Saƙon farko ta koma ta karanto, ta dawo ta karanta na bayan kanta na ƙara ɗaurewa. To wama ya santa har haka? Duk duniya banda Allah da yafi kowa sani babu wanda ya san ta haifi yara biyu sai Dr.hindu, ta tuna hakan.
'A'a Dr. Bata da dalilin da zai saka tayo mani irin wannan saƙon, ko mai take son faɗa mani kanta tsaye zata faɗi'
Ta furta hakan tare da ƙara son canko wanda keda masaniyar hakan amma ta kasa, tunda babun.
Ta kalli Amrah da ta saka Faarah gaba suna baccinsu hankali kwance ta na jin kamar ta tadata ta gwada mata, sai ta ga gara ta kyaleta tai baccin ta. Da tunanin koma waye zai bayyana kanshi idan ya gaji da nuƙu-nuƙun bacci ya kwasheta.
•
"Dan Allah Baby ka kyale shi yau ɗaya dai"Sabeena da ke ta faman lallashin Aabid ta faɗi ta na kallon Zaid. Yau da wani irin kuka Aabid ɗin ya tashi marar dalili, wai ba zashi school ba. Tun zaid na rarrashin shi da dabaru tare da alkawarin kai shi park idan ya dawo amma firr ya ƙi saurarar shi kukanshi kawai yake da tirjewa ya ƙi bari a saka mashi kaya sam.
Hakan ya ƙular da zaid bai san sadda ya fallawa fuskarshi mari ba, hakan ya kara gigitashi ya sake hautsinewa sabeena ta rungumeshi ta na ta faman rarrashi tare da roƙon zaid ɗin akan ya haƙura ya barshi.
Babu abin da ba zaiwa Aabid ba, ya na jin yadda ku kanshi ke taɓa shi amma ba zai fara saba mashi da rashin zuwa makaranta ba. Yasan shi sarai, idan ya ƙyaleshi yau gobe ma zai ce ba zashi ba yaron bai iya cin ƙwan makauniya ba.
"Ki bar goya mashi baya akan abin da kinsan ba zsi faru ba, ki saka madhi kayanshi lokaci na wucewa"
Ya faɗi ya na miƙa mata kayan. Badan taso ba ta ansa ba tasan a binda zai takura ɗanta sam.
Ganin za a saka mashi kayan ya buga tsalle ya dira ƙasa ya na ci gaba da tirje tirje, tsawar da zaid ya doka ma shi ta saka shi dakatawa ya na binshi da ido a tsorace. Bai saba ganin haka ba, zaid bai taɓa ko hararar Aabid ba balle ɗaga murya. Sai da ya ƙare mashi kallo cike da tsoro sannan ya fashe da sabon kuka.
Ganin hakan zaid ya fizge kayan ya saka mashi da kanshi duk kuwa da fizge fizgen da ya ke. Ya saɓai a kafaɗa suka fita. Da gudu sabeena ta bisu bayan ta yayibo hijab ɗin sallarta ta saka.
Ya na buɗe mota ya saka Aabid ita ma ta buɗe ta shige. Ko kallon ta baiyi ba ya ja motar suka tafi.
Aunty sumayya da ke dogon hange ta windon ta, ta cije leɓe. Taso ace ta ji abinda ya faru a wurin cen, leƙawa ta yi taga mai fita da shiga cikin safiyar ta hango fitowarsu. Cotton ɗin ta saki ta na takaicin zuwan da batai ba da wuri, wata ƙila da ta fahimci wani abun.
Mubarak dake tsaye ta jikin gidanshi ya saki murmushi bayan fitar motar su zaid, ya zaro wayarshi da ga aljihu ya na daddana wata number.
Ko maganar minti ɗaya ba suyi ba ya kashe ya na goge number da ga recent call. Ya koma ciki.
••• ••••Gajiya ta yi da zaman da take yi, ta ɗauki wayarta ta kira Amrah ko fira sunyi amma wayar har ta gama ringing ba a ɗaga ba. Ta tashi ta zuge window a hankali ta leƙa taga ko yazo, ba kowa da alama har yanzu bai zo ba. A gogo ta kalla tara har da rabi. Mamaki ta ke abinda ya tsaida shi har haka, yau tun bakwai ta zo dan ta na son yimashi girki..cikin saurin da ta ke ganin zata iya tayi flat bread da liver sauce sai ta haɗa mashi Lipton da ganyayen ƙamshi fa saka a flaks, ta zaci idan ta fito zata ganshi kamar ko yaushe amma taga wayam sai ta gyara table ɗin ta matsar da komai gefe guda kafin ta jera mashi abincin ta koma office ɗinta ta zauna har zuwa yanzu da ta leƙa ba taga alamar yazo ba.
Ta shi ta yi ta fita waje tgara ta zagaya ta rage zaman shiru, magdalin da ke zaune ta bita da harara. Ba ƙaramin haushi Nudhar ke bata ba tun zuwanta ta ƙwace mata matsayin da ta ke hari, ta buga kwafa alamaun zaki sani.
YOU ARE READING
NOORUN NISA
General Fictionƙaddara mai ƙarfi ta haɗa su biyun ba tare da sanin ɗayan su ba. a lokacin da wata ƙadarar ta kawo su ga juna sai suka zama tamkar suna ganin hanjin junan su ne saboda ƙiyayyar da sukewa juna. amma kowannen su ya na mamakin yadda yake jin kaddarar...