37

664 80 5
                                    




Riƙe ya ke da waya ya na tunanin kiran ta ko a'a kafin ya yanke shawar tura mata saƙo kilwn ta fi saurin kula shi.

'Kin tafi kin bar ni da kewarki, I really missed you Dear!'

Ya tura ko minti ɗaya ba ayi ba ta mai do

'Liar'

Waro ido yai ya na ƙara karanta saƙon.

'What a pity!' Ya rubuta tare da emoji ɗin tausayi ya tura.

Ta turo mashi emoji ɗin harara. Yai dariya kawai ya tura mata.

'Good Night, hope you miss me too. I love you '

Bai ƙara jin ansarta ba yai dariya ya aje wayar ya tashi ya hau haɗa kayanahi, Zai bita tunda ta guje shi.

Yau ko baccin safe bai koma ba ya ci gaba da ƙara gyara ƴar jikkarshi da ya ɗauki kaya sunkai kala biyar da abubuwan buƙata. Ya shiga yai wankanshi ya sa kaya, agogo kawai ya ke kallo gari ya ƙara haske ya ɗau hanyar yallaman dan ma yasan in ya fita yanzun suna iya ganin shi 8 shiasa ya daure takwas ɗin ta yi sannan ya fita. Daƙyar ya jira bakwai da rabi ta yi, ya rataya jakarshi ya turawa Sameer saƙon yayi tafiya ba zai zo Office ba kwana biyu.

Sashen Daada ya shiga ba kowa da alama ba wanda ya tashi, ba zai iya jiran tashin su ba dan haka ya fito ya shige mota.

Sai da yai nisa sosai sannan ya tsaya ya kira Nudhar.
••

Ta gama Azkhar kenan ta na shirin komawa bacci dan bata tashi da wuri ba, ta ji ƙarar wayarta. Zaid ta gani, kamar ta share shi sai kuma ta ɗauka

"Good morning Princess"

Ya faɗi da ga cen.

"Ina kwana" ta ce

"Lafiya, kin tashi lafiya?"

"Nifa ban ko gama baccin ba"

"Sorry, Bari in zo sai in dinga rero miki waƙa kina bacci"

Ɗaga wayar ta yi ta harare ta kafin ta ce

"Banso"

Ya saka dariya.

"Baki isa ba Allah, na kusa isowa ma. Ki turoman Address"

Tai dariya ta ce

"To" zata kashe wayarta.

"Ba wasa ba wallahi nan da minti talatin na shigo garin"

Ido ta waro ta na kama haɓa da ɗayan hannun.

"To me za kazo yi?"

"Wurin Umma zan zo hutu, tun da ke yini ɗaya kin gudo"

Wata dariyar ta saka har ta na riƙe ciki, wai ma hutu zai zo. A tunanin ta ma ya na hanyar office ne tunda ta na iya jiyo iskan hanya ta cikin wayar.

"Ke da waye da safiyar nan?"

Ta ji muryar umma. Cikin dariya ta ke faɗa mata Zaid ne ya ce ya na hanyar zuwa mata hutu. Ita ma dariya ta yi ta ce ta na maraba da shi. Ya na jiyo muryar umman ya ce ta bata, ba ta musa ba ta miƙawa umma wayar ta haye gado abunta ta ja bargo.

"Sai ka iso to" ta tsinkayo muryar umma. Da sauri ta juyo idonta waje

"Umma cewa ki kai ya zo?"

"Eh mana, wani abu? Ki tashi ki shirya mashi abin kari ya na gab da isowa. Zan aika a taho da shi."

Ta fita ta barta baki sagale da mamaki, wai da gasken ɗakko ƙafa ya yi? Ai ga alama nan tunda bata ga wasa a fuskar umma ba.

"Zaki miƙe kokuwa?"

NOORUN NISAWhere stories live. Discover now