan gidan yadda ya kamata ba, ni na saka ran yin hakan ganin nine babba a jikoki amma saboda son kai sai abin ya juye Zaid ya zama na kusan shine komai na Dando villa tun daga kyawun muhallali zaki fahimci banbancin da a kai mana tsakani da shi, Gata, Dukiya duk Zaid ne yai kane kane da abin da ya kamata ace haƙƙina ne. A yanzu kuma lokaci yayi da nake ganin ya kamata na maido komai a ƙarƙashi na."
"Ta yaya" ta tamabaya da mamakin irin wannan ƙarfin hali irin nashi, ko dayake taga alamun ba shi kaɗai ne da baƙin hali ba tunda ga mummy ma ta gani, sai dai har a ranta take fatan Allah sa irinsu su tsaya haka nan in kuwa ba haka ba lallai a kwai babbar matsala a ahalinsu.
"Da taimakon ki" ya katse mata tunani.
"Na daɗe ina son samun hanyar da zan bi dan ganin komai ya dawo hannu na, mamana bata bani haɗin kai haka ya sa dole na haɗa kai da Aunty saratu saboda ita ce buƙatarmu ta zo ɗaya. Amma sai na kula ta na amfani da nine dan cimma tata manufar ba tare da ta duba tawu ba shiyasa yanzu nai maganin abun.
YOU ARE READING
NOORUN NISA
General Fictionƙaddara mai ƙarfi ta haɗa su biyun ba tare da sanin ɗayan su ba. a lokacin da wata ƙadarar ta kawo su ga juna sai suka zama tamkar suna ganin hanjin junan su ne saboda ƙiyayyar da sukewa juna. amma kowannen su ya na mamakin yadda yake jin kaddarar...